ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: Sheikh Muhajjadina Sani Kano Ya Bukaci ‘Yan Siyasa Su Kai Zuciya Nesa

by Bello Hamza
4 months ago
Siyasa

A daidai lokacin harkokin siyasa suka kankama, ‘yan siyasa daga bangaren masu mulki da kuma bangaren ‘yan adawa sunata fafutukar ganin sun tabbata a kan karagar mulki ko kuma sun kwace ragamar mulki a matakai daban-daban a fadin tarayyar kasar nan, wani shaharren Malamin addinin Musulunci da ke garin Kano wanda kuma shi ne Shugaban Kungiyar Masu Ilimin Taurari na Nahiyar Afrika Sheikh Muhajjadina Sani Kano ya nemi ‘yan siyasa su kai zuciyar su kai nesa tare da nisantar kalaman batanci da duk wani abin da zai iya ruguje ginshikan zaman lafiya da tattalin arzikin kasar nan.

Sheikh Muhajjadina ya yi wannan bayanin ne a tattaunawarsa da manema labarai a ofishinsa da ke Abuja. Ya ce, wannan kiran ya zama dole musamman ganin yadda fagen harkokin siyasar kasar ke daukar zafi, a inda bangarori daban-daban ke kokari kama madafun iko ta kowacce hanya.

“A ‘yan kwanakin nan ‘yan siyasa suna ta sauya sheka daga jam’iyyar siyasa zuwa wata, hakan ya sa wasu ke ganin an ci amanar su, wasu kuma na ganin tsawon shekara 4 da wasu suka yi suna mulki ba a kyauta musu ba saboda haka za su tabbatar da sauyi ko ta halin kaka” in ji shi

ADVERTISEMENT

Ya kara da cewa, wannan mataki yana da hadari ga rayuwar kasar nan ta bangarori da dama musamman ganin dama kasar na fama harkokin ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda a jihohi da dama ga shi kuma muna fuskantar matsalar tattalin arziki sakamakon matakai da tsare-tsaren gwamnati mai mulki, a wannan lokaci ne kuma muke bukatar ganin ba a samu wanin abin da za su tayar da hankula ba.

Ya kuma yi kira ga ‘yan siyasa da al’umma gaba daya da su kusanci masu ilimin Taurari domin neman fassara da shawarwwari a kan abubuwan da suke fuskanta. Ya ce tabbas akwai kalubale a gaban shugabannin kasar nan amma cikin ikon Allah “Za mu yi nasarar kawo karshen matsalar tsaro da tattalin arzikin da muke fuskanta a yanzu” in ji shi

LABARAI MASU NASABA

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

Daga karshe ya nemi ‘yan Nijeriya masu zabe da su natsu sosai tare da nazarin wadanda za su zaba a dukkan matakai, “Bai kamata mutum ya biye ma Taliya ko kudi dan kalilan wajen zaben wanda zai hau karagar mulki na tsawon shekara 4 ba. Kamata ya yi a duba mutumin da ya fi cancanta wanda zai kawo ayyukan raya kasa. ‘ in ji shi.

Siyasa
Bello Hamza
+ postsBio
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Jihar Kano Za Ta Amfana Matuka Da Gidauniyar Aliko Dangote – Masu Ruwa Da Tsaki
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    An Nuna Damuwa Kan Sake Kamun Da DSS Ta Yi Wa Boɗejo Bayan Samun Belin EFCC
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Dole Al’ummar Arewa Su Rungumi Hanyoyin Kasuwanci Na Zamani —Alfa Musa
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Ba Mu Taba Biyan Kudin Fansa Ba Kuma Ba Za Mu Biya Ba – Kwamishinan Katsina

MASU ALAKA

Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa
Labarai

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila
Manyan Labarai

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Next Post
INEC Ta Sake Sanya Shugabancin ADC Na David Mark A Shafinta Na Yanar Gizo

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.