ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Abubuwan Da Mai Jego Ke Buƙata Kafin Arba’in

by Bilkisu Tijjani
9 months ago
jego

Kulawar mace bayan haihuwa tana da matuƙar muhimmanci domin lafiyarta da ta jariri.

A wannan lokaci jikinta yana cikin tsari na murmurewa daga gajiya, zubar jini, sauyin hormones, da nauyin kulawa da jariri. Saboda haka, tana buƙatar kulawa ta musamman wacce ta haɗa da jiki, tunani, abinci, tsabta, da bacci don kaucewa matsalolin da ake gani a lokacin jego.

  1. Kulawar Lafiyar Jiki

A lokacin kafin kwanaki arba’in, mai jego na buƙatar kula da kanta ta hanyar wanka da ruwa mai ɗumi, tsaftar ko’ina da jikin gaba ɗaya, da canza kayanta akai-akai. Idan tana da ciwon yankan tiyata wato (CS) ko na episiotomy, ya zama dole ta kiyaye tsaftar wurin, ta guji ɗaga abu masu nauyi, ta yi amfani da magungunan da aka rubuta mata, sannan ta dinga dubawa ko akwai kumburi, zafi ko wari. Kulawar jiki mai kyau tana taimaka wa hanta, mahaifa da sauran sassan jiki su dawo yadda ya dace.

ADVERTISEMENT
  • Kyawawan Dabi’u Da Hasken Sanin Allah, Halittar Annabawa Ce Ba Koya Suke Ba
  • Kyawawan Halaye 2: Wasu Annabawa Da Sauran Bayin Allah Da Suka Yi Magana A Tsumman Jego
  1. Kyakkyawan abinci da shan ruwa

Jikinta yana buƙatar abinci mai gina jiki domin dawo da ƙarfin da ta rasa yayin haihuwa da kuma samar da isasshen mama. Abinci irin su kayan lambu, hatsi, nama, kifi, madara, da ’ya’yan itatuwa suna taimakawa sosai. Shan ruwa akai-akai yana hana ƙuraje, kuma yana hana kumburin ciki. Dole ta nisanci shan abubuwa masu haifar da zuwa bayangari, caffeine da shayi da yawa, da abinci mai yaji.

  1. Taimakon zuciya da kwantar da hankali

Sauyin yanayi bayan haihuwa na iya jawo damuwa, kuka ba tare da dalili ba, jin gajiya ko rashin ƙarfin gwiwa. Mai jego na buƙatar natsuwa, kwantar da hankali, kyakkyawar magana daga mijinta da iyayenta, da isasshen hutu. Taimakon tunani yana hana postpartum depression (cutar damuwar bayan haihuwa), wanda ke iya shafar kulawarta ga jariri.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

  1. Isasshen bacci da hutu

Jikinta zai riƙa buƙatar bacci fiye da yadda ta saba. Tun da jariri yana tashi da dare, mace me jego ta riƙa kwanciya duk lokacin da ta samu dama. Bacci yana taimaka wa jiki farfaɗo da ƙwayoyin da suka lalace, sannan yana rage gajiya da ciwon baya ko kai.

  1. Gujewa ayyuka masu nauyi

A lokacin kwanaki arba’in, bai kamata mai jego ta riƙa aiki mai nauyi ba, kamar ɗaga jarka, dafa abinci mai tsawon lokaci, wanke kaya masu yawa da hannu. Wannan na iya jawo matsalar kamo iska a mahaifa, kumburi, ko zubar jini mai tsanani.

  1. Kula da Jinin Jego

Dole ta riƙa lura da launi, wari da yawan jinin jego. Idan jinin ya yi yawa fiye da al’ada, ko ya fara wari mai muni, ko ya dawo da ja sosai, ya zama tilas ta garzaya asibiti. Wannan na iya nuna cutar ciwon sanyi ko tsayawar mahaifa ba sosai ba.

  1. Ziyarar Asibiti:

A cikin makonni biyu zuwa shida bayan haihuwa, ya kamata ta je asibiti domin tabbatar da cewa mahaifa, hanta, jini da dukkan sassan jikinta sun dawo daidai. Likitoci su kan duba BP, jini,da lafiyar jariri.

jego
Bilkisu Tijjani
+ postsBio
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Tuwon Alkama Da Miyar Taushe
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Kula Da Labba Domin Su Kasance Masu Laushi
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Chicken Teriyaki Rice
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Kare Hannu Daga Bushewa

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
ASUU

Yaushe Ne Ƙarshen Rikicin Yajin Aiki Tsakanin ASUU Da Gwamnatin Tarayya A Nijeriya? (3)

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.