ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Batun Dakile Shan Taba Sigari A Tsakanin Yara A Nijeriya

by Leadership Hausa
3 months ago
Taba

Majalisar Dinkin Duniya ce, ta ayyana duk ranar 31 na watan Mayun ko wacce shekara, a matsayin ranar yaki da shan Taba Sigari.

Taken taron na 2026 wanda ta kaddamr shi ne, “Dakile Sanadarin Cikin Sigari Da Ke Sanya Mutum Ya Dawwama Yana Shaye Shaye wato a turance Nicotine da kuma zukar ita kanta Tabar Sigari”.

Wannan taken dai, ya zo kan gaba a kasar nan duba da yadda ake ci gaba da samun, karuwar masu shanta, ciki har da wasu yaran kasar.

ADVERTISEMENT

A nan, ba wai ana nunfin Nijeriya ta gaza yakar dabi’ar bane, sai kawai, yadda ake kara samun yawan wasu shaguna a kasar, da ake sayar da ita, tamkar ana sayar da Biskit ko Alawa.

Abin dubi a nan shi ne, yadda wasu matasan kasar, suka rungumi dabi’ar, babu kakkautawa, musamman duba da cewa,  akalla matasan kasar, daga tsakanin kaso hudu zuwa kaso 5.6 ko akalla zuwa kaso bakwai zuwa sha daya, na yin dabi’ar

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

Wannan adadin idan aka kwatanta, bai na yawan sauran matasa a duniya, da ke yin dabi’ar ba.

Bisa wasu alkaluma da Hukumar Kula da Dakile Shan Taba Sigari ta Kasa wato NTCA ta fitar a kwanan baya, sun nuna cewa, a kasar nan, a duk yara dalibai biyar masu shekaru daga tsakanin 13 zuwa 15, ana samun daya, da ke zukar Taba Sigari

Kazalika, a duk cikin yaran goma, akawi daya sun yi nisa, a yin dabi’ar.

Wasu alkaluma sun bayyana cewa, a duk shekara, akalla ‘yan Nijeriya 30,000 ke utuwa, saboda kamuwa da cutkan da suka shafi yin tu’ammli da shan Sigari, musamman kansar Huhu.

A gafe daya kuma, wadanda suka kamu da cutukan, a duk shekara, na kashe akalla Naira biliyan 211.2, wajen duba lafiyarsu.

Bugu da kari, matsalar na kuma sanya wa, Nijeriya na yin rashin matasa, maso tasowa, saboda kamuwa da cutuakan, da ke da alaka, da shan Taba Sigari.

Nijeriya ba wai ta kasance, Kara zube bane, wajen samar dokoki, musamman  na dakile yin dab’ar ba, domin kuwa, an kirkiri, da Hukumar  Kula da Dakile Shan Taba Sigari ta Kasa,  inda kuma kasar, ta kasance, tana daga cikin kasashen, da suka rattaba hannun yarjejeniya Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya, kan dakile yin dabi’ar

Wannan Jaridar, a bayyane,  matsalar da ke son bajewa a Faifai shi ne, batun samar da dokar dakile dabi’ar, da kuma batun tsarara,  wanzar da matakan  dakile ta.

Alamu na nuna cewa, ba wai kadai dogara kan dokar hana bayar da tallan Sigarin a kafafe ko kuma bin ka’ido ne, batun ba, amma rashin nuna da gasken da ake yi, na wanzar da dokar yadda za ta yi tasiri a kasar, shi ne babban kalubalen.

Haka zalika, batun iya sayen Sigari ta kafar Yanar Gizo da aka kirkro a kasar, hakan ya sanya, ana ci gaba da samun wawagegen gibi, na wanzar da dokar a kasar, yadda ta kamata.

Muna kira ga Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta Tarayya da Hukumar  Kula da Dakile Shan Taba Sigari ta Kasa NTCA da kuma Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasa wato NAFDAC, da su kara kaimi, wajen daukar matakan da suka kamata, domin a rage matsalar.

Ya zama wajbi, Gwamnati ta tashi tsaye haukan, domin dakile yin amfani da kuma sayar da duk wata na’uin Taba Sigari, musamman wadda masana’an suka sarrafa, da sanadaran da ke sanya dandano.

Bugu da kari ya zama wajibi, gwamnatin ta kara tsaurara matakai, kan tallan Taba Sigari a kafafen tallace-tallace, musamman domin a ceto rayuwar yaran kasar, wadanda sune, manyan gobe.

Akwai matukar bukatar, mahukunta a kasar, su tabbatar da sun kara jabga haraji kan masana’antun da ke sarrafa Sigari.

Kazalika, akwai bukatar duba lafiyar matasan kasar, da suka rungumi, wannan dabi’ar.

A nan, muna jinjinawa kungiya ta da ke yaki da shan Taba Sigari ta kasa wato NCS bisa kirkiro da kungiyar matasa da ke yin gangamin wayar da kai, kan illolin dabi’ar.Wannan salon, zai taimaka wajen wayar da kan matasan kasar da suka rungumi dabi’ar, yin watsi, da ita.

Akwai kuma matukar bukatar, yin hadaka da Gwamnati tare da zuba kudade a cikin shirye-shiyen kiwon lafiya.

A duk shekara, wasu masna’antu a kasar nan, na sarrafa wasu kaya masu lahani, da ke shafar lafiyar dubban matasan kasar.

Hakan ba wai, batu ne, na harkar kasuwanci ba, amma wani tsari ne, da aka kitsa a zamanance, domin tarwatsa rayuwar matasan.

Abin takaicin shi ne, rashin mayar da hankali a bangaren masu rike da madafun iko na siyasa, domin a dakile dabi’ar a kasar baki daya.

Muna kira ga Gwamnatin kasar da ta dauki matakan gaggawa, domin tsamo, musamman matasan kasar nan, daga cikin matsalar.

Taba
Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja
  • Leadership Hausa
    Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed
  • Leadership Hausa
    Batun Dawo Da Tallafin Mai Da Atiku Ya Yi Na Ci Gaba Da Tayar Da Kura
  • Leadership Hausa
    Batun Guguwar Kakar Yakin Neman Zabukan 2027 A Nijeriya

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Next Post
Dimokuradiyyar Nijeriya A Shekara 27:Ba Yabo Ba Fallasa

Dimokuradiyyar Nijeriya A Shekara 27:Ba Yabo Ba Fallasa

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.