ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: Da Wuya A Samu Ɗan Takarar Da Zai Iya Kayar Da Tinubu – Orji Kalu

by Sadiq
1 month ago

Sanata Orji Kalu ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu har yanzu shi ne ɗan takarar da ya fi ƙarfi a fafatawar da za a yi a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, duk da ƙalubalen tattalin arziƙin da Nijeriya ke fuskanta.

Da yake magana a shirin siyasa na gidan talabijin na Channels, Kalu ya ce sauye-sauyen tattalin arziƙi da gwamnatin Tinubu ta aiwatar sun fara daidaita tattalin arziƙin ƙasar.

Ya ce canjin kuɗi, farashin man fetur da kuma zuba jari daga ƙasashen waje na ci gaba da inganta, amma ya amince cewa har yanzu ‘yan Nijeriya na fama da tsadar rayuwa.

ADVERTISEMENT

Kalu ya danganta matsalar tattalin arziƙi da matsalolin da duniya ke fuskanta da kuma rashin tsaro.

Ya ce hare-haren ‘yan bindiga da masu tayar da ƙayar baya sun hana manoma da dama komawa gonakinsu, lamarin da ya jawo hauhawar farashin kayan abinci.

LABARAI MASU NASABA

Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Janye Wa Atiku Ba A Zaɓen 2027 – Peter Obi

Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

Ya kuma yi watsi da zargin cewa Shugaba Tinubu ba shi da kyakkyawar alaƙa da Cocin Katolika.

A cewarsa, cocin na da damar bayyana ra’ayinta kan al’amuran ƙasa, kuma shugaban ƙasa na girmama shugabanninta.

Dangane da zaɓen 2027, Kalu ya ce jam’iyyar APC na da tabbacin za ta ci gaba da zama a kan mulki.

Ya bai wa Tinubu maki 65 cikin 100 kan yadda yake tafiyar da mulki, yana mai cewa gwamnati ta samu nasarori a fannonin gine-ginen more rayuwa, tsaro da sauye-sauyen tattalin arziƙi, sai dai ba ta yi isasshen bayani ga jama’a kan waɗannan nasarori ba.

Ya kuma ce kundin tsarin mulkin Nijeriya ya bai wa ‘yan ƙasa damar yin zanga-zangar lumana, amma ya gargaɗi mutane da su yi taka-tsantsan wajen yaɗa labaran ƙarya da bayanan da ke yawo a kafafen sada zumunta.

MASU ALAKA

Manyan Labarai

Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Janye Wa Atiku Ba A Zaɓen 2027 – Peter Obi

September 11, 2026
Cutar Kwalara Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuƙe
Manyan Labarai

Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

September 11, 2026
Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato
Manyan Labarai

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Next Post
Fusatattun Matasa Sun Ƙone Motar KAROTA Bayan Aukuwar Hatsari A Kano

Fusatattun Matasa Sun Ƙone Motar KAROTA Bayan Aukuwar Hatsari A Kano

LABARAI MASU NASABA

Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwarzon Gwamnan Shekarar 2026 Kwamared Nasir Idris

September 11, 2026

Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Janye Wa Atiku Ba A Zaɓen 2027 – Peter Obi

September 11, 2026
Farashin Siminti Zai Ragu Idan Farashin Kayan Aiki Ya Sauka – BUA

Gwarzon Shekarar 2026 Abdulsamad Rabiu

September 11, 2026
Cutar Kwalara Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuƙe

Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

September 11, 2026
Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

September 10, 2026
Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

September 10, 2026
Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.