Ƙungiyar Christian Social Movement of Nigeria (CSMN) ta buƙaci ’yan Nijeriya su nemi shugaba mai gaskiya, ƙwarewa, tawali’u, adalci, riƙon amana da mutunta mutuncin ɗan Adam daga wanda zai zama shugaban ƙasar a zaɓen 2027.
Shugaban kwamitin gudanarwa na ƙungiyar, Elder Sunday Oibe, ne ya bayyana hakan ranar Litinin, yayin gabatar da wani daftarin manufofi a taron manema labarai da aka gudanar ta yanar gizo.
Oibe ya yi gargaɗin cewa matsalolin Nijeriya ba su samo asali daga ƙarancin albarkatu kaɗai ba, har ma da gazawar shugabanci, raunin tsarin bin diddigin ayyukan gwamnati da ƙarancin riƙon amana.
Ya ce shugaban ƙasa na gaba ya kamata ya ɗauki mukamin da aka ba shi a matsayin amanar al’umma, ba dukiyar kansa ba, tare da fahimtar cewa dukiyar gwamnati ta jama’a ce.
Ƙungiyar ta bayyana cewa shugaba nagari ya kamata ya jajirce wajen kare rayukan jama’a, kiyaye Kundin Tsarin Mulki, yaƙi da cin hanci da rashawa, kula da dukiyar ƙasa yadda ya kamata da samar da damar da za ta taimaka wa ’yan ƙasa su inganta rayuwarsu.
Ƙungiyar ta kuma ce Nijeriya na buƙatar shugabanni masu hidimar jama’a, maimakon ’yan siyasar da ke amfani da addini, ƙabila ko talauci wajen yaudarar masu zaɓe domin samun mulki.
Ta jaddada cewa dole ne shugaban ƙasa na gaba ya tabbatar da kare haƙƙin dukkan ’yan ƙasa ba tare da nuna bambanci bisa addini ba.
Haka kuma, ƙungiyar ta buƙaci shugaban ya mutunta Sashe na 10 da Sashe na 38(1) na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999, kamar yadda aka yi wa kwaskwarima.
Sashe na 10 ya haramta ɗaukar wani addini a matsayin addinin hukuma na ƙasa, yayin da Sashe na 38(1) ya tabbatar da ’yancin tunani, lamiri da addini.
CSMN ta nuna damuwa kan hare-haren da ake ci gaba da kai wa al’ummomi, nuna wariya ta addini da abin da ta bayyana a matsayin rashin daidaito wajen kare rayukan ’yan ƙasa.
Ta yi gargaɗin cewa rashin hukunta masu aikata laifuka na iya ƙarfafa masu tsattsauran ra’ayi su ci gaba da aikata ta’addanci.
Ƙungiyar ta ce dole ne shugaban ƙasa na gaba ya ƙarfafa dimokuraɗiyya tare da tabbatar da cewa gwamnati tana kare kowane ɗan ƙasa daidai da sauran jama’a.
CSMN ta danganta waɗannan buƙatu da shirinta na haɗa ’yan takarar shugaban ƙasa Kiristoci 13 domin tattaunawa kan yiwuwar cimma matsaya ɗaya a tsakaninsu gabanin zaɓen 2027.
Ta bayyana cewa manufarta ba ita ce kawai tantance wanda zai zama shugaban ƙasa ba, a’a, tana son inganta shugabanci nagari da zai dawo da tsaro, adalci da fata a zukatan ’yan Nijeriya.
Ƙungiyar ta kuma yi kira ga ’yan Nijeriya, musamman Kiristoci, da su shiga harkokin siyasa cikin sanin ya kamata, maimakon su tsaya kan koke-koke kawai.
Ta buƙaci ’yan ƙasa su riƙa tantance ’yan takarar shugaban ƙasa bisa halayensu, ƙwarewarsu da jajircewarsu wajen yi wa al’umma hidima, maimakon la’akari da addini ko ƙabila.
CSMN ta jaddada cewa shiga siyasa ga Kiristoci bai kamata ya tsaya ga neman kujerar mulki ba, ya kamata ya kasance wata hanya ce ta inganta shugabanci nagari da gina Nijeriya da za ta amfani kowa.













