ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ƴansanda Sun Gano Bindiga Ƙirar AK-47 Da Ake Alaƙantawa Da Shugaban Wata Kungiyar Sa-Kai (Vigilante)

by Rabi'u Ali Indabawa
5 months ago

Wani haɗin gwiwar jami’an Ƴansandan tare da sauran hukumomin tsaro ya kai ga rushe sansanonin ƴan ta’adda da ake amfani da su wajen garkuwa da mutane da sauran laifuffuka a yankunan Ipo da Igwuruta-Ali da ke karamar hukumar Ikwerre a Jihar Rivers.

A yayin aikin, an kama mutum guda tare da ƙwato makamai da harsasai, ciki har da bindigar pump-action, bindiga kirar AK-47 guda ɗaya, da na’urorin sadarwa. An kuma bayyana cewa wasu da ake zargi da zama a sansanonin sun tsere.

  • Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
  • Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar, Blessing Agabe, ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a Port Harcourt ranar Talata, inda aka aikawa manema labarai.

ADVERTISEMENT

Agabe ta bayyana cewa bindigar pump-action din ana zargin ta shugaban wata ƙungiyar sa-kai ta tsaro ta OSPAC ce, wanda aka ce ƴan bindiga sun yi garkuwa da shi a lokacin da ya jagoranci mutanensa domin fuskantar su a makon da ya gabata.

Sanarwar ta ce, “Rundunar ƴansandan Jihar Riɓers na sanar da jama’a nasarar wani haɗin gwiwar aikin tsaro da aka gudanar kan ƴan ta’adda a jihar.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

“Bisa umarnin Sufeto Janar na ƴansanda, rundunar na ci gaba da aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin ƙara kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da ƙarfafa haɗin kai tsakanin hukumomi.

“A ranar 12 ga Afrilu, 2026, da misalin ƙarfe 1:00 na rana, rundunar ta haɗu da sauran hukumomin tsaro ciki har da Nigerian Rundunar Sojojin Ƙasa ta Nijeriya,– Rundunar Sojojin Ruwa ta Nijeriya – Rundunar Sojojin Sama ta Nijeriya– Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Ƙasa (DSS) – Hukumar Tsaro da Kariya ta Farar Hula ta Nijeriya domin ƙaddamar da wani aiki na musamman don rushe sansanonin ƴan ta’adda da ake zargin suna ɓoyewa a wuraren.”

Ta ƙara da cewa a yayin aikin, jami’an tsaron sun gano wuraren boye ƴan ta’adda a sansanonin Ipo da Igwuruta-Ali.

A yayin aikin, an ƙwato kayayyaki kamar haka: bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya, bindigar pump-action guda daya, harsasai 274 na 7.62mm, harsasai guda huɗu, kayan kariya na gargajiya, wata babbar almakashi ta ƙarfe, rediyon sadarwa da sauran kayayyaki.

Binciken farko ya nuna cewa bindigar pump-action ɗin na iya zama ta shugaban ƙungiyar tsaro ta OSPAC wanda aka yi garkuwa da shi a baya.

Sanarwar ta ƙara da cewa an yi nasarar rushe sansanonin ƴan ta’addan, yayin da aka kama mutum guda a yankin, wanda ake ci gaba da bincike a kansa, yayin da sauran suka tsere kafin isowar jami’an tsaro.

Ta ce ana ci gaba da bincike domin cafke waɗanda suka tsere da kuma ceto wanda aka yi garkuwa da shi.

A halin da ake ciki, Kwamishinan ƴansandan jihar, Olugbenga Adepoju, ya tabbatar wa al’ummar jihar ƙudirin rundunar na kare rayuka da dukiyoyi.

Sai dai ya buƙaci jama’a da su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro haɗin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai cikin lokaci domin kama masu aikata laifuka cikin gaggawa.

Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Next Post
Nijeriya Ce Kan Gaba Wajen Wulaƙanta Abinci A Afirka – EU

Nijeriya Ce Kan Gaba Wajen Wulaƙanta Abinci A Afirka - EU

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.