Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya aike da sakon taya murna ga dauka al’ummar Musulmi na Nijeriya a kan murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta, Annabi Muhammadu (S.A.W). A sakon nasa, shugaban ya nemi ‘yan kasa da su yi amfani da wannan lokaci mai albarka don yin addu’o’i na musamman don kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi sassan kasar nan.
Shugaba Tinubu ya yi kira ga Musulmai da su yi koyi da kyawawan halaye da dabi’u na fiyayyen halitta, wadanda suka hada da zaman lafiya, da hakuri, da juriya, da kuma tausayawa juna.
Ya kuma jaddada muhimmancin gina kasa ta hanyar bin doka da oda da kuma girmama dan Adam, inda ya tunatar da cewa babu inda a addini ko a dabi’ance aka amince da ta’addanci, ko garkuwa da mutane, ko zubar da jinin dan Adam.
Tinubu ya kuma roki al’umma da su zama masu sassauci da yin wa juna adalci domin tabbatar da ci gaban tattalin arziki, sannan kuma iyaye da su kula da yara su tashi tsaye wajen tarbiyyar ‘ya’yansu kan kyawawan dabi’u da girmama na gaba.A ranar talata 12 da watan Rabi’ul Awwal wanda ya yi daidai da ranar da aka haifi fiyayyen Halitta Annabi Muhammad S.A.W a gudanar da bukukuwan Mauludi a cikin birnin Katsina da sauran garuruwa.
Kamar kowace shekara ana fara wannan kasaitaccen biki ne a unguwar Yari da misalin karfe 8:00 safe ta hanyar yin tarurruka har zuwa karfe 8:00 na dare.
Ana yin bikin Mauludin da’ira-da’ira inda wasu ke yi karatun Alkur’ani mai girma wasu na yin zikiri a ya yin da wasu ke yi ishiriniya da sauran nau’o’in zikiri domin tunawa da wannan muhimmiyar rana da aka haifi fiyayyen Halitta Annabi S.A.W
Wadannan unguwanni sun shahara wajen soyayya ma’aiki (S) hatta mafi yawan sha’iran birnin Katsina a wadannan unguwanni suke tun iyaye da kakanni.
Wani abin burgewa a wannan Maulud da ake gudanarwa a unguwanni Unguwar Yari da Marna da Masanawa har zuwa Kofar Yandaka ana sanya fararan tufafi ne domin kawata wuraren ga kuma kamshi.
Wani abin ban sha’awa shi ne, matasa ne kashin bayan wannan taro na Maulud a wadannan unguwanni duk da cewa dattawan da suka assasa wannan hidima da su ake yin ta duk shekara.
Ba wai taro da karatutuka kawai ake yi ba, ana raba abinci da abin sha a tsawon wannan lokaci da ake gudanar da wadanda bukukuwa inda jama’a daga sassan birnin Katsina ke halarta duk shekara.
Taron Mauludin da’ira-da’ira na cikin birnin Katsina abu mai dadandan tarihi da ake yi wa tanadi da shiri domin kawata shi da bunkasa shi duk shekara.
Duk dai a wannan rana, ‘yan uwa Musulmi almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky suka gudanar da na su zagayen Mauludin da suka saba yi duk shekara.
Zagayen wanda ya kunshi tawagar wakilin ‘yan uwa almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky Sheikh Yakubu Yahaya Katsina da ‘yan Islamiyya da masu wake da masu fareti da kuma manyan mutane maza da mata ya fara da misalin karfe 9 na safe ya kare da 5:30 na yamma.
Daman dai kamar yadda suka sa yi suna haduwa ne a unguwar madawaki inda alummomi daga bangarori daban-daban na jihar Katsina suke halartar wannan gagarumin taro sannan a fara zagayen.
A wannan shekarar a samun fitowar al’umma kusan fiye da lokutan baya, haka kuma an samu sabbin tsare-tsare daga masu gudanar da taron musamman iri kawa da kwalliya da yara ‘yan Islamiyya suka gwangwaje da ita.
Kamar yadda ake kiran wannan bikin Mauludi shi ne “Zagayen ‘Yan Shi’a” sai dai ba wai ‘yan shi’ar ba ne suke zagaye bikin ba, har da sauran al’umma musamman jama’ar gari da sauran su.
Zagayen ya fara da makarantar Fodiya da ke unguwar madawaki inda suka bi ta Masanawa zuwa Kofar Yandaka suka biyo ta rafin dadi zuwa kwanar Mobil ta sabon layi ta Kerau har zuwa Ladan Wapa
Masu lura da yadda ake tafiyar da wannan zagaye sun yi ittifakin tsawon yawan al’ummar da suka taron a wannan shekarar ya kai kilomita 4 daga farkon muzaharar zuwa karshen ta.
An karkare wannan zagaye da misalin karfe 5:30 na yamma a unguwar filin Samji inda daman bisa al’ada ana ake karkare komi inda Sheikh Yakubu Yahaya Katsina ke yin jawabi bayan an gabatar da faretin ban girma da wassani yara ‘yan Islamiyya daga bisani a yi addu’ar kowa ya tafi abin sa.
Duk da cewa an zagba zafi da rana al’umma sun dake akan manyan titunan da wannan zagaye ya ratsa domin kashe kwalkwatar idon su, musamman ‘yan fareti da ke kawata zagayen kuma al’umma na tsaukin son ganin su.
Kazalika an gudanar da irin wannan zagaye a karamar hukumar Funtua da Malumfashi wanda wakilan ‘yan uwa almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky suka jagoranta a wani yana bai daya.
Wadanda kananan hukumomi sun saba gabatar da wannan zagaye duk shekara wanda ‘yan islamiyya da sha’irai da masu fareti da manyan mutane ke tsaba ado domin wannan murna.
A bana ma, an yi duk da kalubalen rayuwa da ake fuskanta amma hakan bai hana jama’a tsaba ado da kwalliya domin nuna soyayyar Annabi Muhammad (S)a garuruwa Malumfashi da Funtua da ke cikin jihar Katsina.
Wannan rana ta 12 ga watan Rabi’ul Awwal ta kasance wata rana mai dinbin tarihi a jihar Katsina inda ita ma masarautar Daura ta ke gudanar da Sallar Gani wato wani kasaitaccen bikin Mauludi ne mai dadadan tarihi da masarautar ke gudanarwa duk shekara.
Masarautar Daura na daukar baki daga cikin da wajen Nijeriya da kuma duk wani da masarautar ta nada shi sarauta yana halartar wannan biki na. Sallar Gani a garin Daura.
Bisa al’ada gwamnan jihar Katsina ma a Daura yake yin hutun Mauludin wajen halartar bikin Sallar Gani a Daura wato a ranar ta biyu Hawan Magajiya ke nan.
Mai Martaba Sarkin Daura Alhaji Umar Faruk Umar na yi wa al’umma hidima dalilin wannan biki na Mauludin Annabi Muhammad (S) duk shekara inda ake karrama bakin da suka halarci wannan taro musamman wadanda suka zo daga nesa.
Kamar yadda aka saba ana yin kasaitaccen bikin ne tamkar hawan Sallah kuma duk wani mai Sarauta a wannan Masarauta wannan rana yake jira domin baje kolin ado da kawa irin ta sa.
Ko a bana, mutane irin su Dokajin Kasar Hausa, da Gimbiyar Kasar Hausa da Admin Garin Kasar Hausa da Sarkin Takin Kasar Hausa da sauran masu Sarauta irin wannan sun halarci bikin kuma sun ke ce raini wajen sanya sutura da kwalliyar dawakai.
Dadin dadawa masarautar na kwashe kwanaki biyu tana gudanar da wannan biki na Mauludi wanda ake kira Sallar Gani wanda kuma hatta daga jamhuriyar Nijar al’umma na zuwa domin kashe kwalkwatar idon su duk shekara.
Sannan a karshen taron ne ake gane wanda ya cinye taron da ado da kuma kwalliya a tsakanin hakimai da kuma masu sarauta kamar yadda muka bayyana a a sama
Bukukuwan dai na bana sai Allah sam barka musamman ganin yadda al’umma suka nuna matukar soyayya ta hanyar taba ado da kwalliya domin wannan muhimmiyar rana da aka haifi fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (S).














