ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, September 8, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Za Ku Tattala Kuɗaɗen Da Ke Shigowa Hannu Domin Ci Gaban Rayuwa

by Rabi'at Sidi Bala
4 months ago

Shafi ne da ya saba zaƙulo muku batutuwa daban-daban waɗanda suka shafi al’umma, ciki sun haɗar da; zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya da dai sauransu.

Tsokacinmu na yau zai yi duba game da abin da ya shafi yadda za a tattala kuɗaɗen da ke shigowa hannu domin ci gaban rayuwa. Akwai mutanen da idan suna samun kuɗaɗe a wajen sana’arsu, suke cin banza da wofi, da kashe wa ƴan mata wajen ababen more rayuwa, ƙarshe su manta da abin da suka yi da kuɗin domin ba abu ne me mahimmanci ba.

Dalilin hakan ya sa wannan shafi jin ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin game da wannan batu; “Ko ta wacce hanya ya kamata mutane su bi wajen bunƙasa kuɗaɗensu domin ci gaban rayuwar su?, ko akwai wasu hanyoyi da ya kamata a bi domin gudun lalacewar kuɗaɗen da suke shigowa hannu?,  Wacce shawara ya kamata a bawa matasa, musamman masu kashe kuɗaɗensu akan ƴan matan da su kansu sun san ba aurarsu za su yi ba, da kuma masu cin banza da wofi, daga baya su dawo babu abin da suka tsinanawa kansu da kuɗaɗen?”

ADVERTISEMENT

Ga dai bayanan nasu kamar haka:

Sunana Hassana Yahaya Iyayi daga Kano

LABARAI MASU NASABA

Mene Ne Ra’ayinku Kan Shigar Mata Harkokin Siyasa Gadan-gadan?

Tsakanin Yanayin Sanyi Da Na Zafi Wanne Ya Fi Maka Dadi?

Eh yawanci dama kuɗin a sama suke zuwar masu, ba wuya suka sha wajen nemansu ba, shi ne za ki ga ba su da tattali to, sun samu a sama babu wani shan wuya balle su yi tunanin  gina rayuwarsu. Ku yi karatun tanatsu ku gyara yadda za ku taɓa kuɗinku, a nemi kadarori a siya. Wallahi ku yi wa kanku faɗa tun kan dare yayi maku. Wasu ƴan matan sai sun gama wahalar da ku su waiwayo su ce baku yi ba, kun ga ba kuɗin ba budurwar.

Sunana Aminu Adamu, Malam Madori, Jihar Jigawa:

Hanyar dai ita ce sana’a ta halak ko kuma sana’a mai tsafta, domin akwai sana’o’i dake kawo Kuɗaɗe masu yawa amma fa ba halak ba ne don haka sana’ar ma ya kamata a duba kafin a fara. Eh! Akwai hanyoyi da dama kamar sana’a, noma dama kiwo, duk sana’o’i ne dake iya bunƙasa tattalin arziƙin mutum cikin sauƙi, sannan kuma za ka samu halak ɗinka. Shawarata a nan ita ce ya kamata mutane su kiyayi almubazaranci domin abu ne dake jawo da-na-sani a rayuwa, kuma ya kamata a tsaftacce hanyar neman kuɗi a kiyayi neman kuɗin ido rufe.

Sunana Hafsat Sa’eed, Jihar Neja:

A riƙa adana wani kaso ko da ace misali Dashi ne, ko ba komai zai yi abu me mahimmanci. Idan ma ya san ba shi da nauyin kowa ya kasa kuɗin kashi uku ko huɗu, kashi uku ko biyu sai ya adana, kashi guda ɗaya sai ya ɗauka ya ishe shi amfanin kansa. Ta haka ne ko da ace Dashi ne idan ya ɗauka zai yi wuya ya siyi banza da hofi, sai dai ya adana kadarori kamar fili, gini, da sauransu. Matasa musamman maza a daina zama ana kashewa ƴan mata kuɗi a mayar da hankali wajen tara abin da aka tara tun kan lokaci ya ƙure wa mutun, dan zamani ya canja kowanne namiji da kansa yake wa kansa fafutuka ba wani ne yake masa ba in ya tashi aure.

Sunana Lawan Ismail (Lisary), Rano, a Jihar Kano:

Ƙara gina kasuwancinsu da taimakawa marasa shi. Sadaka, kyauta da kuma siyan abubuwan da za a mora a gaba, kamar; kadarori da kuma gina goben ƴan baya. Su daina irin wannan domin tamkar suna almabazzaranci ne, kuma ko a addini babu kyau, gara ma su riƙa taimakawa ƴan’uwa da abokan arziƙi, da kuma marasa galihu da marayu. Allah ya sa mu dace, Amin.

Sunana Aisha T. Bello, daga Jihar Kaduna:

Gaskiya komai a rayuwa yana son tattali, idan babu wannan tattali ai sai a hakali, idan ka tattala za ka ji daɗi a gaba sosai ma. Eh, akwai gaskiya shi ne in ka samu kuɗi sai ka duba menene yafi muhimmanci kayi, idan ka duba sai kayi sauran kuɗi sai ka ajjiye su a haka-a-haka za ka koyi tarawa. Shawarata ga matasa shi ne mu koyi tattali tun kafin aure, saboda haka na da muhimmanci sosai a gaba, Allah ya shige mana gaba, Amin.

Sunana Sunusi Ibrahim sml

Raba ƙafa wajen kasuwanci kamar 2 domin cimma burika da ƙarancin yankewar kuɗi. Ta hanyar tattali da mileage na rayuwa. Shawarata ita ce, mutum ya san me yake damunsa, kar a manta idan ya rasa abu babu mai bashi to, ya kamata ya san me yake yi masa ciwo.

Sunana Sarauniya Nasmah, daga Jihar Zamfara:

Ta hanyar bunƙasa tunaninsu, su zurfafa wajen nazarin inda za su ƙara juya waɗannan kuɗaɗen su zama riba su ma, ko da kuwa rabin kuɗin ne, ko kuma ya kasance suna cire ko da 35% ne na kuɗin suna ajjiyewa domin gudun faɗawa a komar tunanin yadda za su dawo da kuɗin da suka hallakar wajen abubuwan da ba su da muhimmanci. Shawarata ga masu kashe kuɗi ga ƴan matan da ba aurensu za su yi ba, ku sani  kuna zubin dashin da babu kwasa ne, ku juya akalar almubazzarancinku zuwa ga hanyar da za ku sarrafa kuɗinku mafi daidai.

Sunana Buwangal Adamawa:

Saka kuɗi a kasuwanci da ilimi, adana wani kaso kafin kashewa, siyan abin da ke kawo kuɗi baya. Gujewa asara; rubuta abin kashewa, bambance buƙata da sha’awa, ajjiye kuɗi na gaggawa, kaucewa aron banza. Matasa a daina kashe kuɗi akan abin da ba zai taimaka ba. amfani da kuɗi wajen sana’a, ajjiya, da ci gaban kai. tunanin gobe kafin yau.

Sunana Comr. Ibrahim Lawan Stk:

Ya kamata mutane su riƙa tsara yadda za su kashe kuɗinsu. su fi bada muhimmanci ga ajiya, jari, da sana’a mai amfani maimakon kashe kuɗi a abubuwan more rayuwa marasa amfani. Eh, akwai waɗannan hanyoyi sun haɗa da kamar: yin kasafi kafin kashe kuɗi, rage almubazzaranci, ajjiye wani kaso na kuɗin, shiga sana’a ko hannun jari, kaucewa bin son zuciya wajen kashe kuɗin. Shawarar da za a ba matasa ita ce su ji tsoron lokacin da zai zo gaba, kashe kuɗi a banza, wajen mata ko yawon banza, ba zai kawo cigaba ba, ya kamata su yi amfani da kuɗinsu wajen neman ilimi, sana’a, ko gina makoma mai kyau domin rayuwa ta gaba.

Rabi'at Sidi Bala
+ postsBio
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Yadda Alaƙata Da Adamu Zango Ta Bunƙasa A Kannywood —Jarumi Ibrahim Sodangi 
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Fim Ko Gaske:Yaushe Masu Kallon Fina-finai Za Su Daina Daukar Fim A Matsayin Gaske
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Fim ɗin ƙaddara: Anya Ana Samun Irin Wannan ƙaddarar Kuwa?
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Ko Kafa Ƴansandan Jihohi Zai Taimaka Wajen Kawo Ƙarshen Matsalolin Tsaro?

MASU ALAKA

Mene Ne Ra’ayinku Kan Shigar Mata Harkokin Siyasa Gadan-gadan?
Taskira

Mene Ne Ra’ayinku Kan Shigar Mata Harkokin Siyasa Gadan-gadan?

September 5, 2026
Tsakanin Yanayin Sanyi Da Na Zafi Wanne Ya Fi Maka Dadi?
Taskira

Tsakanin Yanayin Sanyi Da Na Zafi Wanne Ya Fi Maka Dadi?

August 29, 2026
Tsakanin Digiri Da Sana’a Wanne Ya Fi Muhimmanci A Wannan Lokacin?
Taskira

Tsakanin Digiri Da Sana’a Wanne Ya Fi Muhimmanci A Wannan Lokacin?

July 25, 2026
Next Post
Ko Kasan ‘Yanwasan Da Za Su Buga Kofin Duniya Na Ƙarshe?

Ko Kasan ‘Yanwasan Da Za Su Buga Kofin Duniya Na Ƙarshe?

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026
Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.