Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada aniyarta na ganin an kammala ginin layin dogo mai tsawon kilomita 284 da zai tashi daga Kano zuwa Katsina, tare da ƙaddamar da shi a watan Disambar shekarar 2026. Gwamnatin ta bayar da wannan tabbaci ne duk da wasu ƙalubale na rashin tsaro, da rigingimun filaye, da kuma tafiyar hawainiyar ayyuka a lokacin damina da aka fuskanta a baya.
An bayyana hakan ne a lokacin da jami’an Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya, da Ma’aikatar Kudi, da kuma wakilan cibiyoyin ba da lamuni da ’yan kwangila suka gudanar da bincike na haɗin gwuiwa domin duba yanayin aikin, inda suka nuna cewa an kammala aikin da kashi 80 cikin 100.
Binciken, wanda ya haɗa da gwajin layin dogon da aka kammala daga Kazaure zuwa Katsina, ya nuna cewa an riga an ajiye kayayyakin da ake buƙata don shimfiɗa titin jirgin a sansanin aikin. Da take jawabi bayan binciken a madadin Babban Sakataren Ma’aikatar Sufuri, Darakta mai kula da ayyukan Sufurin Jirgin Kasa, Engr. Habibat Buhari, ta ce aikin na tafiya yadda aka tsara.
Ta bayyana cewa duk da ƙalubalen tsaro a wasu sassan hanyar da kuma kin amincewa da dokar amfani da filaye a wasu al’ummomi, gwamnati na tattaunawa da su don ganin an magance matsalolin, inda ta tabbatar da cewa hakan ba zai hana ƙaddamar da aikin a watan Disamba ba.
A nasa ɓangaren, Darakta a ofishin Babban Sakataren Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya, Alhaji Muhammadu Kamal, ya bayyana cewa gwamnati na fitar da kuɗaɗe yadda ya kamata, inda tuni ta saki nata kaso 15 cikin 100 na kuɗin aikin a matsayin tallafin gwamnati. Ya ce irin aikin da aka riga aka kammala ya nuna ƙwazon gwamnatin wajen cika alƙawarin kuɗi da ke kanta a yarjejeniyar aikin da ake aiwatarwa da kuɗaɗen rance.
Wakilin kamfanin kwangila na Mota-Engil Nigeria, Vladislav Bystrenko, ya tabbatar da cewa kamfaninsu na da niyyar kammala kashin farko na aikin zuwa watan Disamba yadda aka tsara.














