ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bukatar Kawo Karshen Akidar Kyamar Baki A Kasar Afirka Ta Kudu

by Leadership Hausa and Sulaiman
4 months ago
Baki

Abin takaici ne, matuka, kan yadda wasu ‘yan kasar Afirka ta Kudu, ke ci gaba da cutar da ‘yan Nijeriya da ke zaune a kasar da kuma sauran wasu ‘yan cirani, da suka shiga cikin kasar da suka  fito daga kasashen da ke Afirka.

Akasarin ‘yan cirianin sun tsallaka iyakokin kasashen su, zuwa cikin kasar Afrika ta Kudu ne, saboda samun sa’ida, kan zaman kuncin rayuwa da matsatin attalin arziki da suke fuskanta a kasashen su, domin su samu ayyukan da za su, rufawa kansu asiri

Tarihin Afrika ta Kudu dai, ba zai taba cika ba, ba tare da Ambato sunan dangwagwarmayar nemowa kasar ‘yancin kai ba wato Nelson, musamman duba da cewa, a wancan lokacin, Nijeriya ta tsaya tayin daka, domin ganin kasar, ta samu ‘yancin kanta, amma sai dai, abin bakin ciki, a yau sai wasu ‘yan Afika ta Kudu, suka mayar da kasar fagen daga, na dirkawa ‘yan Nijeriya na jiki, har da ma, kaiwa ga kashe wasunsu.

ADVERTISEMENT

Kazalika, ana kuma ta kone shagunan ‘yan Nijeriya, inda iyalai, ke ci gaba da kulli Kucciya, duba da yadda a makwannin da suka shige, wasu ‘yan Afirka ta Kudu marasa imani, suka hallaka wasu ‘yan Nijeriya biyu.

Ana dai yin amfani da wata kungiya a kasar da ake kira da Dudula, bisa nufin aikata manufar, musamman domin ganin an yiwa bakin haure a kasar, korar Kare, kuma babbar manufar kungiyar shi ne, domin a kai hare-haren kan bakaken fata.

LABARAI MASU NASABA

Batun Shayar Da Jarirai Nonon Uwa Da Ƙalubalen Abinci Mai Gina Jiki

Buƙatar Kawo Ƙarshen Dogon Layi A Tashoshin Sayen Iskar CNG

Karin wani abin takaicin shi ne, duk irin wannan cin mutucin da ake yiwa bakin haren, ana yi masu ne, a gaban jami’an tsaro, inda jami’an tsaron, suke  nuna halin ko in kula, kan ta’asar da ‘yan Afirka ta Kudu, suke aiwatarwa.

A nan za mu iya cewa, ofishin jakadanci na Nijeriya da ke a birnin Johannesburg, ya yi gaskiya, kan fitar da sanarwar gargadin ‘yan Nijeriya da ke a Afirka ta Kudu, musamman ‘yan kasuwa, da su tabbatar da sun kulle shagunansu, domin kaucewa, masu kai hare-haren.

Dan katabus din da shugaban kasar Cyril Ramaphosa ta bakin Ministan kula da harkokin cikin gida na kasar Ronald Lamola, shi ne, yin tir, da kai hare-haren.

A gafe daya kuma, Ministan kula da harkokin ‘yan sanda na kasar Firoz Cachalia, ya ayyana nuna kymar ta bakaken fata da ke  zaune a kasar, a matsayin, abin da kasar, ba za ta laumunta ba.

Za a iya cewa, wadannna kalaman nasu, sun yi dai-dai, amma a bangare daya, za a iya cewa, ba su da wani alfanu, domin kuwa, kalamai ne da mahkuntan kasar, suka saba yi, shekaru da dama da suka shude, matukar ana samu irin wannan yanayin, na cin zarfin bakaken fata a kasar.

Misali, a irin wannan nuna wayar launin fata an hallaka bakin haure 62 tare da tarwatsa dubbansu, daga matsugunan su, a 2008.

Kazalika, kai hare-haren a kan bakaken fata, ya basu daga  yankin Durban  zuwa Johannesburg, a 2015, wanda sai da ta kai ga, an tura dakarun sojin kasar, domin kwantar da kura.

Bugu da kari an samu kai wasu hare-haren, kan ‘yan kasuwa ‘yan Nijeriya a 2019, inda lamarin ya kai ga, gwamnatin tarayya ta wancan lokacin, ta yiwa babban kwamishinan kasar nan kiranye da kuma ‘yan Nijeriya, inda lamarin ya kai ga, harzuka wasu ‘yan Nijeriya, suka gudanar da zanga-zangar, yunkurin kai hare-hare, a kan ‘yan Afirka ta Kudu, da ke a jihar Legas da Abuja.

Duk da yin tir da mahukuntan Afirka ta Kudu ke yi kan wannan halin dabbacin na wasu .

Abin tambaya a nan shi ne, shin akwai wani abu da ya sauya?

Hakazalika, a 2026,  an ci gaba da hallaka ‘yan Nijeriya a Afirka ta kudu, lamarin da ya sanya, a karo na hudu ko na biyar,  a tarihin kasar, aka yiwa mukaddashin babban Kwamishinan kasar nan, kiranye, zuwa Abuja.

A ra’ayin wannan Jaridar,  matsin tattalin arziki da ya yiwa wasu ‘yan Afrika ta Kudu tsanani ne, musamman duba da cewa, rashin aikin yi a kasar, ya kai kaso 33, inda wannan kason, ya haura kusan na duniya, sai  su ke fakewa da Guzuma, sun harbin Karsana, wato cin zarafin ‘yan Nijeriya, har da ma, kai wa matakin hallaka su.

A gefe daya kuma, jami’iyyar ANC mai mulki a kasar, nauyi ya yi mata, musamman kan gazawar ta, ba samarwa da ‘yan kasar, ababen more rayuwa, wanda hakan ya sanya, wasu ‘yan kasar, suka buge da cin mutuncin ‘yan Nijeriya, da ke zaune a kasar.

Bugu da kari, wasu kwararru da suka tofa albarkacin bakin su, sun yi ittifaki da cewa, gazawar gwamnatin kasar, hakan ya kara sanya wa, wasu ‘yan Afirka ta kudu, huce fishin su, a kan bakingazawaryanayin da daukar daukar hukunci a kan bakin hauren, domin kawai, su fice daga cikin kasar.

Wani abu da ‘yan kasar Afirka ta kudu suka jahilta shi ne,  ‘yan Afirka da ke a kasar suke da shugunan da suke gudanar da kasuwancin su a Soweto, ba su ne hummul haba’isin janyo rashin aikin yi a Afirka ta kudu ba, hakan ‘yan kasuwa ‘yan Nijeriya da ke a Johannesburg, ba su ne makasudin gazawar gwamnatin ANC, na samar da ingantaccen tsarin tattalin arzikin kasar ba.

Kazalika, ‘yan kwadago ‘yan kasar Zimbabwean da ke a birnin Cape Town, ba su da wata nasaba da gazawar kebe wani gwagwabin kaso, a cikin ksafin kudi, na Cape Town, domin gwamnatin jihar, ta samar da ababen more rayuwa ga ‘yan jihar.

A nan, za a iya cewa, shuwagabanin baya, da suka mulki kasar a baya, su ne, suka fi cancanta, a dorawa laifin   yanayin da kasar, ke ci gaba da fuskanta, har zuwa yau.

Kusan gum da shuwagabannin kasar suka kan cin mutuncin bakin hauren, ya nuna a zahiri, suna kawai tsoron fushin ‘yan kasar ne.

A nan, za mu iya cewa, matakan da gwamnatin tarayya ta dauka, na kwaso ‘yan Nijeriya zuwa gida abu ne, da ya dace, inda aka fara dawo da mutane 130 tare da kuma yiwa babban mukaddashin kwamishina na kasar nan, kiranye.

Sai dai, babbar tambayar da ta kamata Nijeriya da kungiyar AU su bijiro da ita ita ce, ya batun matakan da za a dauka, kan irin kisan gillar da ake yiwa bakaken fata bakin haure, a Afirka ta kudu?

A kwanan baya, an ruwaito Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya bayyana takaicinsa, kan hare-haren nuna wayar launin fata da bakaken fata, ke kai wa a kan ‘yanuwansu, bakaken fata inda ya yi nuni da cewa, wannan halin na rashin imani, ba shi da wani bagire ko kusa, a cikin harkar mulkin Demokiradiyya, na kowacce irin kasa.

Ya zama tilas gwamnatin Afirka ta kudu, ta gaggauta cafkewa tare da kuma hukunta duk wanda aka samu da hannu, na kai hare-haren domin a hukunta su.

Bugu da kari, mika ta’aziyya da mahukuntan Afirka ta kudu suka yi kan kasan bakin hauren, bai wadatar ba, dole ne a tabbatar da an samar da adalci, ga iyalan ‘yan Nijeriya da hare-haren ya rutsa da su.

Baki
Leadership Hausa
Website |  + posts Bio
  • Leadership Hausa
    Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja
  • Leadership Hausa
    Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed
  • Leadership Hausa
    Batun Dawo Da Tallafin Mai Da Atiku Ya Yi Na Ci Gaba Da Tayar Da Kura
  • Leadership Hausa
    Batun Guguwar Kakar Yakin Neman Zabukan 2027 A Nijeriya
Baki
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Baki
Ra'ayinmu

Batun Shayar Da Jarirai Nonon Uwa Da Ƙalubalen Abinci Mai Gina Jiki

August 14, 2026
Buƙatar Kawo Ƙarshen Dogon Layi A Tashoshin Sayen Iskar CNG
Ra'ayinmu

Buƙatar Kawo Ƙarshen Dogon Layi A Tashoshin Sayen Iskar CNG

July 31, 2026
Ana Ci Gaba Da Tafka Muhawara Kan Shirin Gwamnati Na Haramta Masana’atun Sarrafa Robobi
Ra'ayinmu

Ana Ci Gaba Da Tafka Muhawara Kan Shirin Gwamnati Na Haramta Masana’atun Sarrafa Robobi

July 10, 2026
Next Post
Sin Za Ta Ci Gaba Da Aiki Tare Da Sassan Kasa Da Kasa Wajen Wanzar Da Zaman Lafiya A Gabas Ta Tsakiya

Sin Za Ta Ci Gaba Da Aiki Tare Da Sassan Kasa Da Kasa Wajen Wanzar Da Zaman Lafiya A Gabas Ta Tsakiya

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.