ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, October 23, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sojoji Sun Kashe 25, Sun Daƙile Harin ISWAP A Borno

by Sulaiman
2 weeks ago
ISWAP

Rundunar Sojin Nijeriya ta ce dakarunta sun kashe sama da ’yan ta’addan ISWAP 25 da suka kai wani “hare-hare da dama daga sassa daban-daban” a Kukawa, Jihar Borno.

A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, Mukaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na Hedikwatar Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Gabas, Operation Hadin Kai, Mohammed Goni, ya ce wasu sojoji ma sun rasa rayukansu yayin arangamar.

Sanarwar ta ce ’yan ta’addan ISWAP sun kai wa dakarun Bataliyar Sojoji ta Musamman ta 101 hari da dimbin mayaka daga ɓangarori huɗu, amma sojojin sun yi musu turjiya tare da mayar da martani mai ƙarfi ta hanyar amfani da manyan makamai, dabarun yaƙi da kuma kyakkyawan haɗin gwiwa a fagen daga.

ADVERTISEMENT

Ta ce tallafin rundunar sojin sama ya taimaka wa dakarun wajen fatattakar ISWAP, inda aka kashe da dama daga cikinsu tare da tilasta wa waɗanda suka tsira tserewa a firgice.

“Binciken farko ya nuna cewa an kashe sama da ’yan ta’adda 25, yayin da zuwa yanzu aka gano gawarwaki 14,” in ji sanarwar.

LABARAI MASU NASABA

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

Sai dai rundunar ta ce wasu daga cikin jaruman sojojin Nijeriya sun rasa rayukansu yayin arangamar.

Da yake jajantawa iyalan sojojin da harin ISWAP ya yi sanadin mutuwarsu, Goni ya ce: “Jarumtarsu, sadaukarwarsu da kuma kishin aikinsu za su kasance abin tunawa na dindindin game da hidimar da suka yi wa ƙasa.”

ISWAP
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Gwamna Dauda Lawal Ya Rantsar Da Manyan Sakatarori Biyar
  • Sulaiman
    Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Djibouti
  • Sulaiman
    Ta Yaya Ake Ci Gaba Da Fitar Da Sabbin Kayayyaki A Yayin Baje Koli Na Canton Fair
  • Sulaiman
    Darasi Daga Zuhudun Manzon Allah (SAW)

MASU ALAKA

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara
Manyan Labarai

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

October 23, 2026
Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu
Manyan Labarai

Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

October 23, 2026
Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau
Manyan Labarai

Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

October 23, 2026
Next Post
Hisbah Ta Cafke Mata 6 Kan Zargin Karuwanci A Yobe

Hisbah Ta Cafke Mata 6 Kan Zargin Karuwanci A Yobe

LABARAI MASU NASABA

Mutane 7 Sun Rasu, 11 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Gombe

Mutane 7 Sun Rasu, 11 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Gombe

October 23, 2026
Xi Jinping Ya Umarci Yin Bakin Kokari Wajen Ceto Mutanen Da Girgizar Kasa Mai Karfin Maki 7.0 Ta Rutsa Da Su A Xizang

Xi Jinping Ya Umarci Yin Bakin Kokari Wajen Ceto Mutanen Da Girgizar Kasa Mai Karfin Maki 7.0 Ta Rutsa Da Su A Xizang

October 23, 2026
Binciken CGTN: Daga Samar Da Tsare-tsare Zuwa Aiwatarwa Tsarin Jagorancin Duniya Na Bukatar Karin Dabaru Na Hakika

Binciken CGTN: Daga Samar Da Tsare-tsare Zuwa Aiwatarwa Tsarin Jagorancin Duniya Na Bukatar Karin Dabaru Na Hakika

October 23, 2026
NUJ Ta Gargadi ‘Yan Jarida Kan Yaɗa Rahotannin Da Ba Su Da Inganci Kan Cire Limami Kan Tallata Tinubu A Bauchi

NUJ Ta Gargadi ‘Yan Jarida Kan Yaɗa Rahotannin Da Ba Su Da Inganci Kan Cire Limami Kan Tallata Tinubu A Bauchi

October 23, 2026
Ma’aikatan Lafiya Sun Fara Shirin Tsunduma Yajin Aiki Kan Bashin Alawus Na Wata 19

Ma’aikatan Lafiya Sun Fara Shirin Tsunduma Yajin Aiki Kan Bashin Alawus Na Wata 19

October 23, 2026
Cikakke Kuma Tsattsauran Jagoranci A Kanta Dabarar JKS Ce Ta Gina Kanta

Cikakke Kuma Tsattsauran Jagoranci A Kanta Dabarar JKS Ce Ta Gina Kanta

October 23, 2026
Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Dandalin Xiongan Na 2026

Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Dandalin Xiongan Na 2026

October 23, 2026
Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa

Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa

October 23, 2026
MOC: Manufofin Bunkasa Amfani Da Kayayyaki Sun Fadada Kasuwar Cinikayyar Kayayyaki A Kai A Kai A Farkon Watanni 9 Na Bana

MOC: Manufofin Bunkasa Amfani Da Kayayyaki Sun Fadada Kasuwar Cinikayyar Kayayyaki A Kai A Kai A Farkon Watanni 9 Na Bana

October 23, 2026
NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

October 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.