Gwamnatin Jihar Kano ta sake buƙatar gwamnatin tarayya da ta hanzarta sakar mata kuɗaɗen tallafi har naira biliyan 5 domin taimaka wa ‘yan kasuwar Singa sakamakon mummunar gobara.
Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Abdullahi Baffa Bichi, ne ya bayyana hakan yayin da yake karɓar baƙuncin shugabannin ‘yan kasuwar da abin ya shafa. Ya ƙara da cewa gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, yana yin dukkan mai yiwuwa don ganin an rage radadin da ‘yan kasuwar suka shiga.
Gobarar, wadda ta auku a farkon shekarar 2023, ta lalata dukiyoyi na miliyoyin naira, wanda hakan ya sa gwamnatin tarayya a ƙarƙashin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta yi alƙawarin tallafin kuɗin, amma har yanzu ba a saki kuɗin ba.
Hukumar kula da ahajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) da takwararta ta jiha (SEMA) sun gudanar da bincike kan asarar da aka yi, amma har zuwa yanzu masu gudanar dai ƴan kasuwar da abin yana shafa na ci gaba da jiran agajin gwamnatin da aka yi alƙawari.














