Sakatare janar na kwamitin kolin JKS kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana yau Talata cewa, ya cimma muhimmiyar matsaya da sakatare janar na jam’iyyar ‘yan kwadago ta Koriya ta Arewa kuma shugaban kasar Kim Jong-Un, kan raya dangantakar Sin da Koriya ta Arewa a sabon zamani.
Ya ce bangarorin biyu sun yi tattaunawa mai zurfi game da kare zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankinsu da ma duniya.
Shugaba Xi ya bayyana haka ne lokacin da ya halarci liyafar cin abinci rana da shugaba Kim Jong-Un ya shirya masa. (Fa’iza Mustapha)
ADVERTISEMENT
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/

Discussion about this post