Ma’aikatar ayyukan gaggawa da ceton jama’a ta kasar Sin, ta ce an tura masu aiki ceto sama da 2,500 zuwa yankin kan iyakar Gyirong, sashen jihar Xizang mai cin gashin kai na kudu maso yammacin kasar Sin mai iyaka da kasar Nepal.
A yayin taron manema labarai da ya gudana a yau Lahadi, wasu jami’ai sun yi bitar lamarin, inda suka ce fadowar kankara daga tudu a ranar 26 ga watan Agusta da ya gabata, shi ne ya haddasa malalar laka a Nepal, ibtila’in da ya haifar da rasuwar mutane 43, kana wasu 519 suka bace.
Ya zuwa yammacin jiya Asabar 5 ga wata, an aike da sama da jami’an ceto 2,500, da ababen hawa sama da 500 domin shiga ayyukan ceton, kana an jefa tan 5.43 na kayayyakin tallafin jin kai ta jirage marasa matuka 1,000. Ma’aikatar ta ce an riga an samar da tallafi ga mazauna kan iyakar kasar Nepal su 1,720 bayan aukuwar malalar lakar. (Saminu Alhassan)














