ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Mutum 1,000 Daga Jam’iyyar ADC Sun Koma PDP A Jihar Katsina

by El-Zaharadeen Umar and Sulaiman
3 months ago
PDP

Aƙalla Mutane 1,000 ne suka sauya sheƙa daga jam’iyyar adawa ta ADC zuwa wata jam’iyyar adawar ta PDP bisa zargin cewa inda suka baro babu tsarin tafiyar da shugabanci.

A cewar jagoran sauya sheƙar Muhammad Lawal BK sun dawo jam’iyyar PDP ne saboda sun ga alamun akwai matsala a wancan jam’iyyar da suka baro.

Taron sauya sheƙar ya gudana ne a shalkwatar jam’iyyar PDP a gaban shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Katsina Hon. Nura Amadi Kurfi da sauran jiga-jigan jam’iyyar.

ADVERTISEMENT

Tunda farko da yake jawabi akan dalilansu da sauya sheƙa Muhammad Lawal BK ya bayyana cewa a matsayin su na matasa suna buƙatar canji shi yasa tun farko suka shiga jam’iyar ADC.

Ya ƙara da cewa daga baya suka lura da cewa lallai ba za su samu wannan canji da suka buƙata ba, na ganin an yi wa jam’iyyar APC korar kare a Katsina, shi yasa shi da magoya bayan sa maza ta mata kusan mutum dubu ɗaya suka sauya sheƙa zuwa PDP.

LABARAI MASU NASABA

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna

“Wannan tafiya har mun kafa kungiyar mai suna “Lado Naka Sai Naka Mobement 2027” ƙarƙashin jagorancin na, wanda muke da fatan samun nasara a zaben 2027 idan Allah ya kaimu da rai da lafiya.

Shima da yake jawabin lale maraba shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Katsina Hon. Nura Amadi Kurfi ya nuna farin ciki da yi ma su barka da baron wancan jam’iyyar da ya kira jam’iyyar rashin tabbas.

Ya ƙara da cewa matsalar tsaro kawai da ta addabi Jihar Katsina ya da ce al’umma su zo su haɗa kai wajen ganin sun kwashe mulki a hannun jam’iyyar APC domin mutane su samu zaman lafiya.

Haka kuma ya yi kira ga gwamna Raɗɗa da ya dawo gida ya zauna domin ya fuskanci abinda ke faruwa a Jihar Katsina musamman batun tsaro wanda ya ce yawan da gwamna Raɗɗa ke yi ya yi yawa.

“Yanzu haka da yawan mutanen Katsina suna hannun ƴan bindiga, da yawan su ba su kwana cikin aminci, da yawa sun zama ƴan gudun hijira, saboda haka dole ne mu gaya masa cewa akwai matsala a Jihar Katsina ya dawo ya zauna ya fuskance ta.” Inji

Kazalika ya yi kira ga waɗanda suka dawo jam’iyyar PDP da su kasance masu amana da gaskiya sannan su cigaba da wayar da kan jama’a domin ganin an baiwa ƴan takarar jam’iyyar PDP goyon baya a zaben 2027.

Ya ƙara da cewa, duk fafutukar da jagororan su na jam’iyyar PDP Sanata Yakubu Lado ke yi na ganin matasa sun samu ilimi yana da alaƙa da wannan matsala ta tsaro, domin a cewar idan matasa suka samu ilimi komi na iya zuwa da sauki.

PDP
El-Zaharadeen Umar
+ posts Bio
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Cutar Mashako:Yadda Yara Ke Mutuwar Bazata A Jihohin Katsina Da Kano
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Mauludin Annabi (SAW): Shugaba Tinubu Ya Nemi A Yi Addu’o’in Nasara Kan Matsalar Tsaro
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Shekaru 8 Cikin Raɗaɗi: Wani Bawan Allah Ya Samu Tiyata Kyauta Daga Gidauniyar Mangal
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Tinubu Ya Nemi Malamai Su Taimaka Wajen Yaƙi Da Ƴan Ta’adda
PDP
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
  • Sulaiman
    Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

MASU ALAKA

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu
Manyan Labarai

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna
Siyasa

Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna

September 9, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Next Post
Majalisar Tarayya Za Ta Binciki Masaƙa Ta Kaduna Da Sauran Gine-ginen Gwamnati 11,000 Da Aka Yi Watsi Da Su

Matsalar Tsaro:Kashi 60 Na Masana’antu A Arewa Maso Gabas Sun Durƙushe

LABARAI MASU NASABA

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.