Rundunar Sojojin Saman Nijeriya (NAF) ta tabbatar da cewa ɗaya daga cikin jiragenta masu saukar ungulu (helikopta) ya yi saukar gaggawa (precautionary landing) a Jihar Benuwai, biyo bayan wata tangarɗa da ya fuskanta a yayin da jirgin ke kan aiki.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na NAF, Air Vice Marshal Edward Gabkwet, ya fitar, ya bayyana cewa lamarin ya auku ne a lokacin da jirgin ke gudanar da aikin sintiri na yau da kullum a sararin samaniyar jihar. Ya jaddada cewa babu wani ma’aikacin jirgin da ya samu rauni ko rasa ransa, kuma ba a samu asarar rayuka ko dukiyoyin fararen hula a yankin da jirgin ya sauka ba.
Sanarwar ta ƙara da cewa matuƙin jirgin ya yanke shawarar yin saukar gaggawar ne cikin ƙwarewa bayan na’urorin jirgin sun nuna alamar matsalar fasaha, domin kauce wa aukuwar mummunan hatsari kamar yadda ƙa’idojin aikin sojin sama da tsaro suka tanada.
Bayan faruwar lamarin, rundunar ta tura tawagar ƙwararrun injiniyoyi da jami’an bincike daga sansanin sojojin sama da ke Makurdi (NAF Base Makurdi) zuwa inda jirgin ya sauka domin tantance matsalar, gudanar da gyare-gyaren da suka dace, da kuma dawo da jirgin sansaninsa cikin aminci.














