ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: Magoya Bayan Tinubu Sun Yi Watsi Da Sukar Takarar Musulmi-Musulmi Da Kwankwaso Ya Yi

by Sadiq
2 months ago

Magoya bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu sun yi watsi da sukar da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi kan tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC na Musulmi da Musulmi.

Sun ce batun ba shi da wani tasiri a siyasa kuma ba zai zama abin tattaunawa ba yayin da ake tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

Magoya bayan sun mayar da martani ne bayan Kwankwaso ya ce tikitin takarar Musulmi da Musulmi zai ci gaba da zama babban batu a zaɓen 2027, musamman ganin cewa Shugaba Tinubu ya ci gaba da tafiya da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, a matsayin abokin takararsa.

ADVERTISEMENT

Da yake magana da manema labarai a Abuja a wani taron kwana ɗaya da ƙungiyar North Central Agenda (NCA) ta shirya kan ci gaban tattalin arziƙi, tsari da ayyukan more rayuwa a yankin Arewa ta Tsakiya ƙarƙashin gwamnatin Tinubu, Darakta Janar na Tinubu Support Group (TSG), Dakta Umar Tanko Yakasai, ya ce sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023 ya riga ya kawo ƙarshen wannan muhawara.

Yakasai ya ce mutane da dama sun yi hasashen cewa tikitin Musulmi da Musulmi zai hana Tinubu samun nasara a zaɓen 2023, amma duk da haka ‘yan Nijeriya sun zaɓe shi.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Ya ƙara da cewa yankin Arewa ta Tsakiya, duk da yawan Kiristocin da yake da shi, ya amfana da muƙaman gwamnati da kuma ayyukan more rayuwa a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu.

A cewarsa, ya kamata a riƙa auna gwamnati bisa irin ayyukan da take yi, ba bisa addinin shugabanninta ba.

Ya kuma buƙaci ‘yan siyasa su mayar da hankali kan matsalolin da suka shafi ci gaban ƙasa maimakon sake tayar da muhawara kan addinin ‘yan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC.

Sai dai Kwankwaso ya bayyana cewa tikitin Musulmi da Musulmi zai ci gaba da kasancewa muhimmin batu a zaɓen 2027.

Ya ce ya yi mamakin yadda Shugaba Tinubu ya ci gaba da tafiya da wannan tsari duk da cece-kucen da ya haifar kafin zaɓen shekarar 2023.

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Next Post
NNPP Ta Yi Barazanar Maka INEC A Kotu Kan Ƙin Bin Umarnin Dawo Da Tambarinta A Kan Lokaci

NNPP Ta Yi Barazanar Maka INEC A Kotu Kan Ƙin Bin Umarnin Dawo Da Tambarinta A Kan Lokaci

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.