Rundunar ‘Yansandan Jihar Zamfara ta kama mutum 48 a wani samamen haɗin gwiwa da jami’an tsaro suka kai maɓoyar masu aikata laifuka a Gusau.
Kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya ce an gudanar da samamen ne bayan samun bayanan sirri, bisa umarnin Kwamishinan ‘Yansandan jihar, CP A.M. Bello, tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro.
A yayin samamen, jami’an tsaro sun ƙwato babura 17, kekuna uku, janareta ɗaya, lasifikoki uku da ganguna uku, waɗanda ake zargin masu laifi ne suka bari.
Rundunar ta ce waɗanda aka kama, maza da mata, ana ci gaba da bincike a kansu, kuma duk wanda aka samu da laifi za a gurfanar da shi a gaban kotu.
Kwamishinan ‘Yansndan jihar, CP Bello, ya ce wannan aiki na daga cikin matakan da rundunar ke ɗauka domin yaƙi da aikata laifuka da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a Zamfara.
Ya kuma gargaɗi masu aikata laifuka da su daina, ko kuma su fuskanci hukuncin doka.














