Tawagar kafar yaɗa labaran Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ta musanta rahotannin da ke cewa ya buƙaci ‘yan Nijeriya su goyi bayan sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, tawagar ta bayyana rahoton a matsayin labaran ƙarya, tana mai cewa Sarkin Musulmi ba ya goyon bayan wani ɗan takara saboda matsayinsa na uba ga dukkanin ‘yan Nijeriya.
Sanarwar ta ce Sarkin Musulmi na karɓar baƙi daga dukkanin jam’iyyun siyasa, kuma yana ba su shawara da addu’a ba tare da nuna bambanci ba.
Ta buƙaci al’umma da su yi watsi da rahotannin, tare da gargaɗin masu ƙoƙarin jawo Sarkin Musulmi cikin siyasa.
Haka kuma, tawagar ta yi kira ga ‘yan jarida da masu amfani da kafafen sada zumunta da su tabbatar da sahihancin labarai kafin su yaɗa su.
Ta sake jaddada cewa Sarkin Musulmi na ci gaba da jajircewa wajen inganta zaman lafiya, haɗin kai da kwanciyar hankali a Nijeriya.














