ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Xi Jinping Da Takwaransa Na Seychelles Sun Yi Musayar Sakon Taya Murnar Bikin Cika Shekaru 50 Da Kulla Huldar Diflomasiyya

by CGTN Hausa and Sulaiman
2 months ago
Xi

A yau Talata 30 ga watan nan na Yuni ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na Seychelles Patrick Herminie, suka aikewa juna sakon taya murnar bikin cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashensu.

Cikin sakonsa, shugaba Xi ya ce yana dora matukar muhimmanci ga bunkasar alakar kasarsa da Seychelles, ya kuma sha alwashin kara azama tare da shugaba Heminiyer, wajen mayar da wannan gaba ta bikin cikar alakar kasashensu shekaru 50 da kafuwa wani sabon mafari, na ci gaba da karfafa kawancen gargajiya, da gina shawarar ziri daya da hanya daya mai matukar inganci tare, kana da amfani da dandalin bunkasa hadin gwiwar Sin da Afirka wajen zurfafa cimma gajiyar bai daya, karkashin kudurorin hadin gwiwa na dandalin, da ingaza ci gaban bai daya, da jagorantar daga kawance bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Seychelles zuwa sabon matsayin, ta yadda hakan zai amfani al’ummun kasashen biyu.

A nasa sakon kuwa, shugaba Herminie cewa ya yi Sin ta jima da kasancewa muhimmiyar kawa mai kima ga kasar Seychelles, inda take samarwa kasar muhimmin goyon baya dake kyautata rayuwar al’umma, da walwala da cimma nasarar kudurorin bunkasa kasar ta Seychelles.

ADVERTISEMENT

Kazalika, bangaren Seychelles na nacewa kan manufar kasar Sin daya tak a duniya, zai kuma ci gaba da karfafa hadin gwiwa tare da Sin karkashin shawarar ziri daya da hanya daya, da hada karfi wajen gina shawarar, da dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka na FOCAC, da kuma ci gaba da zurfafa alakar kasashen biyu. Ban da haka, bisa gayyatar shugaban kasar Seychelles, Patrick Herminie, wakilin musamman na shugaban kasar Sin, Xi Jinping, kuma ministan sufuri, Liu Wei, ya halarci bikin ranar kasa domin murnar cika shekaru 50 da samun ‘yancin kan kasar Seychelles a Victoria, babban birnin kasar, ranar Lahadin da ta gabata.

Herminie ya gana da Liu a Victoria, jiya Litinin, inda lokacin ganawar tasu, Liu ya isar da gaisuwar shugaba Xi da kuma fatan alheri ga Herminie.

LABARAI MASU NASABA

Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya

Liu ya ce, kasar Sin tana dora fifiko sosai kan yaukaka zumuncinta da Seychelles, kuma a shirye take, kamar ko da yaushe, ta goyi bayan Seychelles wajen gano hanyar zamanantarwa da ta dace da yanayin kasarta, da ci gaba da fadada hadin gwiwa mai amfanarwa ga juna a sassa daban-daban, da yin tsayin daka wajen goyon bayan juna kan batutuwan da suka shafi muhimman muradu da manyan abubuwa masu cin tuwo a kwarya, da kuma ciyar da dangantakar kasashen biyu gaba zuwa wani sabon mataki.

A nasa bangaren, Herminie ya yi matukar yabawa da zumuncin da ke tsakanin Seychelles da Sin, sannan ya jaddada cewa Seychelles na girmama dadaddiyar abotar da ke tsakanin kasashen biyu, tana kuma bin ka’idar Sin daya tilo a duniya sau-da-kafa, kana tana son zurfafa hadin gwiwa da kasar Sin a fannoni daban-daban domin karfafa ci gaba da bunkasa alakar kasashen biyu. (Saminu Alhassan / Abdulrazaq Yahuza Jere)

Xi
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30
Xi
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka
  • Sulaiman
    Dalilan Da Ya Sa Jam’iyyun Siyasa Suka Jinkirta Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen
  • Sulaiman
    Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya
  • Sulaiman
    2027: A Karon Farko INEC Za Ta Ƙaddamar Da Na’urar Bibiyar Zaɓen Nijeriya

MASU ALAKA

Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka
Daga Birnin Sin

Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

September 11, 2026
Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya
Daga Birnin Sin

Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya

September 11, 2026
Me Ya Sa Kamfanonin Amurka Ke Kyautata Zato Ga Sabuwar Damar Sin?
Daga Birnin Sin

Me Ya Sa Kamfanonin Amurka Ke Kyautata Zato Ga Sabuwar Damar Sin?

September 11, 2026
Next Post
An Gudanar Da Kusan Ayyuka 500 Iri-iri Masu Ban Sha’awa A “Shekarar Cudanyar Jama’a Da Musanyar Al’adu Tsakanin Sin Da Afirka”

An Gudanar Da Kusan Ayyuka 500 Iri-iri Masu Ban Sha’awa A “Shekarar Cudanyar Jama’a Da Musanyar Al’adu Tsakanin Sin Da Afirka”

LABARAI MASU NASABA

Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

Hadin Gwiwar Hada-Hadar Ba Da Hidima Tsakanin Sin Da Afirka Na Karfafa Karfin Afirka

September 11, 2026
Zaben 2027: Jam’iyyun Siyasa Sun Bayyana Shirinsu Yayin Da INEC Ta Fitar Da Jawalin Zabe

Dalilan Da Ya Sa Jam’iyyun Siyasa Suka Jinkirta Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen

September 11, 2026
Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya

Nazarin CGTN: Kungiyar BRICS Tana Kara Taka Rawar Gani A Harkokin Duniya

September 11, 2026
Za A Ci ’Yan Siyasa Masu Kalaman Ɓatanci Tarar Miliyan 10 Da Ɗaurin Watanni 12 — INEC

2027: A Karon Farko INEC Za Ta Ƙaddamar Da Na’urar Bibiyar Zaɓen Nijeriya

September 11, 2026
Me Ya Sa Kamfanonin Amurka Ke Kyautata Zato Ga Sabuwar Damar Sin?

Me Ya Sa Kamfanonin Amurka Ke Kyautata Zato Ga Sabuwar Damar Sin?

September 11, 2026
Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026  Mrs Zubaida Umar

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026 Mrs Zubaida Umar

September 11, 2026
Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

Sin Ta Kafa Manufar Shiga Sahun Manyan Kasashen Dake Da Karfi A Harkar Kera Motoci A Duniya Nan Da Shekarar 2030

September 11, 2026
Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

September 11, 2026
Sanata yari

Gwarzon Ɗan Siyasa Na Shekarar 2026 Sanata Abdul’Aziz Abubakar Yari

September 11, 2026
Kasar Sin Za Ta Taimaka Wajen Bunkasa Wadatar Makamashi Da Ci Gaba Mai Dorewa A Duniya

Kasar Sin Za Ta Taimaka Wajen Bunkasa Wadatar Makamashi Da Ci Gaba Mai Dorewa A Duniya

September 11, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.