ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 16, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wang Yi Ya Halarci Taron Rukunin Abokai Na Tsarin Inganta Jagorancin Duniya

by CGTN Hausa and Sulaiman
4 months ago
Wang Yi

Mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, wanda kuma shi ne ministan harkokin wajen kasar Mr. Wang Yi, ya halarci taron rukunin abokai na tsarin inganta jagorancin duniya, wato “Group of Friends of Global Governance” a jiya Alhamis a hedkwatar MDD da ke birnin New York, taron da ya hallara wakilan kasashe sama da 60, ciki har da ministocin harkokin wajen kasashen Pakistan, da Turkimenistan, da Cuba da Zimbabwe.

A jawabin da ya gabatar a gun taron, Wang Yi ya bayyana cewa, a watan Satumban bara, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar inganta jagorancin duniya, wadda ta samu amincewa daga kasashe da kungiyoyin duniya kusan 160.

Daga nan kuma, bi da bi aka kafa rukunonin abokai na tsarin inganta jagorancin duniya a biranen New York, da Geneva da kuma Vienna, rukunonin da mambobinsu suka kai sama da 60.

ADVERTISEMENT

Wang Yi ya jaddada cewa, domin inganta tsarin jagorancin duniya, kasar Sin ta gabatar da shawarar yin gyare-gyare ta wasu fannoni tara, wato na farko, a yi wa MDD garambawul don inganta ayyukanta. Na biyu, a inganta fada-a-ji na MDD da kuma kwarewarta. Na uku, a sa kaimi ga ayyukan kiyaye zaman lafiya su tafi tare da zamani. Na hudu, a hada kawunan kasa da kasa ta fannin gaggauta ci gaba. Na biyar, a dora ayyuka masu nasaba da hakkin dan Adam a kan tafarkin da ya dace. Na shida, a zurfafa gyare-gyaren tsarin tattalin arziki da hada-hadar kudi. Na bakwai, a kafa dokoki kan fasahar kirkirrariyar basira. Na takwas, a inganta ayyukan jagorantar harkoki masu alaka da yanar gizo da kuma sararin samaniya. Na tara, a inganta musayar al’adu da hakuri da juna da kuma koyi da juna.

Wang Yi ya kara da cewa, a lokacin kakan bana, kasar Sin za ta shirya taron dandalin tattauna harkokin inganta jagorancin duniya a birnin Xiong’an na kasar, kuma tana sa ran yin shawarwari tare da bangarori daban daban, game da yadda za a inganta tsarin jagorancin duniya. (Lubabatu Lei)

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Fitar Da Ka’idojin Na’urar Kiwon Lafiya Ta Sadarwa Tsakanin Kwakwalwa Da Na’ura Mai Amfani Da AI

Rokar Gravity-1 Na Kasar Sin Ya Harba Sabbin Taurarin Dan’adam Daga Teku

Wang Yi
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/

    Xi Ya Taya Jami’ar Jilin Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Tattalin Arzikin Sin Ya Ci Gaba Da Tafiya A Turba Mai Kyau Yayin Da Masana’antun Manyan Fasaha Da Cinikayyar Ketare Ke Habaka
Wang Yi
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    ’Yansanda Sun Kama Mutane 240 Bisa Zargin Laifuka Daban-Daban A Yobe
  • Sulaiman
    Sin Ta Fitar Da Ka’idojin Na’urar Kiwon Lafiya Ta Sadarwa Tsakanin Kwakwalwa Da Na’ura Mai Amfani Da AI
  • Sulaiman
    Gwamnan Kano Ya Naɗa Hafsat Kutama Mukaddashiyar Shugabar Hukumar PCACC 
  • Sulaiman
    Rokar Gravity-1 Na Kasar Sin Ya Harba Sabbin Taurarin Dan’adam Daga Teku

MASU ALAKA

Sin Ta Fitar Da Ka’idojin Na’urar Kiwon Lafiya Ta Sadarwa Tsakanin Kwakwalwa Da Na’ura Mai Amfani Da AI
Daga Birnin Sin

Sin Ta Fitar Da Ka’idojin Na’urar Kiwon Lafiya Ta Sadarwa Tsakanin Kwakwalwa Da Na’ura Mai Amfani Da AI

September 16, 2026
Rokar Gravity-1 Na Kasar Sin Ya Harba Sabbin Taurarin Dan’adam Daga Teku
Daga Birnin Sin

Rokar Gravity-1 Na Kasar Sin Ya Harba Sabbin Taurarin Dan’adam Daga Teku

September 16, 2026
Xi Ya Taya Jami’ar Jilin Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa
Daga Birnin Sin

Xi Ya Taya Jami’ar Jilin Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa

September 16, 2026
Next Post
NNPP Za Ta Kwace Mulki A Jihar Imo – Kwankwaso

2027: Za A Rantsar Da Peter Obi A Matsayin Shugaban Ƙasar Nijeriya - Kwankwaso

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

’Yansanda Sun Kama Mutane 240 Bisa Zargin Laifuka Daban-Daban A Yobe

September 16, 2026
Sin Ta Fitar Da Ka’idojin Na’urar Kiwon Lafiya Ta Sadarwa Tsakanin Kwakwalwa Da Na’ura Mai Amfani Da AI

Sin Ta Fitar Da Ka’idojin Na’urar Kiwon Lafiya Ta Sadarwa Tsakanin Kwakwalwa Da Na’ura Mai Amfani Da AI

September 16, 2026
Gwamnan Kano Ya Naɗa Hafsat Kutama Mukaddashiyar Shugabar Hukumar PCACC 

Gwamnan Kano Ya Naɗa Hafsat Kutama Mukaddashiyar Shugabar Hukumar PCACC 

September 16, 2026
Rokar Gravity-1 Na Kasar Sin Ya Harba Sabbin Taurarin Dan’adam Daga Teku

Rokar Gravity-1 Na Kasar Sin Ya Harba Sabbin Taurarin Dan’adam Daga Teku

September 16, 2026
TCN Ta Samar Da Hanyar Samun Wutar Lantarki A Kebbi Ta Wucin Gadi

TCN Ta Samar Da Hanyar Samun Wutar Lantarki A Kebbi Ta Wucin Gadi

September 16, 2026
APC Ta Tsawaita Rijistar Mambobinta, Ta Ɗage Ranar Babban Taronta Na Ƙasa

APC Ta Nemi A Gudanar Da Bincike Kan Farmakin Da A Kai Ofisoshinta A Kaduna

September 16, 2026
2023: Me Ya Sa Ake Rububin Wike?

Ban Taɓa Yi Wa Tinubu Alƙawarin Zan Koma APC Ba – Wike

September 16, 2026
Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’adda Sama Da 1,100 Cikin Shekara Ɗaya – Kwamanda

Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’adda Sama Da 1,100 Cikin Shekara Ɗaya – Kwamanda

September 16, 2026
Tinubu Zai Kayar Da Atiku Da Obi Ko Da Sun Haɗa Kai – Fayose

Tinubu Zai Kayar Da Atiku Da Obi Ko Da Sun Haɗa Kai – Fayose

September 16, 2026
Jarumin Nollywood Olu Jacobs Ya Rasu Yana Da Shekaru 84

Jarumin Nollywood Olu Jacobs Ya Rasu Yana Da Shekaru 84

September 16, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.