ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sojoji Sun Daƙile Hare-Haren Ƴan Ta’adda, Sun Kwato Makamai A Borno Da Adamawa

by Abubakar Sulaiman
8 months ago
Sojoji

Sojojin Rundunar Operation Haɗin Kai (OPHK) sun daƙile wasu hare-haren da ’yan ta’adda suka kai a sassan jihohin Adamawa da Borno, inda suka ƙwato makamai da harsasai, tare da kashe wasu daga cikin maharan a yayin aikin bin sawunsu.

A wata sanarwa da muƙaddashin jami’in yaɗa labarai na OPHK, Laftanar S.A. Atoko, ya fitar a Maiduguri, ya ce da asubahin Juma’a, 16 ga Janairu, 2026, ’yan ta’adda sun yi yunƙurin kai hari kan sansanin sintiri na Sabon Gari a ƙaramar hukumar Madagali ta jihar Adamawa, ƙarƙashin sashi na 4 na OPHK.

  • Hukumar ‘Yansanda A Borno Ta Kwato Harsasai 912
  • ‘Yan Ta’adda 11 Sun Miƙa Wuya Yayin Da Sojoji Suka Kashe 8 A Borno

Ya ce Sojoji sun hanzarta tunkarar maharan tare da samun ƙarin taimako daga Gulak da Rundunar Quick Reaction Force, inda suka fatattaki ’yan ta’addan ba tare da asarar rai ko kayan aiki ba. Bayan haka, an binciki yankin don tabbatar da babu na’urorin fashewa (IEDs) ko tarko.

ADVERTISEMENT

A wani lamari makamancin haka a ranar, ’yan ta’adda sun kai hari mai yawa daga ɓangarori daban-daban kan Forward Operating Base (FOB) Azir a jihar Borno. Sojoji, tare da taimakon rundunar sama ta OPHK, sun yi musu luguden wuta na tsawon fiye da awa guda, lamarin da ya tilasta wa maharan janyewa.

Atoko ya ce harbin rokar RPG na ’yan ta’adda ya shafi wasu motocin ɗaukar sojoji da dakin kula da CCTV, inda wuta ta lalata wani ɓangare. Duk da haka, sojoji sun ci gaba da riƙe yankin.

LABARAI MASU NASABA

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

An kwato makamai da dama daga hannun ’yan ta’addan da suka haɗa da bututun harba bom na 60mm, da bama-bamai, da na’urorin fashewa da aka ƙera a gida, da harsasan bindigogi masu nauyi da ɗaruruwan harsasan 7.62mm NATO.

Sanarwar ta ƙara da cewa jiragen rundunar sama sun bi sawun ’yan ta’addan da suka tsere, inda aka kai musu hare-haren sama a hanyoyin da suka bi, lamarin da ya janyo mutuwar wasu da dama daga cikinsu.

“Atisayen ya nuna jajircewar sojojin OPHK wajen kare rayuka da dukiyoyi, tare da ƙudirin ci gaba da murƙushe duk wata barazana a yankin Arewa maso Gabas,” in ji sanarwar.

Sojoji
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote
  • Abubakar Sulaiman
    Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa

MASU ALAKA

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci
Manyan Labarai

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato
Manyan Labarai

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia
Manyan Labarai

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
Next Post
Shin Alonso Ya Cancanci Kora A Real Madrid?

Shin Alonso Ya Cancanci Kora A Real Madrid?

LABARAI MASU NASABA

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

September 10, 2026
Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

September 10, 2026
Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026
Sojoji

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
Sojoji

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.