ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, September 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Soke Harajin Sin Ga Kasashen Afirka Wata Dama Ce Ta Tsame Mutane Daga Talauci

by CGTN Hausa and Sulaiman
5 months ago

Ana ta ayyururi da lale marhabin da manufar kasar Sin ta nuna zumunci da ’yan uwantaka ga Afirka game da soke harajin kwastam ga kayayyakin kasashen nahiyar masu huldar diflomasiyya da ita, wadda ake dab da fara aiwatarwa daga ranar 1 ga watan Mayun da ke tafe.

Tun daga lokacin da aka sanar da wannan mataki, masana tattalin arziki suna ta tsokaci kan yadda za a ci gajiyar hakan, kasancewar kasar Sin tana da katafariyar kasuwa mai dimbin masu sayayya.

Don haka, wannan wata dama ce da za a yi amfani da ita wajen tsame al’umma bil’adam na nahiyar daga kangin talauci.

ADVERTISEMENT

A cewar wasu rahotannin dai, sama da mutane miliyan 430 a Afirka na rayuwa cikin matsanancin talauci, wato suna rayuwa da kasa da dala $2.15 a rana, inda hakan ke nuna cewa akwai bukatar yin aiki wurjanjan domin rage radadin talaucin da ke addabar mutane.

Amma bisa samun wannan dama ta soke harajin shigar da kayayyakin Afirka kasuwar kasar Sin, a iya cewa nesa ta zo kusa, domin mafi akasarin talakawan da ke fama da talauci za su samu karin hanyoyin samun kudin shiga musamman ta hanyar noma, kasancewar amfanin gonar kasashen Afirka suna samun matukar karbuwa a kasar Sin.

LABARAI MASU NASABA

Jawabin Xi A Taron BRICS, Mafita Ce Ga Matsalolin Duniya

Duk Wani Yunkuri Na Karfafa Burin Japan Na Fadada Karfin Soji Zai Jefa Yankin Cikin Hadari

Sai dai kuma, watakila wani ya yi tunanin cewa zai yi wahala noma ya tsamar da mutane daga talauci a yau, saboda a zamanin yanzu kayayyakin kere-kere sun fi kawo kudin shiga masu yawa.

Tabbas babu tantama, sabbin kere-kere sun fi kawo kudi, to amma mu a Afirka zuwa yanzu, ba mu da kere-keren da za mu iya sayarwa ga kasashen waje, muna fatan hakan nan gaba.

Don haka, abun da muke da shi sai mu yi amfani da shi, kuma tabbas, noma yana sahun gaba, kasancewarsa babbar sana’ar mafi akasarin talakawanmu.Bugu da kari, daga shekarar 1981 zuwa 2021, an kiyasta cewa sama da mutane miliyan 800 a kasar Sin sun fita daga matsanancin talauci, kuma noma ya taka muhimmiyar rawa a wannan nasara, kasancewarsa daya daga manyan hanyoyin samun kudin shiga masu dorewa.

Babban abun da ake bukata shi ne, da farko su kansu talakawan su sauya tunani, su daina ganin hakan ba mai yiwuwa ba ne, su kulla a ransu cewa abun zai yiwu kuma su tsara ayyukansu da kakkarfar niyya da burin samun nasara, kamar yadda masu hikima ke cewa “Allah ya ce tashi in taimake ka”.

Manoman karkara su yi kokarin kafa gamayya mai karfi bisa jagorancin masana ta yadda za su kulla mu’amala da ‘yan kasuwa masu fitar da kayayyaki wadanda za su dora su a kan hanyar yin abubuwan da suka dace, kuma a rike gaskiya da adalci ga kowa.

Daga bangaren gwamnatocinmu kuma, jami’an wayar da kai su sauke nauyin da ke wuyansu na ilmantar da manoma yadda za su ci gajiyar wannan dama da aka samu ta kawo kaya kasar Sin.

Kana a zuba jari a hanyoyin karkara, da ayyukan ban ruwa, da samar da irin shuka mai inganci da kuma kara horar da manoma a kan dabarun noma.

Hakika, idan manoma suka kyautata niyyarsu kana suka samu tallafin da ya dace tun daga kan kayayyakin aiki zuwa hanyoyin sufuri, noma zai zama babbar hanyar cin gajiyar wannan manufa ta kasar Sin ta soke harajin shigo da kayayyakin Afirka cikin katafariyar kasuwarta, inda za a samu fita daga kangin talauci da kaso mai yawa har ma da samun wadataccen abinci a cikin gida. Masu iya magana sun ce, “Noma tushen arziki”. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Tsohon Firaminsitan Jordan: Kasar Sin Tana Kan Gaba Wajen Gudanar Da Fasahar AI A Duniya
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Hadin Gwiwar BRICS Na Jagorantar Hadin Kan Kasashe Masu Tasowa Da Dogaro Da Karfin Kansu
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Na Shirin Fadada Samar Da Hidimomin Reno Da Na Kiwon Lafiyar Yara Masu Rahusa
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Gudummawar Da Hada-Hadar Ba Da Hidima Ta Sin Take Kawo Wa Duniya
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Jawabin Xi A Taron BRICS, Mafita Ce Ga Matsalolin Duniya
  • Sulaiman
    Duk Wani Yunkuri Na Karfafa Burin Japan Na Fadada Karfin Soji Zai Jefa Yankin Cikin Hadari
  • Sulaiman
    Tsohon Firaminsitan Jordan: Kasar Sin Tana Kan Gaba Wajen Gudanar Da Fasahar AI A Duniya
  • Sulaiman
    Hadin Gwiwar BRICS Na Jagorantar Hadin Kan Kasashe Masu Tasowa Da Dogaro Da Karfin Kansu

MASU ALAKA

Jawabin Xi A Taron BRICS, Mafita Ce Ga Matsalolin Duniya
Daga Birnin Sin

Jawabin Xi A Taron BRICS, Mafita Ce Ga Matsalolin Duniya

September 14, 2026

Next Post
Hukumar Kula Da Gidaje Ta Jihar Edo Ta Rushe Gine-gine Sama Da 500

Hukumar Kula Da Gidaje Ta Jihar Edo Ta Rushe Gine-gine Sama Da 500

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Zamfara Za Ta Mayar Da Yara 453,602 Makaranta

Gwamnatin Zamfara Za Ta Mayar Da Yara 453,602 Makaranta

September 15, 2026
’Yan Ta’adda Sun Kai Wa Ƙauyuka 2 Hari A Adamawa

Boko Haram Sun Kashe Mutane 4 Tare Da Ƙone Gidaje A Adamawa

September 15, 2026
Wani Mutum Ya Kashe Kishiyar Mahaifiyarsa A Kogi

’Yan Ta’adda Na Shirin Kai Hare-Hare Makarantu, Wuraren Ibada Da Sansanonin NYSC – ’Yansanda

September 15, 2026
Gwamnatin Sakkwato Ta Rufe Masallacin Sheikh Lukuwa Bayan Harin Da Aka Kai Masa

Gwamnatin Sakkwato Ta Rufe Masallacin Sheikh Lukuwa Bayan Harin Da Aka Kai Masa

September 15, 2026
Hannun Jari: Dangote Ya Yi Wa ’Yan Nijeriya Alƙawarin Samun Gaggwaɓar Riba

Hannun Jari: Dangote Ya Yi Wa ’Yan Nijeriya Alƙawarin Samun Gaggwaɓar Riba

September 15, 2026
Dangote Ya Sake Zama Wanda Ya Fi Kowa Kudi A Afrika Karo Na 12

Arziƙin Dangote Ya Haura Dala Biliyan 50 Bayan Fara Sayar Da Hannun Jarin Matatarsa – Forbes

September 15, 2026
Jawabin Xi A Taron BRICS, Mafita Ce Ga Matsalolin Duniya

Jawabin Xi A Taron BRICS, Mafita Ce Ga Matsalolin Duniya

September 14, 2026
Duk Wani Yunkuri Na Karfafa Burin Japan Na Fadada Karfin Soji Zai Jefa Yankin Cikin Hadari

Duk Wani Yunkuri Na Karfafa Burin Japan Na Fadada Karfin Soji Zai Jefa Yankin Cikin Hadari

September 14, 2026
Tsohon Firaminsitan Jordan: Kasar Sin Tana Kan Gaba Wajen Gudanar Da Fasahar AI A Duniya

Tsohon Firaminsitan Jordan: Kasar Sin Tana Kan Gaba Wajen Gudanar Da Fasahar AI A Duniya

September 14, 2026
Hadin Gwiwar BRICS Na Jagorantar Hadin Kan Kasashe Masu Tasowa Da Dogaro Da Karfin Kansu

Hadin Gwiwar BRICS Na Jagorantar Hadin Kan Kasashe Masu Tasowa Da Dogaro Da Karfin Kansu

September 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.