ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wakilin Sin a Babban Taron Wha Na 79 Ya Bukaci A Inganta Daidaiton Ci Gaban Lafiya a Duniya

by CGTN Hausa and Sulaiman
4 months ago
Sin

Shugaban tawagar Sin, kuma shugaban hukumar kiwon lafiya ta kasar Lei Haichao a jiya Talata 19 ga watan, a cikin jawabinsa yayin muhawarar da aka yi a babban taron kiwon lafiya na duniya (WHA) karo na 79, ya bayyana cewa, gyare-gyaren tsarin kiwon lafiya na duniya dole ne ya ci gaba da zama a karkashin jagorancin kasashe mambobi, tare da baiwa kasashe masu tasowa damar fada a ji da kuma bukatunsu, kana da inganta daidaiton ci gaban lafiya a duniya.

Lei Haichao ya kara da cewa, cikin shekaru 60 da suka gabata, kasar Sin ta tura ma’aikatan lafiya 31,000 na agaji zuwa kasashen waje, tare da kula da jinyar marasa lafiya miliyan 300, kuma ta kirkiro maganin zazzabin cizon sauro na Artemisinin, inda ta bayar da “gudunmawa irin ta Sin” don inganta samun daidaito a bangaren kiwon lafiya a duniya. Bugu da kari, Sin tana matukar goyon bayan tsarin hadin gwiwar bangarori da yawa, kuma tana goyon bayan matsayin kungiyar lafiya ta duniya (WHO) da rawar da take takawa wajen daidaita ayyukan kiwon lafiya na duniya, tare da hadin gwiwa da bangarori daban-daban, don inganta tsarin kiwon lafiya na duniya ya zama mafi adalci, daidaito da kuma inganci. Ban da wannan kuma, wakilin Sin na dindindin a ofishin MDD dake birnin Geneva na Switzerland da sauran kungiyoyin kasa da kasa, Jia Guide ya yi jawabi a madadin “rukunin abokan inganta tsarin shugabancin duniya” ta Geneva, inda ya yi kira da a gina ingantaccen tsarin kiwon lafiya na duniya mai adalci, da inganci da kuma hadewa da juna.

Jia Guide ya nuna cewa, a halin yanzu tsarin kiwon lafiya na duniya yana fuskantar kalubale da dama. Inganta tsarin kiwon lafiya na duniya nauyi ne dake rataya a wuyar kowa da kowa don kare lafiyar jama’a da inganta ci gaba mai dorewa.

ADVERTISEMENT

Ya kamata bangarori daban-daban su rike manyan ka’idoji uku, na farko, nacewa ga shiga ayyukan tsari cikin daidaito, ta yadda za a saurari ra’ayoyi da damuwar bangarori daban-daban, musamman na kasashe masu tasowa. Na biyu, tsayin tsaya daka kan hadin gwiwar bangarori da yawa. Na uku, kiyayewa da kuma mutunta muradun bil’adama, da kula da ainihin bukatun al’ummun kasashe masu tasowa.

A watan Fabrairun bana ne aka kaddamar da “rukunin abokan inganta tsarin shugabancin duniya” ta Geneva bisa kokarin bangaren Sin, wadda ta zama wani dandali mai kyau ga bangarori daban-daban su rika tattaunawa kan sake fasalin tsarin shugabancin duniya da inganta shi. Ya zuwa yanzu, rukunin yana da kasashe mambobi 47. (Amina Xu)

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

Kasar Sin Za Ta Taimaka Wajen Bunkasa Wadatar Makamashi Da Ci Gaba Mai Dorewa A Duniya

Sin
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30
Sin
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030
  • Sulaiman
    Gwarzon Ɗan Siyasa Na Shekarar 2026 Sanata Abdul’Aziz Abubakar Yari
  • Sulaiman
    Kasar Sin Za Ta Taimaka Wajen Bunkasa Wadatar Makamashi Da Ci Gaba Mai Dorewa A Duniya
  • Sulaiman
    Ɗabi’un Annabi (SAW) Kan Abubuwa Na Al’adar Rayuwa

MASU ALAKA

Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030
Daga Birnin Sin

Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

September 11, 2026
Kasar Sin Za Ta Taimaka Wajen Bunkasa Wadatar Makamashi Da Ci Gaba Mai Dorewa A Duniya
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Za Ta Taimaka Wajen Bunkasa Wadatar Makamashi Da Ci Gaba Mai Dorewa A Duniya

September 11, 2026
Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya
Daga Birnin Sin

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

September 10, 2026
Next Post
Mutane Huɗu Sun Mutu a Kano Bayan Mota Ta Afka Cikin Dam

Mutane Huɗu Sun Mutu a Kano Bayan Mota Ta Afka Cikin Dam

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

September 11, 2026
Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

September 11, 2026
Sanata yari

Gwarzon Ɗan Siyasa Na Shekarar 2026 Sanata Abdul’Aziz Abubakar Yari

September 11, 2026
Kasar Sin Za Ta Taimaka Wajen Bunkasa Wadatar Makamashi Da Ci Gaba Mai Dorewa A Duniya

Kasar Sin Za Ta Taimaka Wajen Bunkasa Wadatar Makamashi Da Ci Gaba Mai Dorewa A Duniya

September 11, 2026
SAW

Ɗabi’un Annabi (SAW) Kan Abubuwa Na Al’adar Rayuwa

September 11, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Shirya Horar Da Malamai 250,000

Gwamnatin Tarayya Ta Shirya Horar Da Malamai 250,000

September 11, 2026
Sin

Sojoji Sun Ceto Mutane 13 Da ’Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su

September 11, 2026
Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

September 11, 2026
Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

Gwamnan Shekara na 2026 Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang

September 11, 2026
Sin

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

September 11, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.