ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, September 12, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: Tsohon Kakakin Majalisar Kaduna Abdulfatah Ya Zama Ɗan Takarar Gwamnan PRP

by Sadiq
3 months ago

Jam’iyyar PRP ta zaɓi tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Rt. Hon. Aminu Abdulfatah, a matsayin ɗan takararta a zaɓen gwamna na 2027.

A cikin wata sanarwa, jam’iyyar ta ce an cimma wannan matsaya ne bayan shawarwari da tattaunawa mai zurfi tsakanin ‘yan takararta, inda aka amince a tsayar da ɗan takara guda domin a fuskanci zaɓen cikin haɗin kai.

PRP ta bayyana Abdulfatah a matsayin gogaggen ɗan siyasa kuma mai ƙwarewa a harkokin shugabanci da mulki, wanda ya shafe shekaru da dama yana hidimar jama’a.

ADVERTISEMENT

Ya taɓa riƙe muƙamin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, sannan ya kuma riƙe wasu muƙamai a hukumomin gwamnati daban-daban.

Jam’iyyar ta ce kasancewarsa a majalisa ya taimaka wajen ƙarfafa tsarin dimokuraɗiyya da inganta aikin dokoki a jihar.

LABARAI MASU NASABA

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna

A cewar PRP, zaɓensa ta hanyar haɗin kai ya nuna zaman lafiya da dunƙulewar jam’iyyar, tare da burin kawo sauyi mai kyau a Jihar Kaduna.

Jam’iyyar ta ƙara da cewa tana fatan magance matsalolin rashin tsaro, rashin aikin yi, talauci da rashin ingantaccen shugabanci idan ta samu nasara a 2027.

Haka kuma ta ce tana ci gaba da riƙo da manufofinta na gaskiya, adalci da mulkin jama’a, wanda ya samo asali daga jagoranta marigayi Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa.

PRP ta bayyana cewa ta yi shirin lashe zaɓen gwamna na 2027 a Jihar Kaduna.

MASU ALAKA

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu
Manyan Labarai

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna
Siyasa

Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna

September 9, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Next Post
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Gwanjon Kadarori: Kotun Daukaka Kara Ta Kori Karar Da Sani Sha'aban Ya Shigar

LABARAI MASU NASABA

Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku

Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku

September 12, 2026
An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro

An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro

September 12, 2026
Shekaru 22 Bayan Rushewar Nigeria Airways, Gwamnati Ta Biya Ma’aikata 2,700 Biliyan 18

Shekaru 22 Bayan Rushewar Nigeria Airways, Gwamnati Ta Biya Ma’aikata 2,700 Biliyan 18

September 12, 2026
Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

September 12, 2026
Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

Sanata Yari Ya Gudanar Da Taron Masu Ruwa Da Tsaki A Zamfara

September 12, 2026
Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Motocin Aiki Ga Manyan Makarantu A Zamfara

Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Motocin Aiki Ga Manyan Makarantu A Zamfara

September 12, 2026
Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

September 12, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Jam’iyyar APC Ce Za Ta Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa Da Gwamnoni A Nijeriya -Dikko Raɗɗa

September 12, 2026
NNPCL Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa ₦860 Kan Kowacce Lita – IPMAN

Mene Ne Ra’ayinku Kan Dawo Da Tallafin Man Fetur Ko Barin Sa?

September 12, 2026
Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

September 11, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.