Wani jigon jam’iyyar APC, Hon. Obidike Chukwuebuka, ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su yi la’akari da ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki da na hukumomi yayin yanke shawarar wanda za su zaɓa a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Jigon na APC, wanda shi ne Shugaba kuma Babban Daraktan Kamfanin Clarivo Holdings Limited, ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar Vanguard, inda ya ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ɓullo da wasu sauye-sauye waɗanda, a ganinsa, suke buƙatar lokaci kafin su bayyana cikakken tasirinsu.
Ya ce cire tallafin man fetur, sauye-sauyen harkokin musayar kuɗin waje, ƙara tattara kudaden shiga, tallafin karatu ga ɗalibai, ayyukan samar da ababen more rayuwa, da matakan ƙarfafa ’yancin cin gashin kan ƙananan hukumomi na daga cikin manyan sauye-sauyen da gwamnatin ta kawo.
A cewarsa, sauye-sauyen sun haifar da gagarumin sauyi da daidaitawa ga ’yan Nijeriya, amma ya kamata a kuma yi la’akari da tasirinsu na dogon lokaci wajen tantance yadda gwamnatin ke gudanar da mulkinta.














