A yau Jumma’a, shugaban kasar Sin, Xi Jinping, ya aike da sakon jaje ga mukaddashiyar shugaban kasar Venezuela, Delcy Rodriguez, dangane da girgizar kasa mai karfi da ta auku a kasar ta Venezuela.
A cikin sakon, Xi ya ce: “Mun yi matukar kaduwa da jin cewa mummunar girgizar kasa ta auku a Venezuela, wadda ta yi sanadin asarar rayuka da kuma barnata dukiya mai yawa. A madadin gwamnatin Sin da al’ummar kasar, ina mika matukar jaje ga wadanda abin ya rutsa da su, tare da nuna tausayawa ga iyalansu da kuma wadanda suka jikkata.
Kasar Sin za ta bayar da taimako ga Venezuela wajen ayyukan agaji kan ibtila’in da kuma sake gina ababen more rayuwa bayan abkuwar ibtila’in. Ina da yakinin cewa, a karkashin jagorancin gwamnatin Venezuela, al’ummar Venezuela za su iya shawo kan wannan ibtila’i tare da sake gina gidajensu cikin hanzari.” (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)














