ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yayin Da Dangote Ya Bayyana A Ganawar Neman Aiki

by Shuaibu Shuaibu
3 months ago
Dangote

Attajirin da ya fi kowa arziki a Afirka, Aliko Dangote, kwanan nan ya halarci wata tattaunawa ta podcast mai suna ‘In Good Company’.

Tattaunawar ta fi mayar da hankali kan jarin da Dangote ke zubawa, amma yanayin tambayoyin da amsoshin da ya bayar, sai suka yi kama da irin wadanda mai neman aiki ke bayarwa.

Tabbas ba neman aiki yake yi ba. An kiyasta arzikin Dangote ya kai kusan dala biliyan 30, kuma a cikin tattaunawar ya bayyana shirinsa na zuba jarin fiye da dala biliyan 45 a nahiyar Afirka.

ADVERTISEMENT

Amma shirin ‘In Good Company’, babbar nasara ce ga Dangote saboda kasancewar shirin, ya fi mayar da hankali ne kan manyan ’yan kasuwa, shugabannin duniya da fitattun masu tunani.

Dangote ya burge mai gabatar da shirin, Nicolai Tangen, da kwarin gwiwarsa da kuma shirinsa na zuba makudan kudade a Afirka, ciki har da gina daya daga cikin manyan cibiyoyin masana’antu a nahiyar — matatar mai ta dala biliyan 20 mai karfin tace ganga 650,000 a rana.

LABARAI MASU NASABA

Buni Ya Nuna Kwarewarsa Ta Diflomasiyya

Shin Tinubu Ya Tabbatar Da Sauke Ribadu Daga Mukaminsa?

Dangote ya nuna kwarewarsa sosai yayin tattaunawar, inda ya yi magana kan ladabi a kasuwanci, muhimmancin hangen nesa da kuma fahimtar bukatun kasuwannin Afirka.

A cewarsa, daya daga cikin manyan bukatun nahiyar shi ne samar da siminti, wanda kasashen Afirka da dama ke fama da karancinsa. Ya ambaci Nijeriya, Zambia da Congo Brazzabille a matsayin kasashen da suke zaman jira har watanni uku kafin su samu siminti.

Da aka tambaye shi inda ya samo kudin gina matatar mai, Dangote ya bayyana bayanai fiye da yadda ya saba yi. Game da bambance-bambancen al’adun kamfanoni a Afirka da wahalar gudanar da kasuwanci, Dangote bai raina nahiyar ba.

Maimakon haka, ya fi mayar da hankali kan al’adun aiki a cikin kamfanoni daban-daban da kuma matakin horas da ma’aikata, wanda ya ce za su iya yin nasara a duk inda suka shiga a fadin duniya.

Dangote har ya ambaci makarantar horaswa da kamfaninsa ke gudanarwa domin zakakuran dalibai daga jami’o’in Nijeriya da sauran kasashen Afirka.

Nicolai Tangen, ba kawai mai gabatar da podcast ba ne; shi ne babban jami’in gudanarwa na ‘Norges Bank Inbestment Management’, wanda ke kula da Asusun Arzikin Kasa na Norway.

Asusun na Norway shi ne mafi girman asusun gwamnati na zuba jari a duniya, inda yake da kadarori da suka haura dala tiriliyan 2.

Yana da hannun jari a kamfanoni 7,200 a kasashe 70 na duniya.Tattaunawar podcast din da Dangote ya yi wani bangare ne na tattaunawa da hadin gwiwar asusun domin zuba jari a Dangote da kuma Afirka baki daya.

Dangote
Shuaibu Shuaibu
+ postsBio
  • Shuaibu Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/shuaibu-shuaibu/
    Buni Ya Nuna Kwarewarsa Ta Diflomasiyya
  • Shuaibu Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/shuaibu-shuaibu/
    Shin Tinubu Ya Tabbatar Da Sauke Ribadu Daga Mukaminsa?
  • Shuaibu Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/shuaibu-shuaibu/
    Akwai Ayar Tabaya Kan Zuba Hannun Jarin Dala Miliyan 750 Na Yari
  • Shuaibu Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/shuaibu-shuaibu/
    Wa Tanimu Turaki Ke Fafutukar Karewa?

MASU ALAKA

Zanga-Zanga: Gwamnatin Yobe Ta Bayar Da Umarnin Rufe Makarantun Jihar
Bakon Marubuci

Buni Ya Nuna Kwarewarsa Ta Diflomasiyya

August 28, 2026
An Kusa Ceto Ɗaliban Neja Da Aka Sace – Ribadu
Bakon Marubuci

Shin Tinubu Ya Tabbatar Da Sauke Ribadu Daga Mukaminsa?

August 28, 2026
Kwairanga Ya Kafa Tarihi A Shugabancin Hukumar Kula Da Kasuwar Hannun Jari Ta Nijeriya
Bakon Marubuci

Kwairanga Ya Kafa Tarihi A Shugabancin Hukumar Kula Da Kasuwar Hannun Jari Ta Nijeriya

July 24, 2026
Next Post
Dangote

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.