ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, July 18, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bukatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

by Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
1 month ago
Annabi

A’uzu billahi minash-shaitanir-rajim. Bismillahir-Rahmanir-Rahim. Allahumma salli ala sayyidina Muhammadinil-fatihi lima ughlika wal-khatimi lima sabaka nasiril-hakki bil-hakki, wal-hadi ila siratikal-mustakim wa ala alihi hakka kadrihi wa mikdarihil-azim. Wa radiyallahu an ashabi rasulillahi sallallahu alaihi wa sallam, la hawla wala kuwwata illa billahil-aliyyil-azim.

Ya himmatash-sheikh izhirilana bihadal-mahaddari waltati bina wastintatinal-nasi bi-zafari. ‘Yan uwa, assalamu alaikum warahmatullahi taala wabarakatuhu. Mungode Allah, da Allah ya hadamu a wannan rana mai albarka mai girma, a cikin addinin mu, kuma mai girma, a cikin darikarmu, ranar da muke haduwa baki daya muke ambatan Allah tabaraka wa taala, a cikin yadda falalolin sa za su zo.

Alhamdullilahi, wannan zikiri kullum muna yi, amma kuma muna haduwa duk karshen shekara mu gode wa Allah, mun cika ayyukan mu na shekara, mun kuma yin wani alkawari da Allah zamu kuma sabunta himma, mu kuma cigaba da wannan shekara. Dama darikan mu da dukkan ma ayyukan mu, mun karba ne iya rayuwa, mun karba ne har rasuwa. Toh kullum muna jaddadawa, muna jaddadawa.

ADVERTISEMENT

A kowane irin hali, irin wannan zama, dada sabunta kai ne. Godiya ga Allah ne, Allah ya karba mana ibadodin da muka yi a shekara da ta shige, ya yafe mana zunuban da muka yi a shekara da ta shige, kuma mun kara kulla azama ta wannan shekara da zata zo, muna fata Allah ya taimake mu, mu ninka, mu ninka, mu ninka ibada a kai, Alfarman Annabi sallallahu alaihi wasallam ya jikan matattunmu, kuma ya yi albarka ga rayayyunmu, ya ja da rayuwarmu da iyayenmu da kakaninmu ga su da suke zaune gabanmu tare da mu. Allah ya ja mana da rayuwar su a cikin al-khairi da budi da lafiya, Alfarman Annabi sallallahu alaihi wasallam, ya biya bukatun mu ga baki daya da bukatun mutanen gari.

Hadisi yazo cewa, “duk wanda zikiri na, da littafi na ya shagalantar da shi, har ma bai ce ina son kaza ba, sai na bashi abin da yake so kafin in bai wa mai addu’a abin da ya roka”. Toh, mungode Allah, zaman mu anan, Allah mu ka ambata, ya shagalantar da mu, wannan biyan bukata ne yanke ga dukkanin, da duk garin, da masu masaukin baki, duk gabaki daya alfarmar Annabi SAW.

LABARAI MASU NASABA

Falalar Salatut Tasbihi

Falalar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

‘Yan uwa, a gurguje, mungode Allah. Mungode Allah da ya sa mu a cikin darikar nan ta Shehu Tijjani RA. Idan mutum zai magana a cikin darikar nan, sai ya rasa ma ta ina zai kama. Saboda hanyoyin magana da yawa a cikin ta, saboda falalarta. Don haka, duk abin da za a fada acikinta, yana nuna abu Uku ne:

Takalli, yana nun wanka daga zunubi; tahalli, yana nuna ado bayan an yi wanka daga zunubi, sai tajalli, da ke nuna haduwa da sarki ubangiji.

Kullum aikin mu kenan. Takalli, mu yi wanka daga zunubanmu duk gabaki daya, mu yi ta istigfari. Sannan in mun yi wanku kuma, sai mu yi tahalli, ado da salatin Annabi SAW, wanda shi ne babban ado, shi yasan irin kayan da ya dace da hadarar Allah, shi yasan irin adon da ya dace, don zamu shiga fadar Allah ne. Toh bayan Manzon Allah ya yi mana ado da salatin sa, toh shikenan kuma sai tajalli, ganawa da sarki, sai ka ji muna fadin, “la ilaha illallah, la ilaha illallah”, shike nan komai ya samu.

Toh wannan shine darikarmu, shine ayyukan da yake cikin darikarmu. Kowanne lokaci, zaka ji mu cikin istigfari, zaka ji mu cikin salatin Manzon Allah SAW, zaka ji mu cikin “la ilaha illallah”. Toh wannan muradi duk ya biya a cikin wadannan, don su suke kare, farillolinmu. Akwai zunubin da in mutum ya yi, za’a ce, sai ya yi kwana arba’in Allah zai karbi farillarsa ko nafilarsa. To yau, ire-iren wannan zunubai, su suka fi yawa, amma mun gode Allah, istigfari, da wannan salati, da wannan zikiri da muke, su kuma neman irin wadannan zunuban suke yi su cinye su.

Wannan na nuna cewa, wadannan ayyuka da muke yi, za su cinye mana duk wani zunubi da zai taba mana farillanmu. Ko bamu je da ladansu na komai ba, bare da lada, ya zama dai sun share mana hanya, farillolinmu sun kai lafiya kalau, wannan ya isa falala. Ko bamu je da ladan komai ba, bare lada ne kan lada, kan lada, har Allah ma ya bamu tun muna ganawa da shi, wato da zuci, da idon zuci, idon basira, har Allah mai iko ne kuma ya bamu ganawa da shi, da idon basaru ma na ganin mu, “wa ma zalika alallahi bi’aziz”, ya bamu wannan duniya da lahira.

To ‘yan uwa kamar yadda muka fada, wannan sune auradan darikarmu. Su mutum zai zo ya karba, sune darikar Tijjaniya: Istigfari, salatin Annabi SAW, da la’ilaha illallah. Safiya da yamma, sai wazifa da muke yi, sai zikirin juma’a. Wadannan sune rukuni hudu, kuma sune darikar Tijjaniya.

Su ne mutum zai zo ya karba, da ganin damarsa, da son sa na alkhairi, da son soyayyar bayin Allah, ya zo ya karba. A sanya masa sharadi, bayin Allah suna da sharadi. Sharadi, har Kur’ani ya fadi sharadi, hadisai duk sun zo da sharadi. Kafin ka zo a gaya maka sharadi, ba a ce sai ka zo ba, ba dole ba ne. Amma yanzu, in ka zo kana so, to sai an sanya maka sharadi. Idan ka bi sharadi sai abin da kazo nema (mashrudi) ya samu. Amma in ka bar sharadi, mashrudi ba zai samu ba.

Wannan hatta, Annabin Allah, ulul azmi, Annabi Musa AS, da ya zo zai bi bawan Allah, Sayyidina Khadiru, “hal attabi’uka ala an tu’allimani mimma ullimta rushda”, sai da ya bashi sharadi. Zaka bi ni, zaka bi darika ta ko? eh zan bi darikarka, to sai na baka sharadi. “Fa’in ittaba’tani fala tas’alni an shai’in hatta uhdisa laka minhu zikra”. To in ka bi ni, sharadi na (Khadiru), kar a tambaye shi komai. “Fala tas’alni an shai’in”, kar ka ce mun damme ko ta kaka ko yaya, . “Hatta uhdisa laka minhu zikra”, har sai in ni na ga dama nace ma abu kaza da muka yi fa kaza kaza ne.

Yanzu kamar Annabin Allah, a ce da shi haka? to amma kuma in dai zai bi, to dole ya bi wannan sharadi. Kuma da sharadi bai cika ba, sai ga ayar Kur’ani na cewa, “haza firaku baini wa bainak”, ka ma gaban ka. Allahu akbar. Shehu Ibrahim Kaulakh na cewa, manya ma an ce musu, haza firaku baini wa bainak, ka ma gaban ka, to kuma waye wani? To, sharadin da shehu Tijjani yake bai wa kowa ne mukaddami, shi ne, “in an shiga ba fita”.

Wannan sharadi, wanda bai sani ba, sai ya ji kamar da wuya, amma abu ne mai sauki. Allah ya tsare, mutum ya shiga cikin wannan alkhairi mai yawa ya fita. Kullum in mun gama, auradan darikarmu, addua muke yi, “Allahumma sabbitna bi hazihit-tarikati-t-tijjaniyah”. Allah ka tabbatar damu a kai, kullum ma addua muke. Sannan, ba za a hada ta da wata darika ba, duk dariku na Allah ne, kuma duk suna kai wa zuwa ga Allah. Amma ba zaka hada su da darikar Tijjaniya ba. Mace in ta auri maza biyu, in ta yi ciki, na waye? In ka samu budi fatahi na Allah, a wajan wa ka samu kenan?

Annabi
Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
+ postsBio
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Salatut Tasbihi
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Haɗa Basmala da Suratul Fatiha

MASU ALAKA

Falalar Salatut Tasbihi
Dausayin Musulunci

Falalar Salatut Tasbihi

July 17, 2026
Matsalar Tsaro: Gwamnatin Tarayya Ta Nemi Taimakon Ƙasashen Waje
Dausayin Musulunci

Falalar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

July 3, 2026
Darussan Da Suka Fi Dacewa A Fahimta Daga Alkur’ani A Wannan Zamanin (2)
Dausayin Musulunci

Falalar Yawaita Tuba Ga Ubangiji (Istigfari)

June 26, 2026
Next Post
Xi Jinping Zai Kai Ziyarar Aiki A DPRK

Xi Jinping Zai Kai Ziyarar Aiki A DPRK

LABARAI MASU NASABA

Sin Za Ta Inganta Kaddamar Da Aikin Kungiyar Hadin Gwiwar AI Ta Duniya Da Wuri

Sin Za Ta Inganta Kaddamar Da Aikin Kungiyar Hadin Gwiwar AI Ta Duniya Da Wuri

July 17, 2026
Tinubu Da Atiku Da Obi Na Ci Gaba Da Zafafa Neman Kuri’un Arewacin Nijeriya

Tinubu Da Atiku Da Obi Na Ci Gaba Da Zafafa Neman Kuri’un Arewacin Nijeriya

July 17, 2026
Sin Ta Yaba Da Matakin Amurka Na Kin Tsawaita Dokar Ta-Baci Dangane Da HK

Sin Ta Yaba Da Matakin Amurka Na Kin Tsawaita Dokar Ta-Baci Dangane Da HK

July 17, 2026
Zaben 2027:Tikitin Muslim-muslim Na Jam’iyyar APC Ya Sake Tayar Da Kura

Zaben 2027:Tikitin Muslim-muslim Na Jam’iyyar APC Ya Sake Tayar Da Kura

July 17, 2026
Xi Ya Gana Da Babban Sakataren MDD Da Firaministocin Thailand Da CambodiaA

Xi Ya Gana Da Babban Sakataren MDD Da Firaministocin Thailand Da CambodiaA

July 17, 2026
Zaben Fidda Gwani Da Ake Takaddama:APC Ta Dauki Matakan Kauce Wa Shari’o’in Kotu

Zaben Fidda Gwani Da Ake Takaddama:APC Ta Dauki Matakan Kauce Wa Shari’o’in Kotu

July 17, 2026
Sin Ta Mika Sabuwar Manhajar Gargadin Gaggawa Ta MAZU Ga Djibouti

Sin Ta Mika Sabuwar Manhajar Gargadin Gaggawa Ta MAZU Ga Djibouti

July 17, 2026
Sake Daukar Shettima Da Tinubu Ya Yi Zai Kara Karfafa APC A Zaben 2027 –Farfesa Yerima

Sake Daukar Shettima Da Tinubu Ya Yi Zai Kara Karfafa APC A Zaben 2027 –Farfesa Yerima

July 17, 2026
Kwamitin Ba Da Shawara Kan Hadin Gwiwar Kasa Da Kasa Na Dandalin BRI Ya Yi Taronsa Na 2026

Kwamitin Ba Da Shawara Kan Hadin Gwiwar Kasa Da Kasa Na Dandalin BRI Ya Yi Taronsa Na 2026

July 17, 2026
Wang Huning Ya Ziyarci Koriya Ta Arewa

Wang Huning Ya Ziyarci Koriya Ta Arewa

July 17, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.