Kasar Sin ta bayyana adawa da sabon takunkumin da kasar Amurka ta kakaba wa kasar Cuba, inda ta sanya shugabannin kasar Cuban cikin jerin sunayen mutanen da aka kakaba wa takunkumin.
Wani kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ne ya bayyana hakan a jiya Juma’a, inda ya ce, al’ummun duniya na fatan ganin samun kwanciyar hankali a Cuba, kuma duk wanda ke neman tayar da zaune-tsaye a kasar Cuba, shi ne zai fada cikin tarkon da ya dana.
A cewar kakakin, kasar Sin na kira ga bangaren Amurka ya daina keta hakkin jama’ar kasar Cuba na rayuwa da neman ci gaba. Jami’in ya yi furucin ne bayan da kasar Amurka ta kakaba takunkumi kan shugaban kasar Cuban Miguel Diaz-Canel, da matarsa, da kuma da, da jikan Raul Castro, tsohon shugaban kasar. (Bello Wang)














Discussion about this post