Ɗan takarar gwamnan Jihar Gombe na jam’iyyar (NDC), Sadiq Abubakar, ya ƙalubalanci ɗan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar PDP, Farfesa Isa Ali Pantami, da ya fito su fafata a muhawarar siyasa a bainar jama’a gabanin zaɓen gwamnan jihar na shekarar 2027.
A cewarsa, wannan tattaunawa za ta bai wa al’ummar Jihar Gombe damar fahimtar wanda ke da kyawawan manufofi da tsare-tsaren da za su ciyar da jihar gaba.
Abubakar ya yi wannan ƙalubalen ne cikin wata sanarwa da ya fitar ga ’yan jarida jiya, inda ya ce taron zai bai wa ’yan takarar damar gabatar da manufofinsu, tsare-tsarensu da hangen nesansu kan ci gaban jihar.
Ya ce hakan zai bai wa al’ummar jihar damar tantance fahimtar ’yan takarar game da shugabanci da abubuwan da suka sanya a gaba wajen tsara manufofi, maimakon dogaro kacokan da kalaman yaƙin neman zaɓe.
A cewarsa, za a kuma bai wa al’ummar Gombe damar saurare kai-tsaye daga bakin ’yan takarar kan matsalolin da suke addabar al’umma da matakan da suke shirin ɗauka idan aka zaɓe su.
Abubakar ya ce irin wannan muhawara na daga cikin muhimman ginshiƙan dimokuraɗiyya, domin tana bai wa ’yan takara damar tattauna batutuwan da suka shafi al’umma, tare da bai wa masu kaɗa ƙuri’a damar nazarin shirye-shiryensu da hanyoyin da suke son bi wajen magance matsalolin jama’a.
Saboda haka, ya yi kira ga Pantami da ya amince da ƙalubalen tare da shiga tattaunawar da za ta mayar da hankali kan ci gaba da walwalar al’ummar Jihar Gombe.
Ɗan takarar NDC ya ce ya kamata a mayar da hankali kan batutuwan shugabanci, bunƙasar tattalin arziki, ilimi, kiwon lafiya, tsaro da samar da ayyukan yi.
Ya ƙara da cewa, bai kamata tattaunawar ta karkata zuwa son zuciya ko muradun jam’iyya ba, sai dai a mayar da makomar Jihar Gombe a matsayin muhimmin batu.
Abubakar, wanda ya taɓa riƙe muƙamin Shugaban Matasa na Ƙasa na jam’iyyar (APC), ya fice daga jam’iyyar zuwa NDC a shekarar 2026, inda daga bisani ya zama ɗan takarar gwamnan Jihar Gombe na jam’iyyar a zaɓen 2027.













