ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Albishir Ga Iyayen Da Suka Karantar Da ‘Ya’yansu Alkur’ani

by Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
3 months ago
Albishir

Annabi Muhammad SAW na duk duniya, da duk halitta baki daya. Annabin Turawa ne, Sinawa, da Jamusawa, da Farisawa, da Larabawa, da duk Afirka baki daya. Kabilunmu iri-iri, da suka hada da Hausa, Fulata, Yoruba, da sauransu da yawa, wadanda ba su da adadi, duk Annabi SAW, Annabinsu ne, an aiko shi gare su duk baki daya.

Annabi SAW an aiko shi ne rahama ga duk halitta, addininsa Rahama ne.

Duk in kaga tsanani a addinin Annabi SAW, ba daga addininsa ba ne, sai dai yana daga tsanantawar Malamai ne.

ADVERTISEMENT

Allah ya aiko Annabi SAW, ya zama cika makon Annabawa, bayansa babu wani Annabi, babu wani ma’aiki.

Har yanzu dai, Allah ya aiko Annabi SAW tare da cika makon littattafai duka (Alkur’ani). Tun zamanin Annabi Nuhu, Allah yake saukar da littattafai, wanda ke dauke da Shari’o’i. Karshen littattafan, shi ne Alkur’ani, sabida ya tattaro komai na daga Shari’o’i da Hakikoki, har tashin Alkiyama, babu wani hannu da zai rubuta abin da yafi wanda ke cikin Alkur’ani ba. Idon anga musulmai ba su cigaba ba a bangaren ilimi, da adalci, da wayewa, to laifin ba daga littafin ba ne, daga mu musulmai ne, don haka, babban alheri, Musulmai su komawa littafinsu.

LABARAI MASU NASABA

Falalar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

Falalar Yawaita Tuba Ga Ubangiji (Istigfari)

Wannan littafin, duka musulmai mun yi imani da shi, don haka, farkon abin da muke koyawa ‘ya’yanmu, shi ne Alkur’ani, don mun san, shi ne mabudi kuma shi ne alheri.

Ana cewa, duk wanda ya fara da karanta Alkur’ani, Allah zai busa rai, ma’ana, Allah zai sanar da shi wani ilimi, da kaifin hankali da basira. Alal misali, da wanda ya iya karatun Alkur’ani da wanda bai iya ba, su fara karatun Boko tare, wanda yake da karatun Alkur’ani sai yafi wanda bai da shi saurin fahimtar karatun, sabida duk abin da ake karantarwa a makarantar Boko, yana cikin Alkur’ani.

Allah zai sake yassare wa mai Alkur’ani hikimar iya kai sako, da ya yi magana, sai a yi saurin fahimta. Duk wanda ya yi karatun Alkur’ani, ya haddace ko bai haddace ba, sai Allah ya sanya masa albarka, ba zai wulakanta a rayuwa ba, a duk fannin da ya shiga, ko dai ya zama babban Malami ko ya zama babban mai kudi. Don haka, duk wanda ya haddace Alkur’ani, za a ga albarka a tare da shi.

Duk inda ake karatun Alkur’ani, Allah zai sanya albarka a wannan wurin. Idan kauye ne, sai ya zama Birni mai gine-gine irin na zamani, idan a wurin kasuwancinsa ne, Allah zai sanyawa kasuwancin albarka.

Mun gode Allah da ya bai wa wadannan dalibai wadanda ke walimar sauka a yau, Alkur’ani. Malaminsu, kowa ya yi masa shaida, lalle Aramma ne na gaske, wanda ya rubuta Alkur’ani da hannunsa. Albarkar Annabi SAW, muna fata, wata rana sai an kwaso yara daga Birni zuwa wannan makarantar Alkur’ani ta Aramma.

Yana daga cikin falalar Alkur’ani cewa, zancen Ubangiji tabaraka wata’ala ne akan kasa, ko harafi daya babu na Annabi SAW aciki, sai dai Allah ya fassaara Alkur’ani da Larabci, yadda Annabi SAW zai iya don ya sanar da Larabawa da ke kusa da shi, amma Alkur’ani sirri ne, sai dai wasu malamai sun ce, ubangiji tabaraka wata’ala ya bar mana wasu abubuwa kadan don mu gane, kamar kuraman baki: “Kaf ha ya ain sad, daha, yasin,…”, wannan sirri ne, ba yare ba ne ballantana a fassara, haka duka Alkur’ani yake, sai dai, Allah ya fassara wa Annabi SAW shi da Larabci, amma na duk halitta ne, don haka, kowa (Turawa, Sinawa, Hausawa,…) da Larabci zai karanta shi.

Sai dai, wasu malamai na daga Sahabbai, Tabi’ai, da sauransu, sun fahimce shi har suka rubuta wasu ma’anoninshi da yarensu. Don haka, an fassara shi da kowane yare. Babu wani yare da zai ce bai san Alkur’ani ba sabida an fassara shi da wannan yaren. Alkur’ani, yana bukatar mu kara himma wajen fahimtarsa kamar yadda yaranmu suke kara yawa wajen haddace shi.

Mu kara godiya ga yadda Allah ya bamu Alkur’ani, don littafi ne da ya dace da kowane zamani: ya dace da wannan zamani da kuma zamanin da zai zo gaba, har tashin Alkiyama.

Babbar birgewa ta malami, idan zai fassaara Alkur’ani, ya fassara shi da irin ilimin wannan zamanin, ya ga duk ilimin kimiyya da fasaha na wannan zamanin acikin Alkur’ani. Allah ya barmu, kuma ya karfafe mu da Alkur’ani. Allah ya saka wa iyayen yara da suka kula da Malamin yaransu da ya haddatar da su Alkur’ani.

Ya zo acikin Hadisi, manzon Allah SAW yace, “duk wanda ya karantar da dansa, ko ya dauko wanda ya karantar masa da shi, Allah da kansa, zai gaisa da wannan mutumin a ranar tashin alkiyama, sannan Allah zai rubuta acikin littafin mahaifin yaron ladan kamar ya yi Hajji 10,000, kamar ya yi Umra 10,000, kamar ya ‘yanta bayi 10,000, kuma bayin darajarsu ta kai kamar, Larabawa ‘ya’yan Annabi Isma’ilu, kamar ya Musuluntar da mutane 10,000, kamar ya ciyar da mayunwaci 10,000 wanda ciyar da mayunwaci daya kuwa, Imam Shafi’i yana cewa, “loma daya da za ka saka a bakin mayunwaci, tafi ka gina masallaci 1,000″, kamar ya tufatar da wadanda basu da kaya su 10,000 kuma Alkur’anin zai zama tare da shi acikin kabarinsa cikin sura mai kyau don dauke masa kewa har zuwa ranar tashin Alkiyama”. Wannan lada, duk na wanda ya tsaya wa dansa ne ya san Alkur’ani.

Allah tabaraka wata’ala, zai sanya cika a ma’aunin mahaifin da ya tsaya wa dawainiyar yaronsa har ya haddace Alkur’ani, zai tsallake siradi kamar walkiya, sannan Alkur’anin zai rike hannunsa har shiga Aljanna, hakan duk yana kunshe ne acikin Tafsirin Suratul Fatiha na Littafin Fakrurrazi.

Wannan duk ladan mahaifin da ya tsayawa dawainiyar yaronsa ne har ya haddace Alkur’ani, to ina ladan malamin yaron, bare kuma na mahaddacin?

Maganar Alkur’ani tana da yawa, sabida in an ce Alkur’ani, amfadi ubangiji, kuma amfadi Annabi Muhammad SAW wanda ya kawo shi. Don haka, kowane littafi, za a fade shi ne da wanda ya kawo shi, Alkur’ani na Allah ne kuma Annabi SAW ya kawo shi.

Dawwamar Alkur’ani, itace dawwamar mu da sanin Allah da sanin Annabi SAW.

Lallai duk Musulmai sun yi imani cewa, Alkur’ani shi ne na daya, amma a wurin hukunci, Malamai sun mayar da shi wurin na goma sabida lalacewa, har wadansu daga cikin Malaman suna cewa, “Wai Hadisi zai shafe hukuncin Alkur’ani”, amma ikon Allah, ba su iya cewa, Ijma’i zai iya soke Hadisi ba.

Albishir
Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
+ postsBio
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Haɗa Basmala da Suratul Fatiha
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Neman Tsari Daga Sharrin Shaidan

MASU ALAKA

Matsalar Tsaro: Gwamnatin Tarayya Ta Nemi Taimakon Ƙasashen Waje
Dausayin Musulunci

Falalar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

July 3, 2026
Darussan Da Suka Fi Dacewa A Fahimta Daga Alkur’ani A Wannan Zamanin (2)
Dausayin Musulunci

Falalar Yawaita Tuba Ga Ubangiji (Istigfari)

June 26, 2026
Manzon Allah
Dausayin Musulunci

Falalar Haɗa Basmala da Suratul Fatiha

June 19, 2026
Next Post
Tasirin Kyawawan Sauye-sauyen Manufofin PoS

Tasirin Kyawawan Sauye-sauyen Manufofin PoS

LABARAI MASU NASABA

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

July 14, 2026
Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

July 14, 2026
An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

July 14, 2026
Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

July 14, 2026
Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

July 14, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Kotu Ta Tsare Shugaban Makaranta Da Malami Kan Zargin Lalata Da Ɗaliba Mai Shekara 6 A Gombe

July 14, 2026
An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

July 14, 2026
Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

July 14, 2026
Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

July 14, 2026
CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

July 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.