ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Afirka Ta Nuna Aniyarta Ta Kawar Da Shingen Da Ya Hana Ta Samun Ci Gaba

by CGTN Hausa and Sulaiman
4 months ago
Afirka

Shin ko mene ne abun da ya hana nahiyar Afirka samun ci gaban tattalin arziki mai dorewa? Amsa a nan ita ce tsarin hada-hadar kudi na duniya da ya kasance karkashin jagorancin kasashen yamma, kamar yadda dimbin shugabannin kasashen Afirka suka bayyana, wajen wani taron kolin da ya gudana a kasar Kenya a kwanan baya.

A wajen taro mai taken “ciyar da Afirka gaba”, da shugabanni da manyan jami’ai na kasashe fiye da 30 dake nahiyar Afirka suka halarta, shugaban kasar Kenya William Ruto, ya fara da gabatar da ra’ayinsa cewa, tsarin hada-hadar kudi da ake amfani da shi a duniya yana hana jari shiga cikin nahiyar Afirka.

Sa’an nan, a nasa jawabi, shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu shi ma ya ce, tsarin hada-hadar kudi na duniya yana taimakawa durkushewar masana’antu a nahiyar Afirka.

ADVERTISEMENT

Shugaban ya yi tambaya cewa, “Yayin da kasashen Afirka ke neman cin bashi, a kan bukace su da su biya kudin da ya ninka na yankunan Turai, da Asiya, da arewacin Amurka, har da ninki 5 zuwa 10, to, ta yaya masana’antun kasashen Afirka za su iya takara da takwarorinsu na wadannan yankuna a karkashin wannan yanayi?”Batun da shugabannin suka ambata na nufin wahalar samun bashi da kasashen Afirka ke fuskanta, sakamakon yadda hukumomin tantance matsayin lamuni na kasasashen yamma, suka bayyana nahiyar Afirka a matsayin “Mai hadarin gamuwa da matsala wajen biyan bashi”.

Hakika kasar Amurka da sauran kasashen dake yammacin duniya sun tsara tsarin nan na tantance matsayin lamuni ne don tabbatar da moriyar kansu, inda suka ba kansu makin lamuni da ya fi na kasashe masu tasowa, ta yadda jari da riba za su rika kwarara zuwa cikin kasuwannin cikin gidansu, tare da lahanta moriyar kasashe masu tasowa, ta hanyar jefa su cikin “tarkon bashi”.

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

A cewar shugaba Tinubu na Najeriya, a shekarar 2026 da muke ciki, kasarsa za ta kashe dalar Amurka kimanin biliyan 11.6 wajen biyan bashin da ake binta, adadin da zai kai rabin yawan kudin da kasar za ta iya samu a duk shekara.

Ra’ayi daya da shugabannin kasashen Afirka suka cimma a wannan karo, dangane da tsarin hada-hadar kudi na duniya, shi ma ya nuna cewa, maganar “tarkon cin bashin kasar Sin”, da kafofin yada labarai na kasashen yamma ke kokarin yayatawa a duniya karya ce. Saboda a zahiri, dalilin da ya sa ake samun “tarkon bashi” shi ne tsarin hada-hadar kudi na duniya, wanda ya shafi ikon hukumomin kasashen yamma na tantance matsayin lamuni, maimakon wata kasa da ke son samar da rance ga kasashen Afirka.

Alal hakika, shi ma hamshakin dan kasuwar Najeriya Aliko Dangote, ya yabawa kasar Sin bisa saukin kai a fannin samar da rance, lokacin da ya yi hira da manema labaru a kwanan baya.

Ya ce, kamfanonin kasar Sin masu samar da injuna sun yarda da kamfanonin Afirka su samu injunan da suke bukata, bisa biyan wani bangare na kudin injuna, daga baya su biya bashi cikin lokaci daban daban, maimakon tsarin kamfanonin kasashen yamma na biyan dukkan kudi nan take ba tare da wani jinkiri ba.

A cewar Dangote, hakan ya sa kasar Sin samar da mafi yawan gudunmowa ga ci gaban masana’antu da kasuwanci na kasashen Afirka.Ta haka muna iya gane cewa, cin bashi mataki ne da ya wajaba ga yunkurin ciyar da masana’antu da kasuwanci gaba.

Sai dai ko za a fada cikin “tarkon bashi” ya danganta da niyyar samar da bashi: Ana samar da bashi ne don kwace dukiya da samun riba fiye da kima.

Ko kuma ana samar da kudin bashi a matsayin wani taimako, sakamakon yadda ake neman kulla huldar hadin gwiwa ta dogon lokaci, da tabbatar da cin moriyar juna da damar samun ci gaba tare.

A zahiri, tsarin hada-hadar kudi na duniya karkashin jagorancin kasashen yamma ya nuna wani yanayi na neman kwace kudi daga kasashe masu tasowa, kuma wannan ya sa kasashen Afirka fara mayar da martani.

A wajen taron koli na wannan karo, kasashen Afirka sun sanar da cewa, za a rage dogaro kan kudaden dalar Amurka, da Euro, gami da tsarin hada-hadar kudi na kasashen yamma, tun kafin shekarar 2029.

Inda matakan da suka tanada sun hada da kafa wani kawance na tantance matsayin lamuni na nahiyar Afirka kafin shekarar 2027, da neman cimma burin yin amfani da kudin na kashin kai wajen gudanar da kaso 50% na cinikin da ake yi tsakanin kasashen Afirka, da kaso 30% na cinikin da kasashen Afirka suke yi da kasashe na sabbin kasuwanni, ciki har da kasar ta Sin a shekarar 2029.

Ta hanyar kara dogaro da kai a fannin hada-hadar kudi, kasashe Afirka sun bayyana niyyarsu ta kawar da shingen da ya hana su samun ci gaba daga tushe.

Batun nan ya yi daidai da maganar da shugaba Tinubu ya fada wajen taron wannan karo, inda ya ce, “Dole ne a daidaita tsarin hada-hadar kudi na duniya, in ba haka ba za a kauce masa.” (Bello Wang)

Afirka
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa
Afirka
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara
  • Sulaiman
    Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan
  • Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
Kotu Ta Tsayar Da Ranar 26 Ga Mayu Don Yanke Hukunci Kan Cancantar Takarar Jonathan

Kotu Ta Tsayar Da Ranar 26 Ga Mayu Don Yanke Hukunci Kan Cancantar Takarar Jonathan

LABARAI MASU NASABA

Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.