Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya ta yi gargaɗin cewa aƙalla jihohi 26 da Babban Birnin Tarayya (FCT) na iya fuskantar ambaliya tsakanin 22 ga Yuni zuwa 5 ga Yuli, 2026, sakamakon hasashen ruwan sama mai ƙarfi da ake sa ran zai sauka a sassa daban-daban na ƙasar.
A cikin hasashen ambaliyar da ta fitar a ranar Litinin ta wannan mako ta hannun Cibiyar Gargaɗin Ambaliya ta Ƙasa ƙarƙashin Sashen Kula da Zaizayar Ƙasa, Ambaliya da Yankunan Gaɓar Ruwa, Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya ta bayyana ɗaruruwan al’ummomi a faɗin ƙasar a matsayin yankunan da ke cikin matsanancin haɗarin ambaliya ko kuma babban haɗarin ambaliya.
A cewar hasashen, “Ana sa ran wurare da muhallansu ke ƙasa za su fuskanci ruwan sama mai yawa wanda zai iya haifar da ambaliya a tsakanin 22 ga Yuni zuwa 5 ga Yuli, 2026.”
Jihohin da aka sanya cikin rukunin matsanancin haɗarin ambaliya sun haɗa da: Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bayelsa, Benue, Cross Riɓer, Delta, Ebonyi, Edo, Ekiti, Enugu, Imo, Kogi, Kwara, Legas, Neja, Ogun, Ondo, Osun, Oyo da Riɓers.
Daga cikin al’ummomin da aka bayyana a matsayin masu matuƙar fuskantar haɗarin ambaliya akwai: Aba, Arochukwu da Umuahia a Jihar Abia; Jimeta da Numan a Adamawa; Eket, Oron da Uyo a Akwa Ibom; Onitsha Inland Town da Awka Urban Drainage Corridors a Anambra; sai kuma Yenagoa, Brass da Nembe Town a Bayelsa.
Sauran wuraren da aka lissafa sun haɗa da: Benin City Urban Core da Auchi a Edo; Ado-Ekiti da Ikere-Ekiti a Ekiti; Enugu, Nsukka da Oji Riɓer Town a Enugu; Owerri, Orlu da Okigwe a Imo; Lokoja da Ajaokuta a Kogi; Ilorin, Jebba da Pategi a Kwara; da kuma al’ummomi da dama a Jihar Legas ciki har da Agege, Alimosho, Apapa, Badagry, Ikeja, Ikorodu, Lagos Island, Lekki da Surulere.
A Jihar Neja, Ma’aikatar ta bayyana Bida, Minna, Mokwa, Suleja da Kontagora a matsayin yankunan da ke cikin haɗarin ambaliya, yayin da Abeokuta, Ota da Sagamu aka lissafa a Jihar Ogun.
Gargaɗin ya kuma shafi Akure, Owo da Okitipupa a Jihar Ondo; Oshogbo, Ile-Ife da Ilesa a Osun; Ibadan, Ogbomoso da Oyo a Jihar Oyo; sannan Port Harcourt Urban Core, Bonny, Ahoada da Omoku a Jihar Riɓers.
Bugu da ƙari, Ma’aikatar ta ayyana wasu sassan Adamawa, Babban Birnin Tarayya (FCT), Kebbi, Kogi, Nasarawa, Filato da Taraba a matsayin yankunan da ke cikin babban haɗarin ambaliya.
Ƙararrawar Gargaɗi
Da yake zantawa da wakilinmu, wani malami a Sashen Tsare-tsaren Birane da Yankuna na Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da ke Nasarawa, Jihar Nasarawa, Dakta John Buba, ya buƙaci jihohin da aka ambata su ɗauki hasashen ambaliyar da muhimmanci a matsayin gaggawar kula da ƙasa.
Ya ce: “A ganina, hasashen ambaliyar shekarar 2026 ya kamata a ɗauke shi a matsayin ƙararrawar gargaɗi da ke kira ga matakin ƙasa, domin lokaci ya yi da za mu daina ɗaukar ambaliya a matsayin baƙon da ke zuwa a ba-zata. Alamu sun nuna cewa ruwan sama zai sauka kamar yadda aka saba, kuma sauyin yanayi ya sa yana ƙara tsananta. Amma abin da ba ya zama al’ada shi ne abin da ke biyo baya. Hasashen ambaliyar da ake fitarwa kowace shekara ya fi kama da ƙararrawar haɗari da ta daɗe tana ƙara, sai dai mun saba da yin watsi da ita.”
Ya ƙara da cewa: “A taƙaice, wannan ba matsalar wasu yankuna kaɗai ba ce; matsala ce ta ƙasa baki ɗaya. Amma duk shekara idan ambaliya ta zo, sai mu riƙa magana kamar mun faɗa cikin wata masifa da ba a zata ba; kamar dai ruwan ya shigo ba tare da wani gargaɗi ba, tamkar ɓarayin da ke zuwa cikin dare.”
Ya ci gaba da cewa: “Ruwan sama na farko kan fara ne a kusan watan Afrilu. Zuwa watan Yuli, ƙasa ta riga ta jike ƙwarai. Koguna sukan cika su yi ambaliya, hanyoyin magudanar ruwa sukan gaza aiki, kuma zuwa watan Satumba, al’ummomi gaba ɗaya sukan nutse cikin ruwa. Gidaje sukan lalace, gonaki sukan shafe, makarantu sukan rufe, asibitoci kuma sukan shiga mawuyacin hali.”
“Daga nan sai a fara abin da ya zama al’ada; fitar da sanarwar ta’aziyya, raba kayan agaji, da kuma zagayawa ta sama domin duba irin ɓarnar da aka yi. Amma gaskiyar da ba ta da daɗin ji ita ce, ambaliya a Nijeriya ba bala’in yanayi kaɗai ba ce. Matsala ce ta gazawar shugabanci da gudanarwa.”
Ya ƙara da cewa: “Hasashen shekarar 2026 ya nuna abubuwan da aka saba gani, kamar ruwan sama mai yawa, hauhawar matakan ruwa a koguna, da yiwuwar sakin ruwa daga madatsun ruwa. Amma bayan abubuwan da yanayi ke haifarwa, ya kuma nuna wasu matsalolin da mutane ke jawowa, waɗanda suka fi tayar da hankali: rashin ingantaccen tsarin tsara birane, toshewar magudanan ruwa, da ci gaba da gina gidaje a wuraren da ruwa ke bi. Wato, ba ruwan sama kaɗai ne ke jawo wannan bala’i ba; mu ma muna da hannu a ciki.”
“Birane, waɗanda ya kamata su zama abin koyi wajen tsari da ingantaccen shiri, sun zama wuraren da ambaliya ke addaba kowace shekara. Hanyoyi sukan koma koguna ba don ruwan sama sabon abu ne ba, sai don babu magudanan ruwa masu kyau, ko kuma an yi watsi da su, ko kuma sun toshe da shara. Ana yin gine-gine a wuraren da ruwa ke bi cikin ƴanci. Kuma idan abin da ba makawa ya faru, sai mu ce ‘aikin Allah ne.’”
Sun Shagaltu Da Harkokin Siyasa
Hakazalika, wani mai rajin kare muhalli, Dakta Harry Tonye, ya shaida wa Blueprint Weekend cewa wasu gwamnoni sun fi maida hankali kan siyasar zaɓen 2027 fiye da ɗaukar matakan da za su rage illar ambaliyar da ake hasashen za ta afku.
Ya ce: “Ina matuƙar damuwa da yadda gwamnatocin jihohi ke shirye-shiryen mayar da martani ga irin waɗannan gargaɗi domin rage illolin bala’o’in da ke tafe. Kuma ba wata Jiha ɗaya nake nufi ba. Ina magana ne kan ɗabi’arsu ta ɗaukar mataki ne bayan abin ya faru, maimakon ɗaukar matakin kariya tun kafin hakan.”
Ya ƙara da cewa: “A mafi yawan jihohi, kamar yadda muka gani tsawon shekaru, shirye-shiryensu da yadda suke amsa irin waɗannan gargaɗi suna zuwa ne bayan matsala ta afku, maimakon tun kafin hakan. Suna jira ne sai abin ya faru kafin su ɗauki mataki, duk da cewa ana samun gargaɗi tun da wuri kuma a sarari. Saboda haka ba a samun ingantattun matakan rage haɗari, kuma idan bala’i ya faru, illolinsa sukan kasance masu tsanani ta fannoni da dama. Da alama ba ma koyon darasi daga abubuwan da suka faru a baya.”
Tonye ya ci gaba da cewa: “A ƙasar da ke fama da ambaliya a kowace shekara, wadda ta yi sanadin mutuwar ɗaruruwan mutane tare da lalata dukiyoyi da gonaki na biliyoyin Naira tsawon shekaru, wannan gaggawar mayar da hankali kan siyasar 2027 abu ne mai tayar da hankali kuma abin takaici.”
Ya ƙara da cewa: “Duk da cewa sauran kusan watanni shida kafin babban zaɓe, tuni ana fara jin ƙarar gangar siyasar 2027 a faɗin Nijeriya. Allunan yaƙin neman zaɓe sun fara sake bayyana. Ana fara kunna injin yaƙin neman zaɓe a hankali. Kamar dai an dakatar da harkokin mulki cikin ladabi domin a ba siyasa wuri.”
“Wannan ne lokacin da ya kamata gwamnati ta fi mayar da hankali kan gudanar da mulki cikin ƙwazo, ƙirƙire-ƙirƙire da tausayi. Amma a maimakon haka, yawancin gwamnoni suna sake tsara ƙawancen siyasa, suna auna ƙarfin ƙuri’un yankuna, kuma suna gwada dabarun yaƙin neman zaɓe. Gwamnoni sun shagaltu da batun wanda zai gaje su, yayin da ƴan majalisu kuma ke nazarin dabarun sake samun tikitin komawa majalisa.”
Me Suke Yi?
Sai dai, a wani ɓangare na ƙoƙarin da ake yi na hana aukuwar ambaliya a Jihar, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kogi (SEMA) ta bayyana cewa ta ƙaddamar da gangamin wayar da kan jama’a kan haɗarin ambaliya da sauran bala’o’i masu alaƙa da ita. Hukumar ta yi gargaɗin cewa har yanzu wasu sassan Jihar na cikin haɗarin fuskantar ambaliya a wannan daminar.
Da yake ba da tasa gudummawar, wani babban jami’in hukumar wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda ba a ba shi izinin yin magana kan lamarin ba, ya ce gwamnatin Jihar ta ɗauki matakan kariya tun da wuri domin kare rayuka, dukiyoyi da muhimman ababen more rayuwa daga bala’in ambaliya.
Ya bayyana cewa Jihar ta Kogi ta sha fama da ambaliya iri-iri a cikin ƴan shekarun nan, lamarin da ya lalata gidaje, gonaki, hanyoyi da sauran muhimman kadarorin tattalin arziki.
Ya ce, “Jihar Kogi ta fuskanci ambaliya iri-iri a cikin ƴan shekarun nan, wanda ya yi sanadin lalacewar gidaje, gonaki, hanyoyi da sauran kadarorin tattalin arziki, tare da shafar hanyoyin samun abin dogaro na al’ummomin da suka fi rauni.”
A cewarsa, ingantaccen tsarin kare bala’i yana dogara ne da tabbatar da cewa saƙonnin gargaɗin farko sun isa ga al’ummomi cikin lokaci kuma a cikin yaren da suke fahimta.
Ya ce, “Dole ne mu tabbatar da cewa saƙonnin gargaɗin farko sun isa ga al’ummomi cikin lokaci kuma cikin sauƙin fahimta. Hukumomin ƙananan hukumomi, sarakunan gargajiya, shugabannin addinai, ƙungiyoyin al’umma da kafofin yaɗa labarai duk suna da muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa wayar da kan jama’a kan hanyoyin kariya da shirye-shiryen tunkarar ambaliya.”
Hakazalika, gwamnatocin jihohin Ekiti, Osun da Enugu sun ƙara zage damtse wajen aiwatar da matakan kariya daga ambaliya yayin da daminar shekarar 2026 ke kaiwa ƙololuwa.
Jami’an waɗannan jihohi, a tattaunawa daban-daban da manema labarai, sun bayyana cewa matakan sun haɗa da tonawa da zurfafa hanyoyin ruwa, gina magudanan ruwa, cire laka daga magudanan ruwa, tabbatar da bin dokoki da kuma wayar da kan al’umma.
A Jihar Ekiti, shugaban Hukumar Kare Muhalli ta Jihar Ekiti (EKSEPA), Cif Bamidele Oguntoyinbo, ya ce ana ci gaba da ayyukan tono da cire laka daga hanyoyin ruwa a Ado-Ekiti, babban birnin Jihar.
A cewarsa, gwamnatin Jihar ta kuma fara aikin tone koguna da rafuka a wasu yankunan da ke yawan fuskantar ambaliya, ciki har da Iso, Oshodi, Elemi, Iremide, Ureje, Olujoda, Falana, Moferere, da kuma GRA Third Eɗtension da ke kan sabuwar hanyar Iyin Ekiti a Ado-Ekiti.
Ya kuma bayyana cewa gwamnatin Jihar ta kashe kimanin Naira miliyan 475.2 cikin watanni 18 da suka gabata wajen ayyukan tono hanyoyin ruwa da cire laka daga magudanan ruwa.
Shugaban EKSEPA ya ce Mataimakiyar Gwamnan Jihar Ekiti, Misis Monisade Afuye, a wani ɓangare na ƙoƙarin rage haɗarin ambaliya, ta kwanan nan ta umarci shugabannin ƙananan hukumomi da Ma’aikatar Tsare-tsaren Birane da Kula da Tsarin Gine-gine da su rushe gine-ginen da aka yi ba bisa ƙa’ida ba waɗanda ke toshe hanyoyin ruwa.
Ya ce, “An ɗauki wannan matakin ne domin kare rayuka da dukiyoyi, bayan hasashen Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya (NiMet) cewa Jihar Ekiti na cikin wuraren da za su fi fuskantar ambaliya a daminar shekarar 2026.”
Ya kuma bayyana cewa gwamnatin Jihar ta sayo wasu manyan injinan rage haɗarin ambaliya, ciki har da na’urorin tono hanyoyin ruwa masu iya aiki a ruwa da kuma manyan motocin ɗaukar injuna, ƙarƙashin Shirin Kula da Zaizayar Ƙasa da Yankunan Tafkunan Ruwa na Nijeriya (NEWMAP) da Bankin Duniya ke tallafawa, domin tabbatar da ci gaba da aikin tono hanyoyin ruwa.
Ya ƙara da cewa hukumar, ta hanyar shirye-shiryen wayar da kan jama’a, ta buƙaci shugabannin ƙananan hukumomi su yi aiki tare da sarakunan gargajiya a yankunansu domin ƙara wayar da kan al’umma game da haɗarin ambaliya.
Hakazalika, Kwamishinan Muhalli da Tsabtace Muhalli na Jihar Osun, Mista Mayowa Adejoorin, ya ce gwamnatin Jihar ta fara ci gaba da tono hanyoyin ruwa da magudanan ruwa a matsayin wani ɓangare na matakan da take ɗauka domin daƙile ambaliya.
Ya ce, “Gwamna Ademola Adeleke ya amince da gudanar da aikin tono hanyoyin ruwa da magudanan ruwa a faɗin Jihar a farkon kowace shekara a matsayin matakin kariya tun kafin ambaliya ta faru.”
Ya ci gaba da cewa, “Saboda waɗannan matakan kariya da aka ɗauka tun da wuri, Jihar Osun ba ta fuskanci wata babbar ko ƙaramar ambaliya ba a cikin ƴan shekarun nan, ko da a lokutan da ake samun ruwan sama mai yawa.”
Ya ƙara da cewa, “An samar da tsare-tsare da ke hana mazauna zubar da shara a cikin hanyoyin ruwa, yayin da aka ƙara wayar da kan jama’a ta kafafen yaɗa labarai kan haɗarin toshe magudanan ruwa. Haka kuma, mun rushe wasu gine-ginen da aka gina a kan hanyoyin ruwa.”
A nata jawabin, Mai Ba Gwamna Shawara ta Musamman kan Harkokin Agajin Gaggawa, Misis Emiola Fakeye, ta ce an gano wuraren da suka fi fuskantar haɗarin ambaliya a faɗin Jihar, tare da ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da saurin kai ɗauki idan wani bala’i ya faru.
A cewarta, an kuma raba kayan agaji ga al’ummomin da ambaliya ta shafa domin rage wa mazauna yankunan illolin da suka fuskanta.
Ta ce, “Mun tallafa wa waɗanda ambaliya ta shafa a wasu al’ummomin da aka gano da kayan agaji tare da haɗin gwiwar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA).”
Ta ƙara da cewa, “An gano garuruwa irin su Ila-Orangun, Aiyegbaju, Iragbiji da maƙwabtansu a matsayin wuraren da ke yawan fuskantar ambaliya, kuma an ɗauki cikakkun matakai domin rage haɗarin ambaliya tare da tabbatar da saurin mayar da martani idan wani bala’i ya faru.”
Sai dai Fakeye ta jaddada cewa gwamnatin Jihar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma ta hanyar hana aukuwar ambaliyar da ka iya jefa rayuka da dukiyoyi cikin haɗari.
Hakazalika, sakamakon hasashen ambaliyar da aka fitar, har ma kafin a fitar da shi, Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, ya amince wa Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Enugu (Enugu SEMA) ta shirya horarwa ga mambobin Kwamitocin Agajin Gaggawa na Ƙananan Hukumomi a dukkan ƙananan hukumomi 17 na Jihar da sauran masu ruwa da tsaki, ƙarƙashin taken “Ginawa da Ƙarfafa Juriyar Agajin Gaggawa a Jihar Enugu.”
A cewar shugabar Enugu SEMA, Misis Chinasa Mbah, an gudanar da wannan shirin a zangon farko na wannan shekara.
Ta ce, “Mun kuma yi haɗin gwiwa da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) da Ƙungiyar Red Cross da sauransu wajen gudanar da shirye-shiryen wayar da kan al’ummomi.”
Ta bayyana cewa, “Hakan ya zama dole ne saboda al’ummomi su ne kan fara kai ɗauki a duk lokacin da wani bala’i ya faru, ciki har da ambaliya.”
Ta ƙara da cewa, “Saboda haka, wannan horo na ƙarfafa ƙwarewa yana taimaka musu su kasance cikin shiri domin ceto rayuka, dukiyoyi da tattalin arziki yayin ambaliya da sauran bala’o’i a Jihar. Wannan kuwa saboda kula da bala’o’i alhakin kowa ne.”
Ta kuma ce, “Baya ga haka, muna yaɗa saƙonnin gargaɗi ta gidajen rediyo tare da shirye-shiryen wayar da kan jama’a, musamman a al’ummomin da ake sa ran za su iya fuskantar ambaliya. Muna yin hakan ne ta hanyar haɗin gwiwa da shugabannin ƙananan hukumomi da sarakunan gargajiya.”
Abin da ya wajaba ne a yi
Da yake magana kan abin da ya kamata a yi domin kauce wa ambaliya, Dakta John Buba ya ce dole ne a sauya salon da aka saba bi wajen yaƙi da ambaliya.
Ya ce: “Da farko, dole ne mu daina tsaya wa kan hasashen ambaliya kawai, mu koma kan hana ta faruwa ko rage illolinta. Tsarin gargaɗin farko yana da amfani ne kawai idan ana ɗaukar matakan da ya kamata bayan an bayar da gargaɗin. Hukumomin da abin ya shafa sun yi nasu ƙoƙari, har ma sun ƙara inganta hasashen shekarar 2026.”
Ya ci gaba da cewa: “Sabbin abubuwan da ke cikin hasashen shekarar 2026 sun haɗa da hasashen ambaliya a matakin al’umma (wato hasashen da ya fi mayar da hankali kan takamaiman yankuna), ingantattun tsarin gargaɗin farko da kuma ingantaccen amfani da bayanai wajen hasashen ambaliya. Saboda haka, gwamnati ta tabbatar da aiwatar da shirye-shiryen kwashe mutane daga wurare masu haɗari, inganta magudanan ruwa, da kuma tsaurara bin dokokin amfani da filaye.”
Ya ƙara da cewa: “Na biyu, dole ne tsara birane ya daina kasancewa a takarda kawai. Dole ne birane su mutunta yanayin ƙasarsu. Ruwa yana da hanyar da ya saba bi, kuma koyaushe zai nemi komawa hanyoyinsa na asali. Yin gine-gine a wuraren da ruwa ke bi ba ci gaba ba ne, illa dai jinkirta wani bala’i ne da zai zo gaba. Na uku, dole ne a tabbatar da ɗaukar alhaki. Idan magudanan ruwa sun gaza aiki, idan gine-ginen da ba bisa ƙa’ida ba sun toshe hanyoyin ruwa, ko kuma tsarin tattara shara ya rushe, waɗannan ba matsaloli ne da suka faru kai tsaye ba. Sakamakon wasu shawarwari ne da aka yanke ko kuma gazawar yanke matakan da suka dace. Dole ne a gano masu alhakin, kuma su fuskanci sakamakon abin da suka aikata.”
Ya kuma ce: “A ƙarshe, dole ne ƴan ƙasa su kasance wani ɓangare na mafita. Ambaliya na ƙara tsananta sakamakon wasu ayyukan yau da kullum kamar zubar da shara ba tare da tsari ba, yin watsi da dokokin kare muhalli, da kuma al’adar cewa ‘ba ruwana’. Gaskiyar ita ce, ya shafi kowa. Hasashen Ambaliya na Shekara (AFO) ba takarda kawai ba ce; madubi ne. Yana nuna ƙasa mai ilimin yadda za ta hana bala’i, amma sau da yawa tana rasa ƙwarin gwiwar aiwatar da abin da ta sani. Haka kuma, ya nuna mana wata sabuwar fahimta game da muhimmancin ruwa.”
Ya ƙara da cewa: “Ruwa ba kawai wata muhimmiyar albarkatun ƙasa ba ne kuma. Yanzu ya zama wata muhimmiyar kadara ta tattalin arziki wadda ke taka rawa wajen bunƙasa ci gaban ƙasa, haɓaka samar da kayayyakin masana’antu da tabbatar da daidaiton muhalli. Sauya fahimta daga kallon ruwa a matsayin wata haja kawai zuwa kallonsa a matsayin ginshiƙin bunƙasar tattalin arziki yana da matuƙar muhimmanci domin tabbatar da ɗorewar tattalin arziki da kuma daidaitawa da sauyin yanayi. Wannan sauyi yana buƙatar ingantaccen tsarin kula da albarkatun ruwa, ba kawai domin tallafa wa sassa daban-daban ba, har ma domin kare al’umma ta hanyar yin ingantaccen hasashen ambaliya da fari.”














