ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota

by Rabi'u Ali Indabawa
2 months ago
Kano

An gurfanar da akalla direbobi 123 a fadin Jihar Kano gaban kotu bayan Rundunar ‘Yansandan jihar ta kama su bisa zargin tuka motoci ba tare da lambar rajista ba ko kuma da lambobin mota da aka rufe, a wani bangare na ci gaba da aiwatar da Operation Clean Plate, wani shiri da aka kaddamar domin dakile ayyukan ta’addanci da sauran laifuka a jihar.

Rundunar ta kuma bayyana cewa ta kama wani mutum mai shekaru 51 a yayin gudanar da wannan samame, inda aka samu bindiga, tabar wiwi, wuka, wayoyin lantarki, batir lithium guda 120 da kuma wata mota da ake zargin ta sata ce a hannunsa.

Kwamishinan ‘Yansandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin da yake yi wa manema labarai bayani a hedikwatar rundunar da ke Bompai, Kano.

ADVERTISEMENT

Bakori ya ce an kaddamar da wannan aiki ne domin magance amfani da motocin da ba su da ingantattun lambobin rajista, wanda ya ce masu aikata laifuka kan yi amfani da shi domin boye shaidarsu da kuma kauce wa binciken jami’an tsaro.

Ya ce tun bayan fara aikin, rundunar ta cafke irin wadannan motoci a kananan hukumomi daban-daban na jihar, kuma an gurfanar da dukkan direbobin a gaban kotu.

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Damfarar Wayar Salula A Jihar Adamawa

IGP Disu Ya Hana Jami’an Ƴansanda Yin Amfani Da TikTok Da Instagram Da Sauransu

“Wannan ba kawai laifin karya dokar zirga-zirga ba ne. Dabara ce da masu aikata laifuka ke amfani da ita domin su boye asalinsu, su aikata laifi sannan su kauce wa kama su,” in ji Kwamishinan.

Ya kara da cewa: “Rundunar ‘Yansandan Jihar Kano karkashin jagorancina ba za ta bari a rika amfani da hanyoyinmu a matsayin mafakar masu aikata laifuka ba.”

Kwamishinan ya ce kamen da aka yi a Sashen ‘Yansandan Panshekara ya kara tabbatar da muhimmancin wannan shiri.

A cewarsa, a ranar 9 ga Yuli, 2026, jami’an da ke aikin sintiri sun tare wata mota da ba ta da lambar rajista, amma direban ya yi kokarin tserewa kafin daga bisani aka kama shi.

Bakori ya ce binciken da aka gudanar kan mutumin da motarsa ya kai ga gano bindiga, tabar wiwi, wuka, wayoyin lantarki, batir lithium guda 120 da kuma motar da ake zargin ta sata ce, inda ya kara da cewa an mika wanda ake zargin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka (CID) na rundunar domin ci gaba da bincike.

Ya ce: “Abubuwan da aka kwato sun tabbatar da dalilin da ya sa muka kaddamar da Operation Clean Plate. Ana amfani da motocin da ba su da sahihin lambobin rajista wajen safarar mutane masu tayar da hankali, makamai da aka haramta, miyagun kwayoyi da sauran kayayyaki masu hadari a fadin jihar.”

Kwamishinan ya bayyana cewa rundunar na ci gaba da bincike domin gano asalin bindigar da sauran kayayyakin da aka kwato, tare da tantance ko suna da alaka da wata babbar kungiyar masu aikata laifuka.

Ya tabbatar wa al’ummar Kano cewa za a ci gaba da gudanar da wannan aiki a dukkan kananan hukumomi 44 na jihar, domin karfafa tsaro da hana masu aikata laifuka amfani da gibin da ke cikin tsarin tsaro.

“Operation Clean Plate ba zai tsaya ba. Za a ci gaba da aiwatar da shi tare da kara fadada shi a dukkan kananan hukumomin Jihar Kano,” in ji Bakori.

Ya kuma bukaci masu motoci da su tabbatar sun yi wa motocinsu rajista yadda ya kamata, sun samu ingantattun lambobin mota, sannan su cire duk wani abin da ke hana a iya gane lambar motar.

Haka kuma, ya roki mazauna jihar su ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai tare da ba su sahihan bayanai domin taimaka musu wajen hana aikata laifuka.

Bakori ya gargadi jami’an ‘yansanda da su guji duk wani rashin kwarewa ko cin zarafi yayin gudanar da aikin, yana mai jaddada cewa kwarewa da ladabtarwa su ne ginshikan aikin rundunar.

“Duk wani jami’in da ya aikata abin da bai dace ba a lokacin wannan aiki, a kai rahotonsa. Ladabtarwa da kwarewa ba abin sassauci ba ne,” in ji shi.

Ya kara da cewa Rundunar ‘Yansandan Jihar Kano za ta ci gaba da jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma tare da kara inganta tsaro a fadin jihar.

Kano
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

An Kama Matashi A Kano Kan Zargin Kashe Abokinsa
Kotu Da Ɗansanda

‘Yansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Damfarar Wayar Salula A Jihar Adamawa

July 18, 2026
Disu
Kotu Da Ɗansanda

IGP Disu Ya Hana Jami’an Ƴansanda Yin Amfani Da TikTok Da Instagram Da Sauransu

June 26, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga
Kotu Da Ɗansanda

Gwanjon Kadarori: Kotun Daukaka Kara Ta Kori Karar Da Sani Sha’aban Ya Shigar

June 18, 2026
Next Post
Yadda Gano Ma’adanin ‘Lithium’ Zai Sauya Rayuwar Al’ummar Kudancin Kaduna

Yadda Gano Ma’adanin ‘Lithium’ Zai Sauya Rayuwar Al’ummar Kudancin Kaduna

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.