ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Abincin Da Ya Kamata Mai Azumi Ya Ci Da Wanda Bai Kamata Ba

by Bilkisu Tijjani
6 months ago
Azumi

Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da warhaka, barkammu da sake haɗuwa da ku a wannan makon a cikin wata mai alfarma na Ramadan a cikin shirin namu na Girki Adon Mata.

Watan Azumi lokaci ne da mutane suke ƙaurace wa abinci tun kafin ketowar Alfijir har zuwa faɗuwar Rana. Hakan yake sa mutane jin yunwa da ƙishin ruwa. Masu Azumi su kan ci abinci iri daban-daban a lokacin sahur da na buɗa baki.

  • Buƙatar Taka-tsan-tsan Wajen Koya Wa Yara Ƙanana Azumi
  • Ramadan: Lokutan Buda-Baki Da Sahur Na Azumi Na 8

Sai dai Likitoci sun bayyana nau’in abincin da ya kamata mai Azumi ya ci da wanda ya kamata ya ƙauracewa.

ADVERTISEMENT

Dr Lawan Musa Tahir, wani likita a asibitin Nizamiye da ke Abuja, babban birnin tarayya, ya shaida irin abincin da ya kamata masu Azumi su ci da kuma waɗanda ba su kamata mai Azumi ya ci ba.

Wane nau’in abinci ya kamata mai Azumi ya ci?

LABARAI MASU NASABA

Tuwon Alkama Da Miyar Taushe

Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna

Masu fama da wasu cututtuka: Masu Azumi sun kasu kashi-kashi: misali, akwai wanda da ma kafin Azumin, saboda da wata larura a asibiti za a ɗora shi kan abincin da ya kamata ya ci ko kada ya ci. Misali a nan shi kamar wanda yake da ciwon suga za a ɗora shi kan dokoki na yanayin abincin da zai ci, ko wanda yake da ciwon hanta, shi ma za a ɗora shi kan dokoki na abinci da zai ci.

Sai mai Olsa shima akwai abubuwan da ya kama ta ya ci da kuma wanda bai kama ta ba.

Haka kuma wanda yake da food allergy, wato wanda jikinsa ba ya karɓar wasu nau’o’in na abinci: to, wannan tun kafin Azumi akwai dokoki na yanayin abincin da yake ci, don haka idan Azumi ya zo zai ci gaba da bin dokokin.

 

Mutane masu lafiya:

Sai kuma mutanen da su da ma lafiyarsu ƙalau. Su ma ya danganta da inda suka samu kansu a lokacin Azumi.

Misali, idan mutum yana zaune a irin ƙasashenmu masu za fi inda mutane suke buƙatar yawan shan ruwa akai-kai, su ma akwai yadda ya kamata su yi.

 

Ga jerin abinci da abubuwan da suka kamata masu Azumi su ci:

A Guji cin abinci mai yaji da wanda yake da maiƙo sosai saboda zai ƙara musu ƙishirwa sannan akwai zafin gari. A ci abinci mai ruwa-ruwa, musamman ‘yaƴan itatuwa irin su Syaba, Abarba, Gwanda, Kankana da makamantansu.

A sha ruwan zafi kamar shayi ko koko ko kunu domin suna gyara ciki musamman bayan an daɗe ba a ci abinci ba.

A guji cika ciki fal da abinci za ka ga wasu suna cin abinci sosai idan an sha ruwa. Hakan yana da matsala. An fi so ka ci abinci kaɗan sannan ka huta yadda idan an jima za ka iya sake ci.

A guji shan taba da dangoginta saboda tana da illa. Babu laifi idan an motsa jiki lokaci Azumi amma a yi shi saisa-saisa.

Azumi
Bilkisu Tijjani
+ postsBio
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Tuwon Alkama Da Miyar Taushe
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Kula Da Labba Domin Su Kasance Masu Laushi
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Chicken Teriyaki Rice
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Kare Hannu Daga Bushewa

MASU ALAKA

Tuwon Alkama Da Miyar Taushe
Girke-Girke

Tuwon Alkama Da Miyar Taushe

September 5, 2026
Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna
Girke-Girke

Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna

August 29, 2026
Yadda Ake Chicken Teriyaki Rice
Girke-Girke

Yadda Ake Chicken Teriyaki Rice

August 29, 2026
Next Post
Za Mu Yi Duk Mai Yiwuwa Don Hana Iran Mallakar Makamin Nukiliya – Netanyahu

Za Mu Yi Duk Mai Yiwuwa Don Hana Iran Mallakar Makamin Nukiliya - Netanyahu

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.