ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, October 28, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ƴansanda Sun Cafke Mutane 4, Sun Ƙwato Motoci 3 Da Aka Sace A Kano

by Abubakar Sulaiman
2 weeks ago

Rundunar Ƴansandan Jihar Kano ta sanar da cafke wasu mutane huɗu da ake zargi da satar motoci tare da ƙwato motoci uku da aka sace tsakanin ranakun 8 da 9 ga watan Oktoba, 2026. Kakakin Rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, shi ne ya sanar da hakan a madadin Kwamishinan Ƴansandan Jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, yana mai cewa nasarar ta samu ne sakamakon amfani da bayanan sirri da fasahar zamani da dakarun yaƙi da garkuwa da mutane da jami’an shiyyar Ungogo suka gudanar.

Mota ta farko ƙirar Toyota Corolla ce (samfurin 2010), wadda wani Aminu Yahaya daga Unguwar Darmanawa ya ba wani dillali mai suna Sale Usman (wanda aka fi sani da Dambu) a Unguwar Fagge domin ya sayar masa tun ranar 22 ga Satumba. Maimakon ya kawo kuɗin, Dambu ya karkatar da motar zuwa Jihar Katsina, inda ƴansanda suka ƙwato ta a hannun wani mai suna Sulaiman da ya yi ikirarin cewa ya saye ta a kan Naira miliyan 7.5.

Mota ta biyu kuwa wata bas ce ta Toyota Hiace mai lambar NSR 261 XB da aka sato daga Kasuwar Singer a Kano. Jami’an tsaro sun bibiyi sawun motar har zuwa Mariri Magadawa a Ƙaramar Hukumar Kumbotso, inda suka yi nasarar damƙe matasa biyu da ake zargi da aikata satar, wato Abubakar Umar ɗan shekara 23 da Mustapha Zubairu Abdullahi ɗan shekara 25.

ADVERTISEMENT

A ɓangare guda, jami’an sintiri na Shiyyar Ungogo sun tare wata babbar mota ƙirar Mitsubishi Canter mai lambar BLF 365 XA a hannun wani Abdullahi Adamu ɗan shekara 40, a yayin da yake ƙoƙarin kai ta wani gareji a Kadawa domin sauya mata fenti. Yayin da ake yi masa tambayoyi, Adamu ya amsa cewa ya sato motar ne daga Garejin Dan Baba da ke Potiskum a Jihar Yobe, lamarin da ya sa Rundunar Ƴansandan Kano ta tuntuɓi takwararta ta Yobe domin miƙa motar ga ainihin mai ita.

Kwamishinan Ƴansanda CP Bakori ya jaddada cewa za a gurfanar da dukkan waɗanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike, tare da gargaɗin al’umma da su sanya na’urorin tsaro a motocin, su kula da wuraren da suke ajiye su, kuma su guji sayen motoci a farashi mai arhar da ya wuce ƙima domin kauce wa faɗawa cikin laifin sayen kayan sata.

LABARAI MASU NASABA

Majalisar Dattawa Ta Buƙaci A Tsaurara Tsaro Bayan Kashe Mutane A Taraba

Gwamnati Da NLC: Abin Da Ma’aikata Ya Kamata Su Sani Kan Tallafin Sufuri Na ₦70,000

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Biyan Tallafin Sufuri Ga Ma’aikata Naira 70,000 A Duk Wata
  • Abubakar Sulaiman
    ADC-PCC Ta Nemi Majalisa Ta Yi Fatali Da Bashin Tinubu Na Dala Biliyan 20 Da Fam Biliyan Ɗaya
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Buƙaci Majalisar Dattawa Ta Yi Watsi Da Buƙatar Ciwo Bashin Tinubu
  • Abubakar Sulaiman
    INEC Na Fuskantar Suka Kan Amfani Da Manhajar AI

MASU ALAKA

Majalisar Dattawa Ta Buƙaci A Tsaurara Tsaro Bayan Kashe Mutane A Taraba
Labarai

Majalisar Dattawa Ta Buƙaci A Tsaurara Tsaro Bayan Kashe Mutane A Taraba

October 28, 2026
Gwamnati Da NLC: Abin Da Ma’aikata Ya Kamata Su Sani Kan Tallafin Sufuri Na ₦70,000
Labarai

Gwamnati Da NLC: Abin Da Ma’aikata Ya Kamata Su Sani Kan Tallafin Sufuri Na ₦70,000

October 28, 2026
’Yan Bindiga Sun Sace Mata 29 Da Wani Yaro A Jihar Neja
Manyan Labarai

’Yan Bindiga Sun Sace Mata 29 Da Wani Yaro A Jihar Neja

October 28, 2026
Next Post
Ya Kamata Amurka Ta Yi Taka Tsan-Tsan Kan Batun Taiwan

Ya Kamata Amurka Ta Yi Taka Tsan-Tsan Kan Batun Taiwan

LABARAI MASU NASABA

Majalisar Dattawa Ta Buƙaci A Tsaurara Tsaro Bayan Kashe Mutane A Taraba

Majalisar Dattawa Ta Buƙaci A Tsaurara Tsaro Bayan Kashe Mutane A Taraba

October 28, 2026
Tsibirin Lemu: Wuri Mai Ni’ima Da Ke Kunshe Da Tarihin Gwagwarmayar Kafuwar Kasar Sin

Tsibirin Lemu: Wuri Mai Ni’ima Da Ke Kunshe Da Tarihin Gwagwarmayar Kafuwar Kasar Sin

October 28, 2026
Sin Da Gambia Sun Gudanar Da Taron Musayar Kwarewa A Kungiyar Ciniki Ta Duniya

Sin Da Gambia Sun Gudanar Da Taron Musayar Kwarewa A Kungiyar Ciniki Ta Duniya

October 28, 2026
Sin Ta Yi Kira Da a Gaggauta Tsagaita Bude Wuta Tare Da Yin Tattaunawa Cikin Ruwan Sanyi Tsakanin Amurka Da Iran

Sin Ta Yi Kira Da a Gaggauta Tsagaita Bude Wuta Tare Da Yin Tattaunawa Cikin Ruwan Sanyi Tsakanin Amurka Da Iran

October 28, 2026
Gwamnati Da NLC: Abin Da Ma’aikata Ya Kamata Su Sani Kan Tallafin Sufuri Na ₦70,000

Gwamnati Da NLC: Abin Da Ma’aikata Ya Kamata Su Sani Kan Tallafin Sufuri Na ₦70,000

October 28, 2026
’Yan Bindiga Sun Sace Mata 29 Da Wani Yaro A Jihar Neja

’Yan Bindiga Sun Sace Mata 29 Da Wani Yaro A Jihar Neja

October 28, 2026
Sin Da Karin Kasashe 25 Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar MDD Ta Inganta Hada-Hadar Dakon Hajoji

Sin Da Karin Kasashe 25 Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar MDD Ta Inganta Hada-Hadar Dakon Hajoji

October 28, 2026
Abubuwan Da Ke Hana Yaran Arewacin Nijeriya Zuwa Makaranta

Abubuwan Da Ke Hana Yaran Arewacin Nijeriya Zuwa Makaranta

October 28, 2026
Majalisar Dokokin Sakkwato Ta Amince Da Kafa ’Yansandan Jihohi

Majalisar Dokokin Sakkwato Ta Amince Da Kafa ’Yansandan Jihohi

October 28, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Shirin Bayar Da Lamunin Gidaje Mara Kuɗin Ruwa A Kano

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Shirin Bayar Da Lamunin Gidaje Mara Kuɗin Ruwa A Kano

October 28, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.