ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Sin Da Kasashen Afirka Ke Rungumar Juna Na Samar Da Damammaki Ga Afirka Ta Fannin Bunkasa Harkokin Yawon Shakatawa 

by Sulaiman and CGTN Hausa
6 months ago
Sin

Lokacin da ministar harkokin yawon shakatawa ta kasar Afirka ta Kudu Madam Patricia de Lille ta kwatanta da kasuwar kasar Sin a matsayin “babban injin” da zai ingiza bunkasuwar harkokin yawon shakatawa a kasarta, lallai gaskiyar al’amarin ta bayyana ke nan, wato kasashen Afirka na kokarin janyo baki masu yawon shakatawa daga kasar Sin. Daga ranar 23 zuwa 25 ga wata, hukumar kula da harkokin yawon shakatawa ta kasar Afirka ta Kudu ta kira taron da ake ma lakabin “Meetings Africa 2026”a birnin Johannesburg, taron da ya samu halartar wakilan kasashen Afirka sama da 20, wadanda suka tattauna batun ta yaya za su janyo baki masu yawon shakatawa daga kasar Sin.

A bana ake cika shekaru 70 da fara kulla huldar diflomasiyya a tsakanin Sin da kasashen Afirka, haka kuma shekara ce da sassan biyu suka tabbatar a matsayin shekarar cudanyar al’umma da musayar al’adu a tsakaninsu. Don haka, taron da aka kira ba kawai yana shafar harkokin yawon shakatawa ba ne, har ma mataki ne na kara karfafa dangantakar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka. Don kara jawo baki masu yawon shakatawa daga kasar Sin, kasar Afirka ta Kudu ta kaddamar da tsarin ETA ga bakin, wanda zai yi matukar rage lokacin da ake dauka wajen samun biza, sa’an nan, sassan kula da harkokin yawon shakatawa na kasar sun fara samar da kwasa-kwasai na koyar da Sinanci ga ma’aikatansu, don daidaita matsaloli da ka iya bulla ta fannin mu’amala da bakin. Kasar Gabon a nata bangaren, ta dauki matakan saukaka harkokin samun biza ga al’ummar Sinawa, baya ga dukufa a kan inganta zirga-zirga da otel-otel ga baki daga kasar Sin. Har wa yau, in mun lura, sama da kasashen Afirka 20 ne suka dauki matakai na soke bukatar neman biza ga al’ummar kasar Sin ko kuma ba su biza a lokacin da suka shiga kasar.

A sa’i daya kuma, karin baki masu yawon shakatawa na kasar Sin na mai da nahiyar Afirka a matsayin wurin da suke mafarkin zuwa don yawon shakatawa. Li Qiaoyang wanda ya fito daga lardin Shandong da ke gabashin kasar Sin, ya taba zuwa kasashen Afirka don yawon bude ido har sau biyu, kasashen da suka yi matukar burge shi. Ya ce, “Irin yanayin halittu da al’adu na musamman na Afirka abin burgewa ne matuka, kuma matasan kasar Sin da yawa na sha’awar zuwa.” A wannan shekara kuma, yana shirin zuwa kasar Tanzania. Baki masu yawon shakatawa irinsu Li Qiaoyang suna da yawa, kuma alkaluman kamfanonin samar da hidimomin yawon shakatawa na kasar Sin sun tabbatar da hakan. Kamfanin GZL da ke birnin Guangzhou na kudancin kasar Sin ya bayyana cewa, a cikin ’yan watannin baya, yawan shawartar harkokin yawon shakatawa zuwa kasashen Afirka ya karu da kimanin kaso 50% zuwa 60%.

ADVERTISEMENT

A yayin da kasashen Afirka ke daukar jerin matakai na jawo baki daga kasar Sin don neman cin gajiyar babbar kasuwar kasar Sin, ga baki masu yawon shakatawa na kasar Sin kuma, sai a ce “Nesa ta zo kusa”. Irin yadda Sin da kasashen Afirka ke rungumar juna ya shaida yadda suke gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai-daya a tsakaninsu, kuma irin yadda suke musayar al’adu da juna zai karfafa fahimtar juna da dankon zumunci a tsakanin al’ummunsu. Daidai kamar yadda Rod Rembendambya, babban kwamishinan kasar Gabon a Afirka ta Kudu ya ce, zuwan baki daga kasar Sin ba ma kawai zai samar da damar inganta otel-otel da ma sauran manyan ababen more rayuwa a wurin ba, hatta ma da mu’amala da musayar al’adu a tsakanin al’ummomin kasashen biyu.

A lokacin da Sin da Afirka ke murnar cika shekaru 70 da fara kulla huldar diplomasiyya a tsakaninsu, da ma shagulgulan murnar shekarar cudanyar al’umma da musayar al’adu a tsakaninsu, karin baki masu yawon shakatawa na kasar Sin na zuwa kasashen Afirka, wadanda a yayin da suke yawon bude ido, za su kara samun fahimtar kasashen Afirka. Bisa ga irin mu’amala da juna, huldar zumunta za ta kara shiga zukatan al’ummominsu.

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

Sin
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Sin
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
Ramadan: Lokutan Buda-Baki Da Sahur Na Azumi Na 2

Ramadan: Lokutan Buda-Baki Da Sahur Na Azumi Na 9

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.