ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwanjon Kadarori: Kotun Daukaka Kara Ta Kori Karar Da Sani Sha’aban Ya Shigar

by Bello Hamza and Sulaiman
3 months ago
Kotu

Kotun Daukaka Kara ta Tarayya dake Kaduna ta Kori takardar daukaka karar da lauyoyin Alhaji Mahmood Sani Sha’aban, suka shigar na a dakatar da hukuncin da wata Babbar kotun Jihar ta yanke na bada umurnin yin gwanjon wasu kadarorin Hon. Sani Sha’aban don biyan bashin da Alhaji Umar Faruk Abdullahi ke binsa bisa rashin cika sharudda.

Da farko dai lauyan mai kara, Halima Fumilola Olodo, ta gabatar da takardar daukaka karar dake neman dakatarwa da kara wa’adin hukuncin da babbar kotun baya ta yanke don baiwa wanda suke wakilta damar biyan kudaden da kansa a maimakon a bar ma Wanda ke bin bashin damar yin gwanjon.

Sai dai a na shi bangaren, lauya mai kare wanda Ake kara, Mista Abdullahi Yahya SAN, ya janyo hankalin kotun kan cewa masu karar sun saba ka’ida tun daga kan lokacin shigar da karar da rashin cika wasu ka’idoji na gabatar da takardar daukaka karar, da rashi mutunta umurnin da Babbar kotun baya ta yanke a kan lokacin da ya kamata a biya bashin.

ADVERTISEMENT

Sannan Mista Abdullahi Yahya SAN ya nemi kotun da ta sa Masu Kara su biyasu diyar rabin miliyan sakamakon bata lokacin da rashin cimma umurnin kotun baya.

Bayan sauraron bangarorin biyu, Justice Onyekachi Aja Otisi ta kotun daukaka karar ta Tarayya, ta kori takardar daukaka karar da lauya mai kare Wanda ke kara ta shigar, bisa rashin cika ka’idoji shigar da karar a kotun daukaka karar ta tarayya dake Kaduna, sannan ta nemi ya biya tarar naira dubu dari biyu ga masu karar kamar yadda lauyan mai kare wanda ake karar ya nema.

LABARAI MASU NASABA

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota

‘Yansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Damfarar Wayar Salula A Jihar Adamawa

Da yake karin bayani game da wannan Zama lauyan wanda ake kara, Mista Abdullahi Yahya SAN, ya ce, da wannan korar karar da aka yi, ya Basu damar Cigaba da aiki da wancan hukuncin da kotun bayan ta yanke na yin gwanjon wasu daga cikin kadarorin Hon. Mahmood Sani Sha’aban don biyan bashin da Alhaji Umar Faruk Abdullahi ke binsa.

A nata bangaren lauyan mai kara, Halima Fumilola Olodo, ta tabbatar da cewa rashin cika wasu daga cikin ka’idojin shigar da karar a kotun daukaka karar ya sa aka kori karar.

Ita dai wannan shari’ar ta samo asali ne daga wata yarjejeniyar bashi da aka sanya wa hannu a shekarar 2018 tsakanin Hon. Sani Mahmood Sha’aban (Dan Buran Zazzau) da Alhaji Umar Faruk Abdullahi domin taimaka wa Sha’aban ya samu ‘yanci daga matsalar kama shi da tsare shi da akayi a gidan yari a Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), a wancan shekarar.

An ba Sha’aban bashin dala miliyan ɗaya na Amurka ($1,000,000) da kuma naira miliyan 11.2 ba tare da riba ko ruwa ba, bisa tanade-tanaden shari’ar Musulunci, tare da sharadin cewa zai mayar da bashin cikin watanni shida.

Lauyoyin Sha’aban ne suka tsara tare da shaida yarjejeniyar, sannan ɗansa ya sanya hannu a madadinsa kafin daga bisani, bayan dawowarsa daga gidan yari, shi ma ya sanya hannu domin amincewa da ita.

Sha’aban ya riga ya fara biyan chabar kudi har dala $290,762 daga cikin bashin dala miliyan ɗaya, amma daga baya ya ƙi biyan ragowar bashin. Daya daga cikin sharuɗɗan yarjejeniyar ita ce a biya bashin cikin watanni shida tare da mayar da shi da irin kuɗin da aka karɓa da su.

Kotu
Bello Hamza
+ posts Bio
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Jihar Kano Za Ta Amfana Matuka Da Gidauniyar Aliko Dangote – Masu Ruwa Da Tsaki
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    An Nuna Damuwa Kan Sake Kamun Da DSS Ta Yi Wa Boɗejo Bayan Samun Belin EFCC
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Dole Al’ummar Arewa Su Rungumi Hanyoyin Kasuwanci Na Zamani —Alfa Musa
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Ba Mu Taba Biyan Kudin Fansa Ba Kuma Ba Za Mu Biya Ba – Kwamishinan Katsina
Kotu
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
  • Sulaiman
    Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

MASU ALAKA

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota
Kotu Da Ɗansanda

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota

July 18, 2026
An Kama Matashi A Kano Kan Zargin Kashe Abokinsa
Kotu Da Ɗansanda

‘Yansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Damfarar Wayar Salula A Jihar Adamawa

July 18, 2026
Disu
Kotu Da Ɗansanda

IGP Disu Ya Hana Jami’an Ƴansanda Yin Amfani Da TikTok Da Instagram Da Sauransu

June 26, 2026
Next Post
Gwamnatin Kwara Ta Kai Saraki Kotu Kan Zargin Ɓata Sunan Gwamna AbdulRazaq

Gwamnatin Kwara Ta Kai Saraki Kotu Kan Zargin Ɓata Sunan Gwamna AbdulRazaq

LABARAI MASU NASABA

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.