• English
  • Business News
Friday, October 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

A Magance Rashin Aikin Yi A Tsakanin Matasa

by Leadership Hausa
2 years ago
Matasa

Rashin aikin yi a tsakanin matasanmu abin takaici ne a halin yanzu, bisa yadda lamarin ke karuwa duk kuwa da dimbin arzikin albarkatun kasa da na mutane da Allah ya hore mana.

Lamarin a duk shekara sai karuwa yake yi inda matasan da suka kammala karatunsu na jami’a da sauran manyan makarantu ke tururuwar neman aiki da nufin samar wa kansu mafita da abin da za su rufa wa kansu asiri, amma kuma sai su fahimci babu wani kwarin gwiwa na samun aiki a duk inda suka fuskanta, a haka kuma za a ga matasa da yawa suna yawo a kan titunanmu suna talla, a daidai lokacin da ya kamata a ce suna can sun samu aiki mai muhimmanci da za su fuskanci rayuwa da shi. A rahoton cibiyar auna karfin tattalin arziki ta JPMG ya nuna, yawan matasa marasa aiki a Nijeriya ya kai kashi 37.7 a shekarar 2022.

  • Hajjin 2024: NAHCON Za Ta Sabunta Ka’idojin Ciyar Da Alhazai Da Masaukansu
  • Gwamnan Sakkwato Zai Saya Wa Kansa Motocin Biliyan Daya

Hasashen ya kuma nuna cewa, yawan marasa aikin zai ci gaba da karuwa zuwa kashi 40.6 a shekara musamman ganin yadda masu neman aikin ke karuwa a sassan Nijeriya.

Cibiyar ta nuna tafiyar hawainiyar da tattalin arzikin kasa ke yi da kuma ganin ba yadda zai iya karbar sabbin matasa fiye da miliyan 4 zuwa 5 da suke shigowa fagen fafutukar neman aiki a duk shekara. Abin takaici a nan shi ne a halin yanzu Nijeriya ce a kan gaba a fadin duniya a matsayin kasar da ta fi kowacce kasa yawan marasa aikin yi, kamar dai yadda kiddigar da aka fito da ita a kwanan nan ta nuna.

Yawan marasa aikin yi a Nijeriya ya kai fiye da kashi 33.3, wannan abin tsoro ne don kuwa mun zarce yawan na kasar Afirka ta Kudu da suke da kashi 32.9 da kasar Iran mai kashi 15.55. Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ba ta kai ga fitar da rahoto wannan shekarar ba zuwa yanzu, babu wanda zai iya karyata wannan lamarin. Rashin aiwatar da tsare-tsaren da za su kai ga bunkasa tattalin arzikin kasa ya ci gaba da zaftare abin da ke shiga aljihun al’ummar kasa gaba daya. Yadda al’ummar Nijeriya ke karuwa da kashi 3.2 yana kara dagula lamarin rashin aikin yi ga matasa. Barnar da rashin aikin yi ke yi a cikin al’umma ta tashi daga ta tattalin arziki zuwa haifar da kanana da manyan laifuka a tsakanin matasa a sassan Nijeriya.

LABARAI MASU NASABA

Madallah Da Hutu Ga ‘Yan Sakandire Domin Azumi 

Ya Kamata A Biya Yaran Da Aka Gurfanar Saboda Zanga-Zanga Cikakkiyar Diyya – Ajiyan Yawuri

Masana sun danganta karuwar rashin aikin yi a tsakanin matasa da yadda ake samun karuwar matsalar tsaro da aikata muggan aiki. Rashin aiki yana tunzura mutane fadawa ayyukan rashin gaskiya saboda neman hanyoyin samun mafita ta rayuwa, wanda hakan kuma ke haifar da karuwar matsalolin tsaro a sassan Nijeriya. Wani abin tayar da hankali kuma shi ne yadda matsalolin tsaro kamar fashi da makami, kashe-kashe, garkuwa da mutane da sauran ayyukan ta’addanci suka ci gaba da karuwa saboda yadda matasa ke fuskantar rashin aikin yi kuma ga shi suna son rufa wa kansu asiri.

Tsaface-tsaface, da yadda ake karrama wadanda suka yi kudi ta hanyar da bai dace ba, a bayyana yake nuna yadda kungiyoyin masu aikata laifuka suke kara karfi a sassan Nijeriya. Jami’an tsaro na ta fafutukar ganin sun kawo karshen masu aikata laifi ba tare da samun nasarar da ake bukata ba, inda hakan ya sa wasu gwamnoni suka yi watsi da hakkin da ke kansu na kare rayuka da dukiyoyin al’umma tare da barin ‘yan ta’adda suna cin karensu babu babbaka. Ayyukan ta’addanci da dama da suka hada da garkuwa da mutane da zaluntar marasa karfi na ta daukar sabon salo a cikin al’umma. Wadannan ayyukan ta’addanci na kara karfafa salon maganan nan ne da ke cewa, “zuciyar da ba a ba ta aiki ba za ta nema wa kanta aiki.”

Ra’ayin wannan jaridar a nan shi ne, wadannan matsalolin sun taimaka matuka wajen durkushe ci gaban kasar nan. Binciken da aka gudanar daban-daban musamman ma wanda Ezeajughu Mary C. (PhD), ya yi, ya nuna dangantaka ta kut da kut a tsakanin rashin aikin yi da yadda ayyukan ta’addanci ke habaka a Nijeriya.

Babu shakka, akwai hanyoyin magance matsalar rashin aikin yi a tsakanin matasa, wanda baya ga magance matsalolin tsaro zai kuma tabbatar da bunkasar tattalin arzikin kasa ba tare da bata lokaci ba. A kan haka ya kamata gwamnatoci a dukkan matakai su karfafa kokarinsu na samar wa matasa ayyukan yi a duk inda suke a fadin kasar nan.

Ganin muhimmancin kanana da matsakaitan masanan’antu da kuma yadda manyan kamfanoni ke tserewa zuwa kasashensu, ya kamata a rugumi farfado da sabbin kananan masa’anantu, ta haka za a tabbatar da bunkasar tattalin arzikin kasa.

Dole gwamnati ta samar da yanayi mai muhimmanci da zai kai ga bunkasa rayuwar matasa tare da samar musu da ayyukan yi, wannan na daga cikin abubuwan da zai kawar da hankalinsu daga aikata laifuka, a kan haka akwai bukatar samar da dokokin da za su rage wahalhalun da ake fuskanta wajen kafa kamfanoni da kuma cire harajin da ake karba a wajen masu niyyar kafa masana’antu a fadin Nijeriya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Madallah Da Hutu Ga ‘Yan Sakandire Domin Azumi 
Ra'ayoyi

Madallah Da Hutu Ga ‘Yan Sakandire Domin Azumi 

March 18, 2025
Ya Kamata A Biya Yaran Da Aka Gurfanar Saboda Zanga-Zanga Cikakkiyar Diyya – Ajiyan Yawuri
Ra'ayoyi

Ya Kamata A Biya Yaran Da Aka Gurfanar Saboda Zanga-Zanga Cikakkiyar Diyya – Ajiyan Yawuri

November 10, 2024
Nijeriya
Ra'ayoyi

Ra’ayoyin ‘Yan Nijeriya A Kan Zagayowar Ranar Samun ‘Yancin Kai

October 5, 2024
Next Post
Fintiri Ya Gabatar Da Kasafin 2024 A Gaban Majalisar Dokokin Adamawa

Fintiri Ya Gabatar Da Kasafin 2024 A Gaban Majalisar Dokokin Adamawa

LABARAI MASU NASABA

An Jinjinawa Tallafin Kamfanonin Sin Ga Tsarin Bunkasa Masana’antun Senegal

An Jinjinawa Tallafin Kamfanonin Sin Ga Tsarin Bunkasa Masana’antun Senegal

October 9, 2025
Masu Kallon Fina-Finai Na Sin Sun Gamsu Da Fina-Finan Da Aka Gabatar A Lokacin Hutun Bikin Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar Sin Ta 2025

Masu Kallon Fina-Finai Na Sin Sun Gamsu Da Fina-Finan Da Aka Gabatar A Lokacin Hutun Bikin Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar Sin Ta 2025

October 9, 2025
‘Yansanda Sun Kama Motar Hilux Ɗin Da Aka Sace A Kano A Hanyar Zuwa Nijar

‘Yansanda Sun Kama Motar Hilux Ɗin Da Aka Sace A Kano A Hanyar Zuwa Nijar

October 9, 2025
Sin Na Ci Gaba Da Goyon Bayan Kawo Karshen Rikicin Gaza

Sin Na Ci Gaba Da Goyon Bayan Kawo Karshen Rikicin Gaza

October 9, 2025
TCN

Jami’an Tsaro Sun Cafke Ɓarayin Kayayyakin Turakun Wutar Lantarki Na Hanyar Mando Zuwa Jos

October 9, 2025
An Yi Tafiye-tafiye Miliyan 16.34 Da Suka Shafi Shiga Da Fita Daga Kasar Sin Yayin Hutun Kwanaki 8 Na Kasar 

An Yi Tafiye-tafiye Miliyan 16.34 Da Suka Shafi Shiga Da Fita Daga Kasar Sin Yayin Hutun Kwanaki 8 Na Kasar 

October 9, 2025
Nijeriya Ta Yi Asarar Ganga Miliyan 13.5 Na Ɗanyen Mai Ta Hanyar Sata Da Zagon-ƙasa – NEITI

Nijeriya Ta Yi Asarar Ganga Miliyan 13.5 Na Ɗanyen Mai Ta Hanyar Sata Da Zagon-ƙasa – NEITI

October 9, 2025
Duniya Ta Kara Ganin Bunkasuwar Sin a Lokacin Hutun Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar

Duniya Ta Kara Ganin Bunkasuwar Sin a Lokacin Hutun Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar

October 9, 2025
Fursunoni Ba Za Su Samu Damar Kada Kuri’a Ba A Zaben 2023 – INEC

Batun Umarnin Kotu Na Kama Tsohon Shugaban INEC Ƙage Ne Kawai – Shugaban Jam’iyyar AA 

October 9, 2025
An Samu Karuwar Sayayya Yayin Hutun Bikin Kafuwar Kasar Sin

An Samu Karuwar Sayayya Yayin Hutun Bikin Kafuwar Kasar Sin

October 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.