ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

A Karshe Jamilu Gwamna Ya Samu Babbar Damar Yin Takara

by Shuaibu Shuaibu
3 months ago
Gwamna

Bayan samun goyon bayan Gwamnan Jihar Gombe, an amince da Jamilu Isyaku Gwamna, a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar APC mai mulki a zaben fidda gwani da jam’iyyar ta gudanar a watan da ya gabata.

Yanzu a babban zaben 2027 Gwamna zai fafata da Bala Tinka na jam’iyyar ADC, da kuma Isa Pantami na jam’iyyar PDP, wanda dukkansu -Tinka da Pantami, sun koma sabbin jam’iyyunsu ne bayan sun gaza samun tikitin takara a APC.

Yayin da yake sanar da Gwamna a matsayin dan takarar APC, Gwamna Inuwa Yahaya, ya bayyana shi a matsayin gogaggen dan siyasa kuma kwararren ma’aikacin gwamnati da ke da karbuwa a tsakanin al’umma, wanda a cewarsa Gwamna yana da amana da kuma tasirin da zai tabbatar wa jam’iyyar nasara a zabe mai zuwa.

ADVERTISEMENT

Da yake nuna godiyarsa kan wannan amana, Jamilu Gwamna, ya yi alkawarin ci gaba da dora wa kan nasarorin da gwamnatin Jihar Gombe ta samu tare da daga martabar jihar zuwa wani sabon matsayi na ci gaba.

Samun tikitin jam’iyyar APC mai mulki wani muhimmin sauyi ne a tafiyar siyasar Gwamna, wanda tun a shekarar 2007 ya fara neman kujerar gwamnan jihar Gombe karkashin jam’iyyar ANPP.

LABARAI MASU NASABA

Buni Ya Nuna Kwarewarsa Ta Diflomasiyya

Shin Tinubu Ya Tabbatar Da Sauke Ribadu Daga Mukaminsa?

A lokacin yakin neman zabensa na 2007, Gwamna ya ziyarci shalkwatar Kamfanin LEADERSHIP Group, inda ya bayyana burinsa da hangen nesansa na ci gaban Jihar Gombe.

Shekaru kusan ashirin kenan yana jiran wannan dama inda samun tikitin jam’iyyar mai mulki, wanda bai taba samu a baya ba, ya kusantar da shi ga cikar burinsa na zama gwamna, abin da ma sunansa “Gwamna” ke nuni da shi.

A shekarar 2011, ya shaida yadda dan uwansa, Ibrahim Dankwambo, ya bar aikin gwamnati a matakin tarayya tare da samun tikitin PDP, wanda ya kai shi ga zama gwamnan jihar.

Bayan shekaru takwas, yanayin siyasa bai ba da damar wani dan uwa ya gaji wani a kujerar gwamna ba amma daga bisani, a shekarar 2022, bayan ya kasa samun tikitin PDP, Jamilu Gwamna ya fice daga jam’iyyar tare da mara wa wa’adin mulki na biyu na Gwamna Inuwa Yahaya baya.

A wancan lokaci ma, Gwamna ya soki PDP, yana mai cewa jam’iyyar ba ta shirya karbar mulki ba inda aka rawaito shi yana cewa; “A gare ni wannan mataki shawara ce ta kaina, tun da ban shirya yin ritaya daga siyasa ba, dole na nemi wata hanya, kuma wannan hanyar ita ce komawa APC.”

Duk da haka, ya jaddada cewa goyon bayan da ya bai wa Inuwa Yahaya, ba don wata bukata ta kansa ba ne, sai dai saboda ci gaban jihar da kuma imaninsa cewa gwamnan na gudanar da aiki mai kyau kuma zai iya yin fiye da haka.

Yanzu alamu na nuna cewa wannan amincewa da goyon bayan da ya bai wa Gwamna Inuwa Yahaya, sun fara haifar masa da da mai ido, domin gwamnan ya nuna masa irin wannan karamci ta hanyar mara masa baya domin samun tikitin takarar gwamna.

Gwamna
Shuaibu Shuaibu
+ postsBio
  • Shuaibu Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/shuaibu-shuaibu/
    Buni Ya Nuna Kwarewarsa Ta Diflomasiyya
  • Shuaibu Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/shuaibu-shuaibu/
    Shin Tinubu Ya Tabbatar Da Sauke Ribadu Daga Mukaminsa?
  • Shuaibu Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/shuaibu-shuaibu/
    Akwai Ayar Tabaya Kan Zuba Hannun Jarin Dala Miliyan 750 Na Yari
  • Shuaibu Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/shuaibu-shuaibu/
    Wa Tanimu Turaki Ke Fafutukar Karewa?

MASU ALAKA

Zanga-Zanga: Gwamnatin Yobe Ta Bayar Da Umarnin Rufe Makarantun Jihar
Bakon Marubuci

Buni Ya Nuna Kwarewarsa Ta Diflomasiyya

August 28, 2026
An Kusa Ceto Ɗaliban Neja Da Aka Sace – Ribadu
Bakon Marubuci

Shin Tinubu Ya Tabbatar Da Sauke Ribadu Daga Mukaminsa?

August 28, 2026
Kwairanga Ya Kafa Tarihi A Shugabancin Hukumar Kula Da Kasuwar Hannun Jari Ta Nijeriya
Bakon Marubuci

Kwairanga Ya Kafa Tarihi A Shugabancin Hukumar Kula Da Kasuwar Hannun Jari Ta Nijeriya

July 24, 2026
Next Post
Yayin Da Dangote Ya Bayyana A Ganawar Neman Aiki

Yayin Da Dangote Ya Bayyana A Ganawar Neman Aiki

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.