Hukumar kula da makamashi ta kasar Sin ta sanar a yau Alhamis cewa, a rabin farko na bana, kasar ta samu saurin ci gaban ayyukan samar da makamashin da ake iya sabuntawa, har ma a karon farko an samar da sama da kaso 40% na wutar lantarki a kasar daga makamashin da ake iya sabuntawa.
Hukumar ta bayyana haka ne yayin wani taron manema labarai, inda ta ce a rabin farko na bana, yawan lantarkin da aka samar bisa makamashin da ake iya sabuntawa ya kai kusan KWH triliyan 2, adadin da ya karu da kimanin kashi 9%, wanda ya kai kaso 41.2% daga cikin gaba dayan lantarkin da aka samar a kasar.
Daga ciki kuma, yawan lantarkin da aka samar daga makamashin iska da hasken rana ya kai KWH triliyan 1.25, adadin da ya karu da kaso 9.3%.
Har ila yau, yawan lantarkin da aka samar da kwal ya kai KWH triliyan 2.5, wanda ya ragu zuwa kashi 49.7% daga cikin daukacin wutar lantarkin da aka samar a kasar, kuma wannan ne karon farko da adadin ya ragu zuwa kasa da 50%. (Lubabatu)














