ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Mece Ce Matsalar Real Madrid? 

by Abba Ibrahim Wada
9 months ago
Madrid

Lokacin da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta naɗa Xavi Alonso a matsayin sabon mai koyarwa, magoya bayan ƙungiyar sun yi farin ciki duba da irin ƙoƙarin da ya yi a tsohuwar ƙungiyarsa ta Bayer Liverkusen.

Ɗan wasa Jude Bellingham gwani ne kuma ƙwararre, amma an kasa samun daidaito tsakaninsa da Mbappe kan yadda za riƙa buga wa ƙungiyar wasa wanda hakan shi ne yake kawo musu tsaiko wajen lissafa ƙwallon yadda ya kamata.

  • Atletico Madrid Ta Zazzaga Wa Real Madrid Ƙwallaye 5 A Metropolitano
  • Real Madrid Ta Shiga Halin Damuwa Bayan Wasanni Uku Ba Tare Da Nasara Ba

Wani lokaci za ka ga cewar zalamar Mbappe ta sa ya koma gurbin ɗan wasan tawagar Ingila, shi ma yana haka, wasu lokutan sai su daburce a gurbi ɗaya wanda hakan yana kawo rashin jituwa.

ADVERTISEMENT

Shi dai Bellingham bai fara buga wa Real wasannin ba a kakar nan, sakamakon jinya, amma ya fara buga mata wasa a wasan hamayya da Atletico ta doke Real Madrid 5-2, wanda ba yadda za ka ɗora alhakin rashin nasarar a kan ɗan ƙwallon saboda shi ne wasansa na farko. Tsakanin watan Oktoba zuwa Nuwamba da aka yi hutu, domin buga wasannin ƙasa da ƙasa,

Bellingham mai shekara 22 ya koma kan ganiyarsa, wanda ya ci ƙwallo ya kuma bayar da ɗaya aka zura a ragar Barcelona a wasan hamayya.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

A wasan Barcelona da wanda Real Madrid ta sharara 4-0 a ragar Ɓalencia ya nuna cewar Bellingham da Mbappe za su iya fitar da Real Madrid kunya idan har kowanne yana kan ganiya.

To sai dai a wasan Elche, Bellingham ne gwarzo, a karawa da Olympiacos a Kofin Zakarun Turai Mbappe ne ya taka rawar gani, amma a wasan Girona ba wanda ya yi fice a fafatawar.

Haka kuma a kakar wasa ta 2023 zuwa 2024 Jude Bellingham da Ɓinicius Junior sun taka rawar gani, waɗanda ke kan ganiya har ƙarshen kakar da ta wuce. To amma tun daga lokacin ƴan wasan ba sa taka rawar gani kamar yadda suka yi a kakar da ta wuce, amma suna iya ƙoƙarin ganin sun fitar da ƙungiyar kunya.

Duk da cewar Mbappe yana cin ƙwallaye tun bayan da ya koma Real Madrid daga Paris St Germain, wasu kan ce yana da son kansa domin a wasu lokutan a wasan Real Madrid sai ka neme shi ka rasa a gurbin mai cin ƙwallaye, sai ka ga an bugo ƙwallon cikin da’ira, amma ɗan ƙasar Faransa na can gefen kusurwa.

Sannan a kakar wasa ta 2023 zuwa 2024, tsohon mai koyar da ƴanwasan ƙungiyar Carlo Ancelotti ya yi amfani da Rodyrgo domin taimaka wa Ɓinicius da kuma Bellingham. Rodyrgo ɗan ƙwallo ne mai hazaƙa tuƙuru, wanda ke aiki sosai da ba kowa yake gane gudunmuwar da yake bayarwa ba a Real Madrid.

Shin Salon wasan Alonso Yana Aiki?

Magoya bayan ƙungiyar suna ganin ya kamata Ɗabi Alonso ya tantance salon da zai riƙa amfani da Jude Bellingham da Kyalian Mbappe da kuma Ɓinicius Junior a kowane wasa da zai yi amfani da su, domin su kasance kan ganiya da ƙwazo.

Hakan zai sa duk ƙungiyar da Real Madrid ta fuskanta ta ɗanɗana kuɗarta a hannun waɗannan ƴan gaba, saboda kowanne mai gwarzo ne da ƙwarewa da gogewa. To amma hakan zai yi wuya a bana a ƙungiyar, kasancewar matasa irin su Arda Guler da Franco Mastantuono suna ƙoƙarin da ya kamata a riƙa fara wasannin da su a kakar nan.

Ƙungiyar tana fuskantar ƙalubale a wasannin da take bugawa a waje, haka kuma canje-canjen da Alonso ke yi bayan kawo gagarumin sauyi, ƙungiyar na samun koma-baya.

A farkon wannan kakar Kylian Mbappe ya karɓi riga mai lamba 10 daga Luca Modric, wanda ya bar Real Madrid a kakar da ta wuce, yayin da aka bai wa Endrick lamba tara.

Me Ya Kamata Real Madrid Ta Yi?

Idan har ƙungiyar Real Madrid tana fatan komawa kan ganiya tana buƙatar gyare-gyaren da za su sa ta ƙara riƙe kambunta. Dole tana buƙatar mai tsare baya daga tsakiya da wani mai tsare bayan amma daga tsakiyar fili da fitatcen mai cin ƙwallaye da kuma ɗan wasan tsakiya ɗaya.

Sannan ƙungiyar dole ta yi duba na tsanaki kan ƴan wasan da ke buga mata ɓangaren gefe da tsarinsu bai yi iri ɗaya da na ƙungiyar ba, kuma ta yi waje da masu yawan jin rauni da suke daɗewa suna jinya da waɗanda ke wasan gurbin tsakiya marasa tasiri.

Bugu da ƙari, ya kamata ta riƙe tsarin salon wasa na 4-3-3, sannan ta fitar da waɗanda take ganin za su iya yin abin da ake buƙata, domin kai hare-hare a koda yaushe. Haka kuma ya kamata kawo yanzu Real Madrid tana da ƴan wasa 11 fitattu da za ta iya fuskantar kowacce ƙungiya, a maimakon yawan sauye-sauye, wanda a wani lokacin hakan ba ya fitar da ita kunya.

Real Madrid tana buƙatar samar da fitatcen mai cin ƙwallaye, za kuma ta iya sa Endrick, kafin ta je kasuwa. Ya kamata a fayyace jagora a Real Madrid ƙarara tsakanin Ɓinicius ko kuma Mbappe.

Kociyan ƙungiyar Xaɓi Alonso yana buƙatar ya yi nazari kan yadda ƙungiyar za ta amfana daga wajen masu buga mata gurbin tsakiya tsakanin Ɓalɓerde da Camaɓinga da kuma Bellingham.

Sannan kuma daga ɓangaren masu tsaron baya ta dogara da Militao, sannan ta sayo wani mai tsare baya daga tsakiya da zarar an buɗe kasuwa. Sai kuma ƙungiyar ta dawo da tasirinta a gasar zakarun Turai, ta hanyar tsare baya yadda ya kamata tun da tana da fitatcen mai tsare raga.

Madrid
Abba Ibrahim Wada
+ postsBio
  • Abba Ibrahim Wada
    https://hausa.leadership.ng/author/abba-ibrahim-wada/
    Yadda FIFA Ta Yi Yunƙurin Sasanta Rikicin Israila Da Amurka A Kofin Duniya
  • Abba Ibrahim Wada
    https://hausa.leadership.ng/author/abba-ibrahim-wada/
    Har Yanzu Nijeriya Tana Fatan Zuwa Kofin Duniya Na 2026
  • Abba Ibrahim Wada
    https://hausa.leadership.ng/author/abba-ibrahim-wada/
    Waye Zai Lashe Ƙyautar Gwarzon Ɗan Wasan Afrika Na 2025?
  • Abba Ibrahim Wada
    https://hausa.leadership.ng/author/abba-ibrahim-wada/
    Ko Ka San Dalilin Da Zai Bai Wa Nijeriya Damar Zuwa Gasar Cin Kofin Duniya?

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana
Wasanni

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

September 8, 2026
Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain
Wasanni

Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain

September 7, 2026
Next Post
An Daƙile Yunƙurin Juyin Mulkin Benin, In Ji Ministan Cikin Gida

An Daƙile Yunƙurin Juyin Mulkin Benin, In Ji Ministan Cikin Gida

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.