A yau Laraba ne aka fitar da “Rahoton binciken albarkatun bayanai na kasar Sin na 2025”, a yayin taron koli na gina kasar Sin ta dijital karo na tara.
Rahoton ya nuna cewa, a shekara ta 2025, yawan bayanan da aka samar a kasar Sin ya karu da kashi 27.28% idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabaci hakan, inda ya kai ma’aunin ZB 52.26.
Daga mahangar kasa da kasa, yawan bayanan da ake samarwa a Sin ya kai kashi 27.44% bisa na duniya baki daya.Daga mahangar fannoni na musamman, a shekarar ta 2025, yawan bayanan da ake samarwa a fannin fasahar kera mutum-mutumin inji mai siffar mutum ya karu da kashi 477.78%, kana na tattalin arzikin samaniya ta kusa da doron kasa ya karu da kashi 75%, wanda hakan ya nuna gagarumin ci gaba da aka samu.
A yau ne aka bude taron koli na gina kasar Sin ta dijital karo na tara a birnin Fuzhou. Taken taron shi ne: “Gaggauta ci gaban kirkire-kirkire na fasahar dijital da kuma zurfafa gina kasar Sin ta dijital.” (Amina Xu)















Discussion about this post