Jakadan Nijeriya a Sin, Lt. Janar Abdulrahman Bello Dambazau mai ritaya, ya ce gwamnatin Nijeriya tana aiwatar da dimbin gyare-gyare domin cimma burikan ci gaban kasar da kyautata rayuwar al’umma, kuma wadannan burika na ba da muhimmanci sosai ga alakar Nijeriya da kasashen waje, ciki kuwa har da kasar Sin. Abdulrahman Bello Dambazau, ya bayyana haka ne a jawabin da ya yi, yayin bikin murnar cikar Nijeriya shekaru 66 da samun ‘yancin kai, wanda ofishin jakadancin Nijeriya ya shirya jiya Laraba a birnin Beijing.
Ya ce bikin na bana mai taken “Daga Gyare-Gyare zuwa Kwanciyar Hankali: Karfafa Sabunta Fatan Nijeriya domin Samun Wadata ta Bai Daya” na nuna cewa karfafa fatan na bukatar abubuwa kamar zuba jari da fadada ayyukan masana’antu da ababen more rayuwa da kara samar da damarmaki ga kasar.
Jakadan wanda ya bayyana bana a matsayin shekara mai muhimmanci saboda cikar Nijeriya da Sin shekaru 55 da kulla huldar diplomasiyya, ya ce a shirye Nijeriya take ta zurfafa dangantaka da Sin a bangarorin kere-kere da aikin gona da makamashi da sufuri da tattalin arzikin dijital da kiwon lafiya da ilimi da sauransu.
Ya kara da cewa, Nijeriya na son fadada kayayyakinta da ke shiga kasuwar Sin da karfafa alakar cibiyoyin hada-hadar kudi na kasashen biyu da kulla hadin gwiwa mai dorewa. Kuma a shirye ofishin jakadancin yake ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta mu’amala tsakanin kasashen biyu da tabbatar da dorewar dangantakarsu.
Taron ya samu halartar wakilan gwamnatin kasar Sin da jakadu da jami’an diplomasiyya da wakilan hukumomin kasa da kasa da ke kasar Sin, da jami’an ofishin jakadancin da sauran ‘yan Nijeriya mazauna Sin. (Fa’iza Mustapha)














