ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027:Gwamnoni Na Fuskantar Turjiya Wajen Gwagwarmayar Kare Kujerunsu Da Kuma Samar Da Magadansu

by Yusuf Shuaibu
3 months ago
Gwamnoni

A yayin da jam’iyyu ke samar da ‘yan takara a jihohi 28 da za a gudanar da zaben gwamna a 2027, gwamnonin da wa’adinsu ya kare na kokarin samar da magadansu, yayin da kuma gwamnonin da ke wa’adi na farko na fafutukar ci gaba da rike kujerunsu, wanda suke fuskantar turjiya wajen wannan gwagwarmayan.

Babu zaben gwamna a jihohi bakwai a 2027. Sai dai kuma sauya sheka da karyewar kawance da tasirin ci gaba da zama a kan kujerar mulki sun kasance abubuwan da za su yi tasiri ga ‘yan Nijeriya a wannan lokacin.

An bayyana cewa a yanzu haka an samu turjiya wajen gwagwarmayar kula da gwamnati a fadin jihohi 18 na arewacin Nijeriya. Jam’iyyun siyasa sun fito da ‘yan takararsu. Manya masu tasiri sun zabi bangarorinsu. Yayin da a wasu jihohi, mutanen da suka kasance a abokan siyasa a baya yanzu sun zama abokan gaba.

ADVERTISEMENT

Zaben gwamnoni a 2027 a arewacin Nijeriya za a fafata shi ne a fannoni da dama kasancewar a yanzu an samu rarabuwan kawukana da kabilanci da rashin tsaro da kuncin tattalin arziki da kuma tasirin siyasar uban gida.

Daga cikin jihohin arewa da fafatawar za ta fi zafi, akwai Kaduna, wanda aka samu ‘yan takara uku masu karfi da suka hada da Gwamna Uba Sani na jam’iyyar APC da Shehu Usman Bawa (wanda aka fi sani da Shehu ABG) na jam’iyyar PDP da kuma tsohon dan takarar gwamna, Isa Ashiru, na jam’iyyar ADC, masana harkokin siyasa na ganin wannan fafatawa za ta yi zafi sosai.

LABARAI MASU NASABA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

Sani ya shiga fafatawar ne da damarmaki guda biyu, kasancewarsa a matsayin gwamna da kuma zama dan takarar jam’iyya mai mulki ta APC da ta riga ta kafu. Amma Ashiru, wanda ya sha kaye a wurin Sani a shekarar 2023, manasa na ganin cewa hadin gwiwar siyasa ne mai karfi tare da tsohon Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai, mutum da ake dauka a matsayin ruhin siyasar adawa a Jihar Kaduna.

El-Rufai da Sani sun kasance abokan tafiya na kusa a baya, yanzu wannan alakar ta kau, kuma tana iya yin tasiri wajen kawo wa gwamnan cikas.

A Kano, Gwamna Abba Yusuf na fuskantar kalubale a harkokin siyasa na rayuwarsa. Bayan ya sauya sheka daga NNPP zuwa APC, zai isa zaben 2027 ba tare da kungiyarsa ta Kwankwasiyya da ta taimaka masa wajen samun nasarar a 2023 ba.

Uban gidansa na siyasa kuma tsohon gwamnan Jihar Kano, Dakta Musa Kwankwaso, ya bude kofa ga tsohon mataimakin gwamna Gwarzo, ana sa ran zai dauki tutar jam’iyyar NDC tare da samun goyon bayan Kwankwasiyya.

Yayin da PDP a bangaren Wike ta tsayar da Dakta Muhammad Bello Dalha, sannan akwai Sheikh Ibrahim Khalil daga jam’iyyar ADC. Duk da hayaniyar da ke ciki, masana harkokin siyasa suna ganin cewa har yanzu Yusuf yana da tasiri a jihar, sai dai idan kungiyar Kwankwaso ta yi cikakken aiki.

A Jihar Benuwai, Gwamna Reb. Fr. Hyacinth Alia, na jam’iyyar APC, wanda ya samu mulki a 2023, yana fuskantar adawa daga tsohon alkalin alkalai na tarayya, Cif Michael Aondoakaa na jam’iyyar PDP, wanda ke da karfin a matakin jihar da kuma goyon bayan daga tsohon gwamnan jihar, Samuel Ortom.

Tsohon dan majalisar wakilai, Herman Hembe na jam’iyyar ADC da babban lauya, Sebastian Hon, na jam’iyyar SDP sun kara karfin fafatawar. Amma fa, gwamna yana da tasiri sosai a siyasar jihar.

Fafatawar ta fi sauki a Jihar Taraba. Gwamna Agbu Kefas, bayan ya samu tikitin APC, yanzu yana fuskantar farazana daga Sanata Emmanuel Bwacha, abokin hamayyarsa na APC a 2023, wanda ya koma PDP kuma aka tabbatar da shi a matsayin dan takarar gwamna.

Sai dai rikicin cikin gida a cikin PDP na Taraba, ya rage karfin fafatawar adawa, yayin da INEC har yanzu ba ta tabbatar da dan takara ba.

A Adamawa, yin ritaya na Gwamna Fintiri ya bude damar kowa da kowa. APC na dogara ne kan tsohon shugaban hukumar PTDF, Ahmed Tijjani Galadima, yayin da PDP ta fitar da Dakta Maurice Bonolboki, wanda ya dawo cikin jam’iyyar cikin hanzari kwanaki kafin zaben fid da gwani bayan zargin an ware shi a APC.

Mafi yawan masu nazarin harkokin siyasa suna ganin tsohon mataimakin shugaban kasa, Abubakar Atiku, wanda ke neman shugaban kasa a jam’iyyar ADC, yana da tasiri sosai a Adamawa. Goyon bayansa ga dan takarar ADC na iya zama babban abin da zai juya sakamakon zaben.

Borno da Yobe sun ci gaba da kasancewa manyan ginshikan APC mafi tasiri a arewacin Nijeriya. Tun dawowar dimokuradiyya a 1999, babu jam’iyyar adawa da ta taba lashe zabe na kujerar gwamna a kowanne daga cikin jihohin.

Dukkan gwamnonin jihohin sun kammala wa’adinsu guda biyu, APC a Borno ta cimma matsaya kan dan takara na hadin gwiwa, Injiniya Mustapha Gubio, wanda gwamna mai barin gado Babagana Zulum yake goyan baya, yayin da APC na Yobe ta goyi bayan tsohon sakataren gwamnatin jihar, Baba Malam Wali, wanda shi ne magajin da Gwamna Mai Mala Buni ya fi so. Jam’iyyar adawa suna nan a duk jihohin biyu amma ba su da wata barazana mai tasiri.

A Jihar Filato, Gwamna Caleb Mutfwang, wanda ya yi abin mamaki ya bar PDP zuwa APC a farkon shekarar 2026, ya lashe zaben fid da gwani na APC da kuri’u sama da 233,000. Tare da cikakken goyon baya daga shugaban jam’iyyar APC, Farfesa Nentawe Yilwatda, Mutfwang zai shiga zaben ne a matsayin babban dan takara mai farin jini.

Babban mai kalubalensa, Kefas Wungak Ropshik na jam’iyyar PDP, yana samun taimakon jama’a, amma yana fuskantar babban kalubale na rikin jam’iyyarsa.

Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, sabon mamba ne a APC, ana hasashen zai ci gaba da rike kujerarsa. Mai kalubalantarsa mafi karfi shi ne Sanata Kabiru Marafa na jam’iyyar NDC, wani babban jigon a siyasa a jihar, wanda masana sun ce, yana iya rage tasirinsa kadan saboda barin APC.

A Nijar, Gwamna Muhammed Bago na da tarihin wajen samar da ababen more rayuwa da biyan albashin ma’aikata, wanda ya ba shi tasiri a jihar. A Sakkwato, Gwamna Ahmed Aliyu yana samun cikas saboda karuwar rashin tsaro da kuma kalubale mai inganci daga tsohon mataimakin gwamna, Manir Daniya na ADC.

A Jihar Kebbi, Gwamna Nasir Idris na fuskantar turjiya daga wurin tsohon ministan shari’a, Abubakar Malami na ADC, wani dan takara mai karfi.

A Katsina, Gwamna Dikko Radda zai fafata da Lado Danmarke na PDP, wanda ya kasance abokin hamayyarsa a 2023, a cikin wani zabe mai tsananin tasiri sosai.

Daga cikin jihohi 19 arewacin Nijeriya, ana has ashen cewa APC za ta iya rike akalla gwamnonin 12. Amma a Kaduna, Kano, Adamawa, Bauchi da Taraba, sakamakon har yanzu bai bayyana ba, kuma a nan ne za a samu makomar siyasar Nijeriya a arewa.

Gwamnoni
Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027:Kamun Ludayin Yakin Neman Zaben Manyan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa

MASU ALAKA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
Tambarin Dimokuradiyya

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

September 5, 2026
Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
Tambarin Dimokuradiyya

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

September 4, 2026
Ko INEC Na Da Hannu A Rikice-rikicen Jam’iyyun Siyasa A Nijeriya?
Tambarin Dimokuradiyya

INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027

August 28, 2026
Next Post
Ma’aikatar Wajen Sin Ta Yi Karin Bayani Game Da Ziyarar Da Xi Zai Yi A Koriya Ta Arewa

Ma’aikatar Wajen Sin Ta Yi Karin Bayani Game Da Ziyarar Da Xi Zai Yi A Koriya Ta Arewa

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.