ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, September 12, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

AFCON 2025: Ƙasashe 5 Da Za Su Iya Lashe Gasar Nahiyar Afirka

by Sadiq Usman
9 months ago

A ranar Lahadi aka fara gasar Kofin Nahiyar Afirka (AFCON) ta 2025 a Birnin Rabat, da ke Ƙasar Morocco, inda mai masaukin baƙi ta doke Comoros da ci 2–0, wanda hakan ya sa ta fara gasar da ƙafar dama. 

Brahim Díaz da Ayoub El Kaabi ne suka zura ƙwallayen biyu bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, lamarin da ya nuna irin ƙwarewa da ƙarfi da tawagar ke da shi, wanda ya sa ake kallon su a matsayin waɗanda za su iya lashe gasar.

  • Xi Ya Taya Jose Antonio Kast Murnar Lashe Zaben Shugaban Chile

Ƙasashe 24 ne suka samu gurbin zuwa gasar ta bana, inda ake sa ran za a buga wasanni masu zafi cike da armashi.

ADVERTISEMENT

Daga cikin ƙasashen da za su fafata akwai manyan ƙasashe irin su Morocco, Masar, Senegal, Aljeriya, Nijeriya, Côte d’Ivoire, Kamaru, Afirka ta Kudu, DR Congo, Mali, Tunisiya, da sauran ƙasashe kamar Comoros, Sudan, Angola, Zambia, Uganda, da Benin.

Manyan Ƙasashen Da Ake Hasashen Za Su Iya Lashe Gasar Ta Bana

1. Moroko — A matsayinta na mai masaukin baƙi na gasar, kuma ɗaya daga cikin ƙasashen Afirka mafi ƙarfi a duniya, Morocco ta fara gasar AFCON ta 2025 a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashen da ake shakka. Samun gogaggen mai horaswa, samun goyon bayan magoya baya a gida, da kuma haziƙan ’yan wasa, ya sa sun zama sahun gaba wajen neman lashe gasar. Tawagar tana fatan kawo ƙarshen dogon lokaci da ta shafe ba tare da lashe gasar ba.

LABARAI MASU NASABA

Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

2. Masar — Masar, wadda ta lashe AFCON sau bakwai a tarihin gasar, ta shiga gasar da tarihi da kuma dogaro da fitaccen ɗan wasan nan, Mohamed Salah, wanda ke da burin jagorantar Pharaohs zuwa nasara.

Tarihi da ƙwarewarsu a wannan gasa ya sa suka zama barazana ga kowace ƙasa.

3. Senegal — Zakunan Teranga, zakarun AFCON na 2021, har yanzu suna daga cikin manyan ƙasashen Afirka. Suna da tawagar ƙwararrun ‘yan wasa, suna buga ƙwallo cikim sauri da tsari mai kyau, wanda hakan ya sa abokan hamayya ke shakkarsu.

4.  Aljeriya — Ana musu kirari da masu abun ban mamaki. Ko da yake Aljeriya ta fuskanci ƙalubale a ’yan shekarun baya, amma duk da haka har yanzu tana da ’yan wasa masu fasaha da gogewa.

5. Nijerya  — A gefe guda kuma, Nijeriya na da Super Eagles, wadda ke da ‘yan wasa masu cike da basira da ƙarfi a gaba. Nijeriya ta zama barazana a Afrika a baya-bayan nan duna da irin jajirtattun ‘yan wasan da ta haɗa da kuma gogaggen mai horaswa.

Sauran Ƙasashen da Za Su Iya Ba Da Mamaki

Ƙasashe irin su Côte d’Ivoire (zakarun gasar bara), Kamaru, Tunisiya, Afirka ta Kudu, Mali, da DR Congo su ma na da ƙwarewa da haziƙan ’yan wasa da za su iya taka wa manyan ƙasashe burki idan suka yi amfani da damar da suka samu.

Gasar AFCON ta 2025 na shirin zama ɗaya daga cikin gasar da za ta fi ɗaukar hankali duba da irin tanadi da shirin da masu masaukin baƙi suka yi.

Gasar ta haɗa manyan ƙasashen da suka shahara a tarihin ƙwallon ƙafar Afirka da kuma ƙasashe masu tasowa da ke shirin nuna bajintarsu. Duk da cewa Morocco na da fifiko saboda kasancewarsu masu masauki baƙi da kyakkyawan tsari, ƙasashe irin su Masar, Senegal, Nijeriya, da Côte d’Ivoire sun yi shiri na musamman domin fafatawa wajen lashe kofin na bana.

Masoya ƙwallon ƙafa a faɗin Afirka na sa ran ganin gasa mai cike da tsari, tarihi da abubuwan tunawa.

MASU ALAKA

Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura
Rahotonni

Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

September 12, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu
Rahotonni

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Umarnin Kawo Karshen Matsalar Tsaro
Rahotonni

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

September 5, 2026
Next Post
Sin Ta Nuna Adawa Da Kalaman Jami’in Japan Game Da Mallakar Makaman Nukiliya

Sin Ta Nuna Adawa Da Kalaman Jami'in Japan Game Da Mallakar Makaman Nukiliya

LABARAI MASU NASABA

Yaƙin Amurka Da Iran Ya Janyo Asarar Fitar Da Ganga Biliyan 2.8 Na Mai

Yaƙin Amurka Da Iran Ya Janyo Asarar Fitar Da Ganga Biliyan 2.8 Na Mai

September 12, 2026
Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku

Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku

September 12, 2026
An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro

An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro

September 12, 2026
Shekaru 22 Bayan Rushewar Nigeria Airways, Gwamnati Ta Biya Ma’aikata 2,700 Biliyan 18

Shekaru 22 Bayan Rushewar Nigeria Airways, Gwamnati Ta Biya Ma’aikata 2,700 Biliyan 18

September 12, 2026
Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

September 12, 2026
Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

Sanata Yari Ya Gudanar Da Taron Masu Ruwa Da Tsaki A Zamfara

September 12, 2026
Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Motocin Aiki Ga Manyan Makarantu A Zamfara

Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Motocin Aiki Ga Manyan Makarantu A Zamfara

September 12, 2026
Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

September 12, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Jam’iyyar APC Ce Za Ta Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa Da Gwamnoni A Nijeriya -Dikko Raɗɗa

September 12, 2026
NNPCL Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa ₦860 Kan Kowacce Lita – IPMAN

Mene Ne Ra’ayinku Kan Dawo Da Tallafin Man Fetur Ko Barin Sa?

September 12, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.