ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Albishir Ga Iyayen Da Suka Karantar Da ‘Ya’yansu Alkur’ani (2)

by Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
2 months ago
Iyayen

Ya zo acikin Hadisi, manzon Allah SAW yace, “duk wanda ya karantar da dansa, ko ya dauko wanda ya karantar masa da shi, Allah da kansa, zai gaisa da wannan mutumin a ranar tashin alkiyama, sannan Allah zai rubuta acikin littafin mahaifin yaron ladan kamar ya yi Hajji 10,000, kamar ya yi Umra 10,000, kamar ya ‘yanta bayi 10,000, kuma bayin darajarsu ta kai kamar, Larabawa ‘ya’yan Annabi Isma’ilu, kamar ya Musuluntar da mutane 10,000, kamar ya ciyar da mayunwaci 10,000 wanda ciyar da mayunwaci daya kuwa, Imam Shafi’i yana cewa, “loma daya da za ka saka a bakin mayunwaci, tafi ka gina masallaci 1,000″, kamar ya tufatar da wadanda basu da kaya su 10,000 kuma Alkur’anin zai zama tare da shi acikin kabarinsa cikin sura mai kyau don dauke masa kewa har zuwa ranar tashin Alkiyama”. Wannan lada, duk na wanda ya tsaya wa dansa ne ya san Alkur’ani.

Allah tabaraka wata’ala, zai sanya cika a ma’aunin mahaifin da ya tsaya wa dawainiyar yaronsa har ya haddace Alkur’ani, zai tsallake siradi kamar walkiya, sannan Alkur’anin zai rike hannunsa har shiga Aljanna, hakan duk yana kunshe ne acikin Tafsirin Suratul Fatiha na Littafin Fakrurrazi.

Wannan duk ladan mahaifin da ya tsayawa dawainiyar yaronsa ne har ya haddace Alkur’ani, to ina ladan malamin yaron, bare kuma na mahaddacin?

ADVERTISEMENT

Maganar Alkur’ani tana da yawa, saboda in an ce Alkur’ani, amfadi ubangiji, kuma amfadi Annabi Muhammad SAW wanda ya kawo shi. Don haka, kowane littafi, za a fade shi ne da wanda ya kawo shi7, Alkur’ani na Allah ne kuma Annabi SAW ya kawo shi.

Dawwamar Alkur’ani, ita ce dawwamar mu da sanin Allah da sanin Annabi SAW.

LABARAI MASU NASABA

Falalar Haɗa Basmala da Suratul Fatiha

Falalar Neman Tsari Daga Sharrin Shaidan

Lallai duk Musulmai sun yi imani cewa, Alkur’ani shi ne na daya, amma a wurin hukunci, Malamai sun mayar da shi wurin na goma sabida lalacewa, har wadansu daga cikin Malaman suna cewa, “Wai Hadisi zai shafe hukuncin Alkur’ani”, amma ikon Allah, ba su iya cewa, Ijma’i zai iya soke Hadisi ba.

Mun gode Allah, muna tare da ilimi, muna tare da Hadisan Annabi SAW in sun tabbata daga Annabi suke, wanda in auna su duka, za a gane daga Allah suke. Yadda za mu gane cewa, wannan Littafi daga Allah yake, shi ne da fadinsa tabaraka wata’ala, “Walau kana min indi gairillahi, la wajadu fihi kairan kasiran – wannan littafi da ba daga ubangiji yake ba, da an samu cakudi da yawa acikinsa”. Alkur’ani ya yi gaskiya, babu wani ilimi da za ka shiga, sai kaga sabani da yawa, wani wuri a bayyana shi da “eh”, wani wuri kuma da “a’a”.

Don haka, duk wata mas’ala ta ilimi sai kaji an yi sabani amma banda maganar Allah – babu raunanna a ciki kuma babu karya, sai tabbatacciya. Da wannan ya zama, Musulmai komai na su farko, shi ne Alkur’ani sannan Hadisi wanda bai sabawa Alkur’ani ba, sannan maganar Malami wanda bai sabawa wadannan ba. Don haka, babu rigima, komai a sarari yake.

Shehunnanmu Sufaye sun ce, ko kaga waliyyi yana tashi sama, ko yana taka ruwa, amma in kaga yana sabawa Alkur’ani ko Hadisi, to Dujal ne ba waliyyi ba. Wannan magana, ta amfanar da kyau, har ya zamto yanzu, batun karamu ba sa birgewa, suna da girma a wurin mu amma ba sa birgewa, amma mutum muga yana bin Alkur’ani da Hadisan Manzon Allah SAW wanda basu sabawa Alkur’ani ba, shi kenan bawan Allah ne, ko ya tashi sama ko bai tashi sama ba. Mun gode Allah, duk wannan shi muke karantar da ‘ya’yanmu, wadansu Allah ya taimake su sun haddace Alkur’anin, amma ko mutum bai haddace ba, matukar yana tare da Alkur’anin, sai yaga albarka.

Sannan su yi ilimi kowane iri, har na bokon, har su iya zama Farfesoshi, a fannonin ilimi, irin su kimiyya da fasaha, likitanci, lissafi, aikin gona, kwamfuta, da sauransu.

Duk wani ilimi, ga ma’abocin Alkur’ani, ya kan zuwa masa cikin saukin fahimta sabida kowane ilimi yana cikin Alkur’ani. Don haka, duk karatun addinin Musulunci da ya sabawa kimiyya da fasaha, to ba a karance shi sosai ba ne.

Amma abin takaici, yadda aka mayar da Alkur’ani littafin yanke hannu da jefe mazinaci kawai.

Alkur’ani yana da ayoyi fiye da 6,200 amma bayanin Shari’a bai wuce ayoyi 200 ba sauran duk bayanin ilimi suke yi, na daga iliman sararin samaniya, taurari, kasa, tekuna, duwatsu, tsirrai, namun daji, nau’o’in kasa, da bayanin abin da ke cikin kasa, da bayanin abin da muke gani da wanda ba ma iya gani.

Don haka, abun kunya ne ga Musulmai, ga su da wannan babban littafi amma sun zama kamar shara, yau sun zama a baya a fannin ilimi sabida sun wulakantar da Alkur’ani. A wannan zamani ma, da zarar mutum ya yi kira ga a koma wa karatun Alkur’ani sai a yi masa mummunan zato, to in musulman suna son dawo da girmansu, to su komawa asalinsu, littafinsu da sabuwar fahimtarsa (Alkur’ani).

Allah ya sakawa ‘ya’ya da Malaman yaran da suka yi sauka da haddar Alkur’ani. Annabi SAW yana cewa, “ku isar da sako na, ko da da aya daya ce”.

Da wannan za mu fahimci darajar wanda ya isar da Sura, ballantana Alkur’ani baki-daya.

Hadisi yazo, “duk wanda ya haddace Alkur’ani kamar Annabi ne sai dai ba a yi masa wahayi”. Ya dace mu koma wa Alkur’ani – littafi ne na wayewa, da rayuwa, wanda ya koya mana zaman lafiya, da yadda zamu zauna da kanmu da iyalinmu lafiya, da yadda, zamu zauna da iyayenmu lafiya, kai har da yadda zamu zauna da kowa ma lafiya.

Bugu da kari, Alkur’ani ya koya mana yadda za mu raya kasa, bai bar mana wani abu na amfani ba sai da ya gaya mana shi, a fusaha irin ta ubangiji.

Mun gode Allah, bamu ce a zubar da kowane littafi ba amma mu yi hattara, duk littafi in dai yana biye da Alkur’ani shi kenan ya yi, amma in maganarsa ba ta yi daidai da Alkur’ani ba, to wannan ba za a yi aiki da shi ba.

An tambayi Sayyada A’isha, “menene halin Annabi SAW, Alkur’ani halinsa SAW”. Don haka, in aka ruwaito wani hali da ba Kur’ani ba kuma aka ce maka halin Annabi SAW, to wannan kamar Sayyada tace maka, wannan karya ne!

Allah ya saka wa shugabannin makaranta – Malam Musa Imam da suka tsayawa wannan makaranta ta Islamiyya da Boko don tafiya da zamani, kamar yadda duk aka fada a baya. Allah ya tsare ku da tsarewarshi, ya baku gari naku na kanku, duk abin da ake tsoro Allah ya tsare ku, duk abin da ake nema na alkairi, Allah ya kawo shi.

Iyayen
Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
+ postsBio
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Haɗa Basmala da Suratul Fatiha
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Neman Tsari Daga Sharrin Shaidan
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Bukatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Buƙatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

MASU ALAKA

Manzon Allah
Dausayin Musulunci

Falalar Haɗa Basmala da Suratul Fatiha

June 19, 2026
Falalar Neman Tsari Daga Sharrin Shaidan
Dausayin Musulunci

Falalar Neman Tsari Daga Sharrin Shaidan

June 12, 2026
Bukatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW
Dausayin Musulunci

Bukatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

June 5, 2026
Next Post
Fursunoni 9 Sun Kammala Haddar Alƙur’ani A Kano

Fursunoni 9 Sun Kammala Haddar Alƙur’ani A Kano

LABARAI MASU NASABA

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

June 24, 2026
’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

June 24, 2026
Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

June 24, 2026
Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

June 24, 2026
Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

June 24, 2026
Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

June 24, 2026
Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

June 24, 2026
Sabbin Ministoci

Kafa ‘Yansandan Jihohi: Majalisa Ta Amince Da Tsarin ‘Yar Tinƙe Wajen Kaɗa Ƙuri’a 

June 24, 2026
Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

June 24, 2026
Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

June 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.