ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Abin Da Ya Sa Matatar Ɗangote Ta Ƙaryata Iƙirarin Dillalan Man Fetur 

by Abubakar Abba
2 months ago
Ɗangote

Mahukuntan Matatar Man Ɗangote, sun ƙaryata iƙirarin kamfanin dilalancin Mai na  S&P Global na cewa, Ɗangote, na shigo da Man, daga ƙasar Lomé bayan Matatar ta fitar da shi, zuwa ƙasar ta Lome, inda take yin hada-hadar kasuwancinsa, a ƙara Togo.

A cewar Matatar ta Ɗangote, wannan iƙirarin na S&P Global, bai da wani tushe, ballanta wata makama, kuma an kitsa hakan ne, domin a kawai, a karkatar da kan jama’a.

“Wannan zargin kan Matatar, babu wasu bayanai, da suka goyi bayan iƙirarin, na cewar Matatar na hada-hadar Man a ƙasar Togo, “ Inji sanawar da mahukuntan Matatar suka fitar.

ADVERTISEMENT

A cewar sanarwar, ɗaya daga cikin nauyin da ke a Matatar ta Ɗangote, shi ne, sarrafa Man da zai wadaci ƙasar, kuma Matatar za ta ci gaba da kasancewa, kan gaba wajen samar da Man a cikn ƙasar.

Sanarwar ta jaddda cewa, zargin Matatar na shigo da Man, ya saɓa ƙa’idar manufar da aka kafa Matatar ta Ɗangote.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

A cewar mahukuntan, duk wani batu da ya shafi ɗaukacin kwangilar sayar da Man da duk wata yarjejeniya, ko kuma shigo da Man, mahukuntan Matatar,  sun haramta yin hakan.

“Idan aka ƙiyasata tsadar kuɗaɗen da za a kashe wajen yin jigilar Man metric tan. daga Matatar Mai ta ƙasar Lomé, zuwa cikin ƙasar nan, tsadasr za ta kai zuwa dala 82.

“Matatar Man ta Ɗangote, ba ta yin ragi wajen shigo da Man, ballantana, ta cike giɓin tsadar kuɗin jigilar shigo da Man, cikin ƙasar nan ba, domin yin gasa kawai, ta ƙirƙiri tsadar Man a cikin kasuwannin sayar da Man, a cikin ƙasar

Sanawar ta ci gaba da cewa, babu wani mai Sarrafa mai da zai iya jurewa ciki giɓin tsadar yin jigilar Man domin shigoa da shi, zuwa cikin ƙasar.

Mahukuntan sun bayyana cewa, Matatar, na bin dukkanin ƙa’aidar da ta dace, wajen yin jigilar Man Matatar a zuwa cikin ƙasar nan.

Ta ƙara da cewa, ta bin wannan ƙa’idar ce, domin ta tabbatar da cewa, ta rabar da Man a ɗaukacin faɗin Nijeriya.

Sanarwar ta bayyana cewa, wannan iƙirarin na kamfanin S&P Global, ƙarya ce, tsagwaronta domin Matatar ta Ɗangote, na gudanar da ayyukanta ne, bisa ƙa’ida.

A cewar sanarwar, Matatar ta Ɗangote, ta kasance kan gaba a ƙasar nan, wajen yin gangamin rage yadda ake shigo da Man Fetur zuwa cikin Nijeriya.

Sanarwar ta yi nuni da cewa, barin ana shigo da Man cikin ƙasar nan, tamkar, daƙile ƙoƙarin sarrafa shi, a cikin ƙasar ne, wanda hakan kuma ke shafar kuɗaɗen ajiyar Gwamnatin ƙasar na ƙetare, tare da shafar kuɗaɗen musaya na Nijeriya.

Kazalika, sanarwar ta ce shigo da Man, zai kuma durƙurƙusar da ƙoƙarin manasana’atun sarrafa na cikin ƙasar nan.

“Babu ƙwaƙwarar hujja  kan batun iƙirarin na kamfanin na S&P, kan cewar Matatar ta Ɗangote, na sake shigo da Man cikin Nijeriya.” Inji sanarwar.

Idan za a iya tunawa, babban jami’i a ɓangaren kula da makamashi a  kamfanin na S&P Global, Matthew Tracey-Cook, ne, ya gabatar da wannan iƙirarin a jawabinsa a wajen  taron da ƙungiyar Injiniyoyi ta ƙasa wato MEMAN.

Matthew yayi zargin cewa, dilalan Mai a ƙasar nan, na ƙara yawan shigo da Man da aka tace daga ƙetare, zuwa cikin Nijeriya, wanda kuma ya fito ne, daga Matatar Ɗangote, musamman daga ƙasar Lomé, inda ake hada-hadar sa, a ƙasar  Togo.

Koda yake dai, Tracey-Cook, bai Ambato sunnan Matatar ta Ɗangote, wanda kuma Matatar ta Ɗangote, na da masaniyar hakan.

“Watanni da dama da suka wuce, musaman daga tsakanin Maris zuwa watan Yunin 2026, munga an shigo da Man da yawansa ya kai sama da kaso 70 zuwa 80, wanda kuma akasarinsa, ya fito ne, daga Matatar ta Ɗangote,” A cewarsa.

Jaridar PUNCH, ta ruwaito cewa, wasu daga cikin masu shigo da Man a watan Nuwambar 2025, sun zargi Matatar ta Ɗangote, kan sayar da Litocin Man da aka sake sarrawa, ga ƴan kasuwa a cikin ƙasar nan da Man, kan Naira 65 na kowacce Lita ɗaya.

Ƙungiyar ƴan Defon Man da kuma ƙungiyar masu sayar da Man ta ƙasa wato PPMAN da kuma sauran ƙananan masu sayar da man wato PROOAN suma a hirarar da ban da ban  Jaridar Punch ta yi da su, sun tabbatar da wannan zargin.

“Matatar ta Ɗangote na sayar da Man ga ƴan kasuwa na ƙasa da ƙasa, kan farashin Naira 65 na kowacce Lita, saɓanin yadda Matatar, ke sayarwa ƴan kasuwa a cikin Nijeriya,” A cewarsu.

Hakan ne ya sanya babu ɗaya daga cikin ƴaƴan ƙungiyar mu, da zai iya sayen Man, daga Matatar ta Ɗangote.

Sun yi zargin cewa, idan Matatar ta Ɗangote ta sayawar da ƴan kasuwar na ƙasa da ƙasa, su kuma suna kai Man zuwa ƙasar Lomé, inda suke yin iƙirarin cewa, sun sayo ne da yawa.

Duk da cewa, Matatar ta Ɗangote, ta yi watsi da wannan zargin kan sayarwa da ƴan kasuwar na ƙasa da ƙasa Man kan farashi mai sauƙi a ƙasar Togo idan aka kwatanta kan farashin da take sayarwa a Nijeriya, wanda hakan, ya sanya ƴan Nijeriya ke ci gaba da tambaya menene ya sanya Matatar cikin ƙasar da ke tace Man, take sayar da shi, a ƙasar Togo.

Har zuwa yanzu dai, Matatar ta Ɗangote, akwai ƙarar da ta shigar a gaban kotu, kan buƙatar, a dakatar da shigo da Man ɗuwa cikin ƙasar nan, daga waje.

Ɗangote
Abubakar Abba
+ postsBio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Nazari Kan Wasu Dalilan Da Ke Haddasa Sabanin Abotakar Jarumi Ko Jaruma A Kannywood

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Rukuni Na Biyu Na Tawagar Kwararrun Likitoci Ta Sin Ya Tafi DRC Don Taimaka Wa Kasar Shawo Kan Yaduwar Cutar Ebola

Rukuni Na Biyu Na Tawagar Kwararrun Likitoci Ta Sin Ya Tafi DRC Don Taimaka Wa Kasar Shawo Kan Yaduwar Cutar Ebola

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.