ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda ‘Yan Ta’adda Suka Tarwatsa Bikin Aure A Kaduna

by Sani Anwar and Sulaiman
3 months ago
'Yan Bindiga

Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki kauyen Kahir da ke Karamar Hukumar Kagarko a Jihar Kaduna, inda suka kashe mutum 13 tare da yin garkuwa da wasu mutane da ba a tantance yawan adadinsu ba.

Wani mazaunin Kagarko, Shehu Bala, wanda ya tabbatar wa wakilinmu ta wayar tarho a ranar Litinin da ta gabata, ya ce; lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:47 na daren Lahadi.

  • Kwankwaso Ya Bayyana Dalilinsa Na Komawa Jam’iyyar ADC
  • Fadar Shugaban Ƙasa Ta Soki Jami’iyyar ADC, Ta Ce Su Fuskanci Matsalolinsu

Ya bayyana cewa, ayarin ‘yan bindigar dauke da bindigogi kirar AK 47, sun kutsa kai wajen daurin auren, inda suka bude wuta a zauren.

ADVERTISEMENT

Har ila yau, a cewar tasa, an garzaya da mutane da dama da suka samu raunukan harbin bindiga zuwa babban asibitin Kagarko, inda ya ce; an kai wasu mutum biyu da suka samu munanan raunuka zuwa Kaduna.

“Hakika, akwai abokaina guda biyu da ke cikin zauren da suka samu raunuka a yayin harin,” in ji shi.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Nijeriya Ba Sa Bukatar ‘Yan Jarida Su Faɗa Musu Suna Jin Yunwa’ — Atiku

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

“Amma ba za a iya tantance adadin wadanda aka yi garkuwa da su ba, saboda harbe-harben da aka yi.”

Wani shugaban al’umma da ya nemi a sakaya sunansa, shi ma ya tabbatar wa wakilinmu faruwar lamarin ta wayar tarho a ranar Litinin.

Kazalika, ya bayyana sunayen wasu daga cikin wadanda aka kashen da suka hada da Bako Danjuma, Williams Luka, Peter Williams, Joseph Yakubu, Bictor Peter, John Dan Asabe, Angulu Markus, Maikano Aribi, Douglas John, Ado Yakubu, Zaphaniah Alhaji, Joseph Kaddah da Francis Unguwa Doya.

Ya kara da cewa, ‘yan bindigar da suka shafe kusan sa’a guda suna gudanar da wannan ta’addanci ba tare da kawo wani daukin gaggawa ba, sun kuma mamaye wasu shaguna tare da kwashe kayan abinci da magunguna daga hannun wani masanin kimiya a cikin al’umma.

Shugaban al’ummar, ya ci gaba da cewa; tuni an binne wadanda aka kashe, koda-yake ya ce; har yanzu ba a tuntubi wadanda suka sace mutanen ba.

“Hakika, an jefa al’ummar yankin baki-daya cikin bala’i, saboda harbe-harben da ‘yan bindigar suka yi a ranar Lahadi da daddare, har wasu suka tsere cikin daji,” in ji shugaban yankin.

Haka zalika, wata majiyar ‘yansanda a sashen Kagarko ta tabbatar da yin garkuwar da kuma faruwar al’amarin, duk da cewa; ‘yansandan ba su san ainihin adadin wadanda aka sace a harin ba.

Da aka tuntubi Kakakin Rundunar ’Yansandan Jihar Kaduna, DSP Hassan Mansur, shi ma ya tabbatar da sace-sacen da kashe-kashen da aka yi, inda ya ce; rundunar za ta fitar da cikakken rahoto kan lamarin.

“Har yanzu, rundunar ba ta samu cikakken bayani kan lamarin da ya faru a unguwar ta Kahir ba, amma za a fitar da cikakken rahoto kan lamarin bayan samun cikakken bayani,” in ji shi.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, wasu ‘yan bindiga sun yi wa al’umma kawanya, a cikinsu har da Janjala.

Mutum 14 da suka hada da dan banga da matarsa da aka yi garkuwa da su a yankin makwanni uku da suka gabata, suna hannun ‘yan bindigar.

Kaduna
Sani Anwar
+ posts Bio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Tattalin Arziƙin Ƙasa: Masana Sun Buƙaci Tinubu Ya Yi Hattara Da Shawarar IMF
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Cututtukan Da Aka Fi Fama Da Su Lokacin Damina Da Yadda Za A Kauce Musu (2)
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Cututtukan Da Aka Fi Fama Da Su Lokacin Damina Da Yadda Za A Kauce Musu (1)
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Talauci Ya Sake Karuwa Da Kashi 63 Duk Da Sauye-sauyen Tattalin Arzikin Da Gwamnati Ta Yi – IMF
Kaduna
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace
  • Sulaiman
    ’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin
  • Sulaiman
    Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi
  • Sulaiman
    Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

MASU ALAKA

Zan Ware 10bn Don Inganta Ilimin Matasa Idan Na Ci Zabe – Atiku
Manyan Labarai

‘Yan Nijeriya Ba Sa Bukatar ‘Yan Jarida Su Faɗa Musu Suna Jin Yunwa’ — Atiku

June 25, 2026
Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi
Labarai

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

June 24, 2026
Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”
Ra'ayi Riga

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

June 24, 2026
Next Post
Wayoyin Wutar Lantarkin Adelabu Sun Zama Tamkar Igiyoyin Shanya

Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

June 24, 2026
Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

June 24, 2026
Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

June 24, 2026
Sabbin Ministoci

Kafa ‘Yansandan Jihohi: Majalisa Ta Amince Da Tsarin ‘Yar Tinƙe Wajen Kaɗa Ƙuri’a 

June 24, 2026
Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

June 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.